Tambayoyi da Amsoshi



T19: Shin ya halatta mutum ya bar taklidin A'alam cikin fararrun mas'alolin da suka shafi zamani saboda gazawarsa wajen ciro ingantattun hukuncinsu?

A: Idan har shi mukallafi bai so ya yi ihtiyati cikin mas'alar ba, ko kuma ya gagare shi to idan har ya sami wani mujtahidi A'alam wanda yake da fatawa akan mas'alar to wajibi ne a gare shi ya koma gare shi ya yi masa taklidi. a cikin mas' alar.

T20: Dangane da juyawa daga   daya daga cikin fatawoyin imam khumaini (r.a), shin wajibi ne a koma ga fatawar mujtahidin da ya ba da izinin ci gaba da taklidin mamaci ? ko kuma ya halatta a koma ga fatawar sauran wasu mujtahidai?

A: A nan wajibi ne a koma ga mujtahidin da ya ba da izinin ci gaba da takalidin mamaci.

T21: Shin canza takalidi (al-udul) daga A'alam zuwa ga wanda ba A'alam ba ya halatta?

A: Uduli a nan ya saba wa ihtiyat, hakika ma dai ba ya halatta a bisa ihtiyat idan har fatawar A'alam  din akan mas'alar ta saba wa fatawar wanda ba A'alam ba.

T22: Na kasance na ci gaba da taklidin. Imam (r.a) saboda la'akari da fatawar  daya daga cikin manyan mujtahidai, to bayan da na yi nazarin amsoshinka cikin "al-lstifta'at" da kuma ra'ayinka kan ci gaba da takalidin Imam khumaini (r.a), sai na bar wancan na ci gaba da ayyukana dai-dai da fatawoyin hnam (r.a) bugu da kari kan fatawoyinka, shin akwai wata matsala a cikin wannan "udul" nawa?

A: Ba ya halatta a bisa Ihtiyat na wajibi canza takalid daga rayayyen mujtahidi zuwa ga wani rayayyen, sai dai idan a ganin mukallafi na biyun ya fi na farkon ilimi kana kuma fatawarsa ta saba wa fatawar na farko, to a wannan halin wajibi ne bisa ihtiyat ya koma ga na biyun.

T23: Wanda ya kasance yana takalidi wa Imam (r.a) kana kuma ya ci gaba da yi masa takalidi (bayan rasuwarsa), shin zai iya komawa ga waninsa na daga cikin maraji'ai cikin wata mas'ala kamar rashin daukar garin Teheran cikin manyan birane ko kuma a'a?

A: Hakan ya halatta a gare shi, ko da yake bai kamata a bar ihtiyat, ba wajen ci gaba da taklidin Imam (r.a), idan har yana ganin fifikonsa kan rayayyu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next