Tarihin Fatima Zahra [a.s]Mahaifiyarta ce babbar matan Shugaban Ma'aika, Ta rigayi kowa imani da wahayi ya sauka, Ta ce da Manzo Inni amantu. tun Manzo ya tare da Nana Khadija cikin gidan da ta ba shi kyauta a nan cikin garin Makka. Gidan ya kasance mai dakuna hudu ne. Daki na farko shi ne kafin a shiga cikin gidan. watau kamar zaure yake. Na biyxi shi ne inda yake ibada. A nan ne wahayi yake sauka masa in yana gida. Na uku shi ne inda yake da iyalinsa. Na hudun shi ne inda yaransa suke kwana. Manzo ya kasance da iyalansa cikin wannan gida mai albarka har zuwa lokacin da Allah (swt) ya yi masa umurni da ya yi hijira zuwa Madina. An ce da zai yi hijira ya bai wa Akilu bin Abi Talib. ko kuma ya gaje gidan. kamar yadda aka yi ma sauran sahabbai. don shi a lokacin bai musulunta ba. Sannan Mu'awiyya Ibn Hindu ya saya ya mai da shi masallaci. sannan kuma Nasiru Abbasy yagyara shi. sai Ashrab Shaaban Sarkin Misra ya gyara shi. ya kuma fadada shi Allah (swt) ya ba mu lkon zuwa ziyara amin. A shekara ta biyar bayan auren Manzo da Nana cikin wannan gidan da muka yi bayani mai albarka Allah ya azurta su da diya mai albarka wacce ita ce diyar Manzo ta farko. Nana ta haife ta tana da shekara 35 a duniya. Manzo kuma yana da shekara 30 a duniya. Bayan ta kai shekara goma sha daya sai Manzo ya aurar da lta ga dan dan uwan mahaifiyarta. watau shi ne Abu Asi bin Rabra. An ruwaito cewa Nana Khadija (as) ta kashe mata kudi masu yawa wajen bikin auren kasantuwar lta ce ta farko. kuma auren zumunci ne ga dangin Nana Khadija. An dauki lokaci mai tsawo ana ta shagalin bikin mai alfarma. Sun kasance tare da mijinta Abu Asi. zama na soyayya da kauna. duk da cewa ita musulma ce. amma shi bai musulunta ba. sannan kuma Musulunci bai yi umurnin raba aure ba tsakanin musulma da wanda ba musulmi ba Sun kasance cikin wannan halin tsawon shekara 15. Kodayaushc ta kira shi zuwa ga Musulunci yakan ce mata shi yana son ya musulunta. amma yana jin kunya kar a ce ya musulunta saboda matarsa. A lokacin da aka yi yakin Badar. Abu Asi yana daga cikin wadanda inusulmi suka yi garkuwa da su a matsayin bayi Lokacin da Manzo ya ba da dama a Ko da Abu Asi bin Rabia ya komo Makka sai ya ba ta labarin abin da ya faru da kuma umurnin da Manzo ya ba shi Sai ya hada ta da dan uwansa a kan ya raka ta wajen Makka don ta bi hanyar Madina ya zuwa ga Mahaifinta. Da Abu Sufyanu bin Umayya ya ji labari. sai ya tura Jabbaru bin Awwad a kan ya jc ya dawo da ita. wai a kan za ta yi hijira da rana suna kallo! ko da Jabbaru bin Awwad ;ya riskc ta a hanya.sai ya kamata ya yi mata azaba har sai da ta yi Darni aan aa ke ciKinia Sannan ya dawo da ita Makka. Ta kuma shiryawa da daddare ta yi hijira zuwa Madina. A nan muna iya ganin cewa ba a Karbala ne Banu Urnayya suka fara dirar ma iyalan Manzo ba. a'a tun ferkon duniya suka daukar ma kansu share hasken wahayi. Har ya zo cewa ran da aka kawo ma Yazid bin MiTawhya kan Imam Husaini bin Ali (as) bayan an kashe shi, sai ya rera waka. a ciki yake cewa da iyayensa da aka kashe a Badar za su ga wannan da sun jinjina mishi. kuma da bakin cikinsu ya kwaranye. To amma Allah (swt) bai yarda ba. kuma har abada ba zai yarda ba. Ta kasance a gidan Babanta har zuwa wani iokaci mai tsawo. Sannan Abu Asi bin Rabia ya musulunta ya yi hijira zuwa Madina. Bayan isowarsa Madina ne Manzo ya yi umurni da a mayar da aurensa da masoyiyarsata asali watau Zainab (as). Bayan mayarda auren babu jimawa sosai. sai Allah (swt) ya yi mata wafati. aka binno ta a makabartar Baki'a kusa da masallacin Manzo. Abu Asi bin kabi'a bai kuma yin wani aure ba. har shi ma ya yi wafati. saboda bakin cikin rabuwa da yar kwarai mai tarbiya gaba da baya. Ta haifar masa da yara guda biyu Aliyu Da Amamatu. Shi Aliyu ya rasu yana dan shekara goma zuwa sha biyar. Ita kuma Amaniatu ta aun Imam Aliyu (as) saboda wasiyyar da N'ana Fatima (as) ta bar mishi. Sannan kumata auri Mugira bin Naufal bin Abdul Mutallib saboda wasiyyar da Imain Alhu (as) ya bar mata.
|