Tarihin Fatima Zahra [a.s]



 

WAHAYI YA SAUKA A KAN A BA IMAM ALIYU (AS)

 Bayan abin da ya w akana kamar yadda muka yi bayani a baya. sai Manzo ya ce "'Ya Alnu ma yi maka albisliir?" Sai Imam Aliyu ya ce na'am. Sai Manzo ya ce Lallai Allah mai girma da daukaka ya nga aurar maka da ita a can sama tun kafin in aurar maka da ita a nan doron kasa. A nan gurin dazun Jibnlu ya zo min daga sama yana mai cewa: "Ya Muhammad lallai Allah mai gnma da daukaka ya yi duba ya zuwa mutanen kasa sai ya ga kai ne mafi alhennsu. Sai ya zabe ka don isar da sakonsa Sannan ya yi duba na biyu sai ya zaba maka dan uwa. waziri. sahabi. sannan ya aurar masa da diyarka Fatima. Yau Mala'ikun sama suka kare walimar auren,Ya Muhammad Allah mai girma da buwaya ya umurce ni dain

umurce ka a kan ka aura wa Aliyu, Fatima a nan doron kasa. Sannan kuma ka yi musu albishir da haihuwar 'ya'ya biyu tsarkakakku, zababbu, madaukaka nan duniya da kuma lahira.' Ya Aliyu wallahi yana tashi dazu kana kwankwas kofa."

AUREN NANA FATIMA DA IMAM ALIYU A BAITUL MA'AMUR

An nmaito daga Jabir Ibn Abdullah (ra) yana cewa Ummi Aiman ta shiga gurin Manzo tana kuka, sai Manzo ya ce mata "Me ya same ki?'" Sai ta ce: "Wani mutumin Ansar yaauar da 'yarsa sai na ga an yi mata kwalliya mai kayatarwa. Sai na tuna ran da ka aurar da Fatima sam ba ta sami wani abu mai kamar haka ba." Sai Manzo ya ce "'Na rantse da wanda ya tayar da ni da karamci ya kebantar da ni da sakonsa lallai ran da Allah zai aurar da Fatima. ya umurci Mala'ikunsa makusanta (mukarrabin) kan su hadu a mda AFarshinsa yake. Daga cikinsu akwai Jibnlu. Mikailu da Israfilu. Sai ya umurci tsuntsaye a kan su yi wake. Sai suka yi wakoki masu dadi na muma da auren Fatima. Sannan sai ya umurci Shajaratul duba" a kan ta zuba wa duk wanda yake gurin da luuluu da zinare na kwalliya da koraye da jajayen yakutu."9

Ga wata ruwayar kuwa. ita ce an yi daurin auren ne a Sidratul Muntaha can sama ta bakwai ran da Manzo ya yi mi'iraji.

An samo daga Anas Ibn Malik (RA) yana cewa "Wata rana muna zaune a masallaci. sai Manzo ya ke ba Aliyu (AS) labarin cewa. "Jibrilu (as) ya ba ni labarin cewa Allah (SWT) ya aurar maka da Fatima. Mala'iku dubu arba'in ne suka halarci daunn auren. Sai Allah (SWT) ya yi wahayi ga "Shajaratul duba' a kan ta wadatar da kowanne daga cikinsu da lu'ulu'u da murjani. Kowanne ya diba ya yi kwalliya da shi. Sannan Hurul'in (matan Aljanna) suka kwashe sauran suka yi kwalliya da shi. Da shi ne kuma suke alfahari a cikin kayan kwalliyarsu har zuwa tashin kiyama.""

Ya zo a Biharul Anwar cewa: Mala'ikun sammai sun hadu a Baitul Ma'amur'. Aka aza mumbann karamci na haske. Sai Allah ya yi wahayi ga wani daga cikin Mala'ikunsa na hijabobi ana kiransa da suna Rahil a kan ya hau wannan mumbarin ya yi yabo dagodiya ga Allah Shi Malaikin ya kasance duk cikin Malaiku babu mai fasaharsa da mandikinsa wajen bayani.

sai ya hau yana mai cewa: uoaiya ta taocara ga Alian tun kaTin farkon halitta da bayan gushewar halittu baki dai a Muna yi masa godiya da ya sanya mu cikin Mala'iku Rauhanai. Da renonsa iie muka zama abin da muka zama. Muna matukar godiya gare shi a kan ni'imomin da ya yi mana. Ya kare mu daga juyawa ya zuwa ga sha'awa, sai ya sanya sha'arwarmu ya zuwa masa tasbihi

"'Shi ne mai bayar da rahma. mai mika kyauta. Ya daukaka daga abin da masu shisshigi suke siffantawa ya zuwa gare shi." Bayan nan sai ya ce: "Allah mai mulki da buwaya ya zabi zababbe daga cikin zababbunsa ga zababbiyar baiwarsa. Shugabar mata baki daya, 'yar shugaban Annabawa da Manzanni, sannan Limamin 'Muttakina.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next