Tambayoyi da Amsoshi



A: Yayin tsarkake tufafi da makamantansa da ruwa mai gudu ko kuma ruwan kur matsewa ba sharadi ba ne, duk wata hanyar da aka bi wajen fitar da ruwan da ke jikinsa ya wadatar, ko da kuwa ta hanyar jijjiga mai tsanani ne a misali.

T50: Mene ne hukuncin alwala .da kuma wanka da ruwan da a dabi'ansa shi mai kauri ne? Misali kamar ruwan teku da saboda yawan gishirin da ke cikinsa ya mai da shi mai kauri.

A- Dan kawai ruwa ya yi kauri saboda kasantuwan gishiri a cikinsa ba ya hana a kira shi "Ruwa Mudlak". A shar'ance abin da ke tabbatar da kasantuwan ruwa "mutlaki" shi ne idan har jama'a za su kira shi wannan ruwa da sunan mutlaki.

T51: A wasu lokuta a kan sanya wa ruwa wani sinadarin da ke sanya shi ya zamanto da launin madara, to shin wannan ruwa ya zama "ma'ul Mudaf" ruwa wanda ya cudanya? Shin mene ne hunkuncin alwala ko tsarki da shi? A: Hukuncinsa ba hukuncin "ma'ul Mudhaf' (ruwan da ya cudanya) ba ne.

T52: Idan ruwa mai gishiri-gishiri ya tafasa, shin ana iya alwala da ruwan da ya taru na daga tururinsa?

A: Idan har abin da ya taru na daga wannan za'a iya kiransa "ma'ul Mudlak" (wato ruwa mutlaki) to ana iya amfani da shi.

T53: Yayin wanke tufafi masu najasa da ruwa mai yawa shin wajibi ne a matse su ko kuma zuba (isasshen) ruwa kan inda najasar ta taba bayan gusar da najasar ya wadatar?

A: Zubo (isasshen) ruwa a kansu da kuma fitar sa daga gare su ya wadatar ko da kuwa ta hanyar jijjiga su cikin ruwa mai yawa, ne matsewa ba sharadi, ba ne.

T54: A lokacin da muke son wanke darduma ko shimfida mai najasa da ruwan famfo, shin su kan tsarkaku ne da zarar saduwar ruwan famfon da wurin najasar ko kuma sai an fitar da ruwan wankin daga jikinsu.

A: Yayin tsarkake abu mai najasa da ruwan famfo fitar ruwan wankin ba sharadi ba ne, face dai yana tsarkakuwa ne daga zarar isar ruwan ga wurin da ya najastu bayan gushewar najasar da kuma gushewar ruwan wankin daga gurin.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next