Tambayoyi da Amsoshi



T110: Idan har gwargwadon hashafan namiji ya buya a farjin mace, to amma maniyyi bai fita ba kana kuma macen ba ta kai kolin jin dadinta ba, to shin wanka ya wajaba a gare ta ne kawai ko kuma ga namijin ne kawai ko kuma wajibi ne a kansu su biyun ?

A: A bisa wannan yanayi da aka ambata wajibi ne gare su su biyun.

T1ll: Dangane da mafarkin mata, shin a wani irin yanayi ne wankan janaba yake wajaba a gare su? Kana shin ruwan da yake fito musu yayin wasa da mazaje yana da hukuncin maniyyi ne? Kana kuma shin wajibi ne su yi wanka tattare da cewa basu kai ga jin dadinsu ba kana ba su ji mutuwar jiki ba? A takaice dai yaya janaba take tabbata ga mata ba tare da jima'i ba?

A: Idan mace ta ga alamar maniyyi a jikin tufafinta bayan farkawarta daga barci to wajibi ne ta yi wankan janaba. to amma ruwan da yake fito musu yayin wasa da makamancinsa ba shi da hukuncin maniyyi, sai dai idan ya fito tare da mutuwarjiki da kuma isa gajin dadi na koli.

T112: Shin wanka yana wajaba ga budurwar da sha'awarta ta tashi ta hanyar karatun littafan batsa ko kuma ta wata hanya ta daban? To idan har wankan ya wajaba, to wane wankan ne ya wajaba a gare ta?

A: Karanta littattafan da suke motsa sha'awa bai halatta ba. Bisa dukkan hali dai wajibi ne gare ta ta yi wankan janaba idan har maniyyi ya fito mata.

Tl13: Yayin da mace ta fahimci zuban wani ruwa cikin sha'awa lokacin wasa shin wajibi ne ta yi wankan janaba?

A: Idan har mace ta fahimci zuban maniyyi daga gare ta to wanka ya wajaba a gare ta, haka ma idan tana shakkan abin da ya fito din maniyyi ne ko kuma, a a, matsawar dai ya fito ne tare da sha'awa ta musamman.

T114: Idan mace ta yi wanka daga zarar saduwa da mijinta kana maniyyinsa ya ci gaba da zama cikin mahaifanta, shin wankanta yana nan da ingancinsa idan har maniyyin ya fito mata bayan wankan? Kana shin wannan maniyyi da ya fito bayan wanka yana da tsarki ko kuma a'a?

A: Wannan maniyyi da ya fito mata najasa ne, sai dai idan har abin da ya fito mata din maniyyin mijin ne to ba ya wajabta wanka a karo na biyu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 next