Tambayoyi da Amsoshi



T139: Ni dalibi ne na jami'a a bangaren likitanci, to a wasu lokuta ya kan zama dole mu taba jikin mamata yayin darasi, tare da cewa ba mu san wadannan mamata musulmai ne ko kuma a'a ba? To amma shuwagabannin gurin su kan ce mana an riga an yi wanka wa wadannan mamata, dan haka muke so a mana bayani kan abin da ya wajaba a kan mu dangane da salla da dai sauransu bayan taba wadannan gawawwaki kana bisa ga abin da aka ambata shin wajibi ne sai mun yi wanka?

A: Idan har asalin yin wanka ga wadannan mamata bai bayyana maka ba kana kuma kana da shakkan faruwar hakan, to wajibi ne ka yi wankan shafan mamaci idan har ka taba su ko wani bangare na jikinsu kana salla ba ta inganta in har ba ka yi wanka ba. To amma idan har ya bayyana maka cewa an yi musu wanka to babu wata matsala idan ka shafi jikin nasu ko kuma wani bangare na jikin ko da kuwa kana shakkan ingancin wankan.

1140: Idan wani mutun ya fara rurrushe maKabartan musulmai ba tare da la'akan da abin da shari'a ta shinflda ba, to mene ne abin da ya wajaba kan sauran musulmai dangane da wannan mutum?

A: Abin da ya wajaba kansu shi ne hana faruwar mummunan aiki amma tare da la'akari da sharudodi da kuma martabobinsa.

NAJASOSI, DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCENSU

T141: Shin jinni yana da tsarki?

A: Jinin dabban da jininta yake gudanya yayin yanka shin dan' Adam ko kuma waninsa najasa ne.

T142: Alamar jini da yake saura a jikin tufafin mutum bayan wanke shi, shin najasa ne?

A: Idan dai har abin da ya saura din ba ainihinjinin ba ne, kana kuma ya ki fita bayan an wanke shi, to ba najasa bane.

T143: Mene ne hukuncin gudan jinin da ke cikin kwai?

A: Ba najasa ba ne amma cinsa ya haramta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next