Tarihin Fatima Zahra [a.s]



 (8). An ruwaito daga Ibn Umar yana cewa: Manzo ya sumbanci kan Fatima sai ya ce: Uwata da Ubana fansarki ne. kin kasance kamar yadda nake.

(9)  An ruwaito daga Aisha tana cewa: Fatima ta zo gurin Manzo. ba ka iya bambance tafiyar ta da ta Manzo. sai Manzo ya ce 'Barkan ki da zuwa diyata. Sai ya zaunar da ita a dama ko hagu da shi. Sannan sai ya sirranta mata wani magana sai ta fashe da kuka! Sai ya kuma sirranta mata wata
magana kuma sai ta fashe da dariya Sai  na ce ban taba ganin kuka da dariya kurkusa kamar yau ba. Sai na tambaye ta dalili. sai ta ce ba za ta fada min sirrin mahaifinta ba Bayan wafatin Manzo sai na kuma tambayar ta sai ta co: Da farko Manzo ya sirranta mm ne a kan Jibrilu ya kasance yakan yi masa tilawar Kur'ani sau daya a shekara. amma bana ya yi mishi sau biyu Yana ganin wannan alama ce ta ajalinsa ya kusa Sai na fashe da kuka Sirrantawa ta biyu kuwa shi ne ya ce min ashe ba na yarda ln zama shugabar matan duniyaba' Sai na fashe da dariya. Ga wata ruwayar kuwa sai ya ce '
Ƙe ce farkon wacce za ta riskc ni cikin iyalain gidana." sai na
fashe da dariya.

(10)  Malaman Sunni kamar su Buhari. Muslim. Ahmad Ibn Hambal. Ibn Maja. Sajistani. Tirmizi. Nisa i. Nisaburi. Baihaki. Ibn Hajr. Suyudi. dss Duk sun ruwaito wannan hadisin da za mu zo da shi da isnadi daban-daban.

(a). Manzon Allah ya ce: Fatima tsokace daga gare ni. wanda ya cutar da ita hakika ya cutar da ni.

(b) Manzon Allah ya ce: Fatima tsoka ce daga gare ni Yana cutar da ni duk abin da ya cutar da ita. yakan bakanta min duk abin da ya bakanta mata

c) Manzon Allah ya ce. Fatima yanki ne daga gare ni. tsoka ce daga gare ni yana bakanta niin duk abin da ya bakanta niata. ana faranta min duk abin da ya faranta mata. Ya Fatima Allah yana fushi da fushinki yana yarda da yardarki

(d) Manzon Allah ya ce: Wanda ya san ta hakika ya san ta, wanda bai san ta ba to ita tsoka ce daga gare ni. Ita ce zuciyata da ruhin da ke cikin kirjina. duk wanda ya cutar da ita hakika ya cutar da ni. Lallai Allah yana fushi da fushinta. yana yarda da yardarta.

(11) Abul Farj ya ruwaito cikin littafin Al-agani yana cewa: 'Wata rana Abdullahi Ibn Hasan ya shigo gurin Umar Ibn Abdul Aziz yana karami (yaro), sai ya taso daga cikin Majalisarsa ya tarbe shi, sannan ya sunkuya ya sumbanci fatar cikinsa. Sai ya ce masa zan tuna maka wannan don ceto gobe kiyama. Lokacin da Abdullahi Ibn Hasan ya tafi sai 'yan majlisarsa suka kama zargin sa suna cewa 'Dan wannan yaron ne kake yi wa irin wannan girmamawar!" Sai' ya ce na ji daga majiya mai tushe. (Kamar ka ce na ji daga Manzon Allah ne) Manzon Allah yana cewa. ' Fatima tsoka ce daga gare ni. yakan faranta min duka abin da ya faranta mata." Na tabbata da Fatima tana raye da ta yi farin ciki da abin da na yi wa danta (Abdullahi Ibn Hasan)... Kowane daya daga cikin Banu Hashim yana da ceto wanda zai yi ranar kiyama. Ina fatan cetona ya zama daga cikin cetonsa (Abdullahi Ibn Hasan Ibn Ali Ibn Abi Talib) "

Samhudi bayan ya kawo hadisin da Manzo yake cewa: Fatima tsoka ce daga gare ni. wanda ya cutar da ita hakika ya cutar da ni. wanda ya faranta mata hakika ya faranta min." sai ya ce wannan ba ita kawai ba har ma "yaYanta. Sai shi Suhaili ya ce "Wannan hadisin yana nuni da duk w anda ya zagc ta ya kafirta. wanda kuma ya yi mata salati kamar ya yi yya mahaifinta ne. Sannan ya ce su ma ya yanta haka ne. donnn su ma tsoka ce daga gare ta."

Allah (swt) yana cewa: "Wadanda suke cutar da Allah da Manzonsa, Allah ya la'ance su duniya da lahira, ya kuma yi masu tattalin azaba mai wulakantarwa. " Allah (swt) yana cewa: "Wudannan wadanda suke cutar da Manzon Allah suna-da azaba mai radadL " Ya Allah ka yi mana tsari daga fadawa cikin wannan hatsann. ka sama mu cikin masoya Fatima (as) da iyalanta. Sharifai (12) An ruwaito daga Ibn Abbas yana cewa: An tambayi Manzon AJlah wacc kalma co Annabi Adam ya roki Allah da ita bayan ya ci 'yayan itaciya. Allah ya yafc masa? Sai ya ce ya roki Allah ne don darajar Muhammad. Aliyu. Fatima. Hasan da Husain. sai Allah ya gatarta masa .



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next