Tarihin Fatima Zahra [a.s]Salatin Allah (SWT) da Mala'ikunsa (AS) ga Manzo, kafin umurtan muminai dalili shi ne akan yin koyi da Allah da Mala'iku wajen yi wa Manzo salati. A nan mai karatu yana iya ganin cewa babu wata ibada wace tnuminai suke yi wacce take koyi ne ga Allah da Mala ikunsa in banda salatin Manzo (SAAW). Kennan ba mai yiwuwa bane mutum iyakirdadon matsayin yin salati ga Manzon Allah (SAAW) da iyalan gidansa. An ruwaito daga Imam Sadiq (AS) yana cewa karkashin tafsirin ayardaAllah(SWT)yakecewa: LALLAI ALIAHADAMALA IKUNSA... Salatin Allah Mabuwayi ga Manzonsa shi ne rahama. salatin Malaiku shi ne tazkiwa da yabo gare shi. sannan salatin muminai gare shi shi ne addua. Da wannan ayar ne da muka ambata Malamai baki daya suka tafi a kan wajibcin yin salati ga Manzon Allah (SAAW). har ma Imam Shafi'I ya tafi a kan cewa duk wanda ya yi tahiyar salla ta karshe bai yi wa Manzo salati ba ba shi da salla. sai ya sake. Wannan shi ne yake har yau a mazhabar ShafTiwa, Sayyid Tabataba'i yan cewa: An samu ittifaki tsakanin sunni da shi’a a kan yi wa Manzo salati shi ne mutum ya ce: Allahumma salli ala Muhammad wa Ali-Muhammad. Ya zo a cikin Durrul Mansur na Imam Suyudi yana cewa: An ruwaito daga Ibn Abi Shaiba. Ahmad, Abdu Ibn Hamid, Bukhari, Muslim. Abu Dauda, Tirmizi. Nisa'i. Ibn Hajri yana cewa: Wani mutum ya tambayi Manzo cewa: Ya Manzon Allah. yi maka sallama wannan mun sani. Amma yaya salati a gare ka yake? Sai Manzo (SAAW) ya ce: Ku ce: Allahumma salli ala Muhammad wa ali-Muhammad kama sallaita ala Ibrahima wa ali-Ibrahima, Allahumma barik ala Muhammad wa ali-Muhammad kama barakta ala Ibrahima wa ali-Ibrahima, innaka hamidun majid. Sayyid Tabataba'I yana cewa: Hakika ya zo a wurare kamar 18 na daga ruwayoyin As'habus sunan da Jawami'u (manyan malaman hadisai na sunni kamar Bukhari, Muslim dss) gwama salatin Manzo da iyalan gidansa, banda hadisin da muka ambata a sama. Wadanda suka ruwaito daga sahabbai daban-daban, kamar Ibn Abbas. Ka'ab Ibn Hajri, Aliyai (AS) Abu Sa'idul Khudri, Abu Huraira, Abu Mas'ud Al-ansari. Burda Ibn Mas'ud, dss. Amma ruwayoyin Malaman Shi'a kuwa wannan sun fi haddin kirguwa. Ya zo a cikin Yabiul Muwadda cewa: An ruwaito daga Manzon Allah yana cewa kada ku yi min salati yankakke. Sai sahabbai suka ce wane irin salati ne yankakke ya Manzon Allah'.' Sai ya ce: salati yankakke shi ne ku ce: Allahumma salli ala Muhammad. sai ku yi shiru ku ki karasawa. In za ku yi min salati ku ce: Allahumma salli ala Muhammad wa ali-Muhammad. Ya zo a cikinYanbiul Muwadda cewa Abu Nuaim Alhafiz da wasu jama'a daga Malaman tafsiri. sun ruwaito daga Mujahid da Abu Salih daga Ibn Abbas (RA) yana cewa Ali-yasin. sune Ali-Muhammad domin Yasin suna ne daga sunayen Muhammad (SAAW).
|