Tarihin Fatima Zahra [a.s]Sanna sai ta kuma amsa sallama sai ta ce: "'Ya dan Ammina Mika'ilu ya zo shi ma ya fadi kwatankwacin abin da Jibrilu ya fada. Bayan nan kuma sai ta kuma amsa sallama, ta bude idanuwanta ta ce: Ya dan ammina, hakika na ga yakini. Azara'ilu ne ya buda ftikafukansa. na gan shi kamar yadda Mahaifma ya siffanta min shi." NANA FATIMA (AS) A GADON JINYA!
Rayuwar Nana (as) ya zo karshe. ranar rayuwarta ta yi fatsi-fatsi tana gab da faduwa. Babu abin da ya rage mata sai dai haduwa da Mahaifinta. Ta kwanta a shimfida lokacin da rashin lafiya, rama da bakin ciki suka galabaitar da ita. ba ta burin maganin wani mai magani don ta sha. Ba ta burin ta ci gaba da rayuwa ko kadan, duniya da abin cikinta sun yi mata kunci tun bayan wafatin Mahaifinta. An ruwaito daga Imam Sadiq (as) yana cewa: Kunfuz (1) ya bugi Nana Fatima (as) da gindin takobi (ranar Bai'a) a kirji, wannan sai ya zama sanadmar rashin lafiyarta. wanda ta yi wafati. Aliyu shi ya yi jinyanta sannan Asma'u binti Umais ta taimaka mishi. Ta shimfida buzun rakumi a tsakar daki ta kwanta ta tada kanta da filo na ganyen dabino. tana tunani tana kuka tana ceua: Oh sun ki yarda da wasiyyancin Mahaifina. sun ki yarda da shugabancin da zai hada kan musulmi baki daya. Sun janyo rarrabuwar kawunan musulmi, sun janyo wa Musulunci rauni da gazawa a idon duniya. Ni ce Fatima mafi mutunci a gurin Manzon Allah (saw). Ga ni kwance cikin rashin lafiya da bakin cikin abin da wannan arumman suka aikata. Shin mutuwa ta kusa ne'.' Ina wasiyyin Manzon Allah (saw)? Yanzu Alnnn da na sani ne mai shaja'a ya zama mai rauni don maslahar addini9 Hakika ajalina ya kusa.., Hakika lokacin tafiyata yayi. Yaya yarana:- Hasan. Husaini. Zainab da Ummi Khulsum (as) za su kasance bayana9 Me ya yi girman masifar da za ta samc su"' Yanzu marawna ne wannan masifar za ta saffie su! Manzo ya sha fada min yana cewa: Danki. Hasan za a ba shi guba ya sha bai sani ba ya mutu Husaini kuwa za a kashe shi shahidi. kisan killa yana tsananin kishirwa! Ga shi tun yanzu ina da rai na fara ganin alama... Ya kasance yakan kama hannun Husaini. yana shafar kansa yana kuka saboda masifun da za su same shi! Yakan kama Hasan ya rungume shi yana sumbantarsa. yakan tuna halin da zainab da Ummi-Khulsum za su sami kansu a ciki sai ya fashe da kuka..." Ta kasance cikin kwanukan rashin lafiyanta takan ce: "YA HAYYU YA KAYYUM. ka tsiratar da ni don Rahmarka Ya Ubangijina ka nisantar da ni daga azabar wuta. ka shigar da ni Aljanna ka nskar da in ga Mahaifina." Sai Imam Aliyu (as) ya ce mata. "Muna miki addua ne Allah ya ba ki latiya. sai ta ce Ya baban Hasan baa bin daya fi soyuwa a gare ni kamar in tafi in riski mahaifina.Imam Aliyu (as) ya ga Nana (as) tana kuka, sai ya tambaye ta me ya sa ta kuka9 Sai ta ce tana kokawa ne'a kan abin da zai same shi bayanta. Sai ya ce: "Wallahi duk wannan a gurina ba a bakin komai yake ba mutukar a tafarkin Allah ne!" Duk da Imam Aliy u (as) da Nana (as) sun yi kokarin kada wani ya sani bacin mutanen gidan. amma ina labari ya isa ko'ina cikin Madina cewa 'yar Manzo. "Bakiyatun Nubuwwa ba ta da lafiya, kuma rashin lafiyar ya yi tsanani! Ko ina da ma sai zuwa ake gaishe ta. na daga sahabbai. matan Manzo. matan Madina. dss. Lokacin da rashin lafiya ya yi tsanani sosai sai Abubakar da Umar suka je su ma don su gaishe ta kada ta yi wafati tana fushi da su. ba su roke ta gafarar abin da ya faru a tsakaninsu na batun Bafa da gonar Fadak ba, kamar yadda muka dan yi bayani a baya. Ya zo a cikin littafin Ibn kutaiba. malamin sunni (Imama was siyasa) juzu'i na daya shafi na 14 da Aalamul- Nisa'u. juzu'i na uku shafi na 1314 yanacewa: "Umar (r.a)yaccma Abubakarmu jemugaishe da Fatima. hakika mun bata mata rai. Sai suka nufi gidan Fatima. Sun nemi lzninta a kan su shigo su gaishe ta. amma ta ki yarda. Sai suka je -gem Aliyu suka yi mishi bayani. sai ya shiga da su L.okacm da suka tsaya gabanta. sai tajuya fuskanta zuwa wajen bango! Suka yi mata sallama ba ta amsa musu ba! Sai Abubakar (r.a) ya yi rnata magana yana cewa: 'Ya abar kaunar Manzon Allah! Wallahi dangin Manzon Allah su suka fi soy uwa gare ni daga dangina Km fi soyuwa a gare ni daga A'isha diyata Na yi burin a ce na yi wafati ban rayu ba bayan wafatin Mahaifinka. Kina ganin bay'an na san ki. na san matsayinki da daukakarki zan hana ki hakkinki da gadon Mahaifinki Manzon Allah' Sai dai ni na ji Mahaifinki yana cewa: Ba a gadonmu. abin da muka ban ya zama sadaka. Sai ta ce: 'Za ku yarda in gaya muku hadisi daga Manzo wanda kuka sani?" Sai suka ce 'Na'am. Sai ta ce: "Ina gama ku da Allah. ba ku taba jin Manzo ya ce: Yardar Fatima yardata ne. fushinta fushina ne. duk wanda ya so Fatima diyata hakika ya so ni. wanda ya faranta mata hakika ya faranta min........ ? Sai suka ce na am mun ji haka daga Manzon Allah (saw). Sai ta ce: Allah da Mala'ikunsa su ne shaidu. hakika kun bakanta min. ba ku faranta min ba Idan na hadu da Annabi (saw), zan kai karan ku gurinsa Sai Abubakar ya ce ma neman tsari gurin Allah Madaukaki a kan fushinsa (Manzo) da fiishinki (Fatima)" Sai Abubakar ya fashe da kuka kamar zuciyarsa za ta fashe... Sai ya fita yana ta kuka. "Daga nan sai mutane suka taru, sai ya ce musu, 'Kowannenku yana kwana cikin gidansa hankali kwance da iyalansa. Ni kuma kun bar ni da halin da nake ciki! Ba ni da bukatar bai'ar da kuka yi min, ku zo ku waroare min bai'aY ku!" Akwai ruwayoyin sunni da shfa a kan wannan masu yawa. Mai karatu yana iya bincikawa. Sannan sai tajce: 'Ya mai karbar rayuka ka saukaka min kar ka tsananta! Ya zuwa ga Allah za ka kaini ba ya zuwa wuta ba." Sannan ta rufe idanunta. Sai Allah ya amshi ranta!!.
|