Tarihin Fatima Zahra [a.s]Lokacin da Manzo (SAW) ya tsaya a Khaibar bayan ya ci su da yaki tsawon kwana uku. sai Yahudawan Fadak suka aiko mishi a kan a yi sulhu don kar ya iso gare su. a kan sun ba shi rabin gonar Fadak da abin da ke cikinta na dabinnai da sauran "yayan itace masu yawan gaske Bayan nan sai Allah (swt) ya saukar da wahayi a kan wannan gonar (Fadak) ya bai wa Manzo shi kadai, mallakar kansa inda yake cewa: "Abin da Allah ya sanya ganima ga Manzonsa daga mutanen kauyokan nan. to na Allahne. kuma na Manzonsa ne..." Wannan gona ta kasance a hannun Manzo mallakarsa yana sarrafa gonar da abin da ake samu ta wajen taimaka wa Banu Hashim. fakirai da miskinan Madina An yi kiyasi a kan cewa akan samu misalin kamar dinare dubu Ashirin da hudu zuwa dubu sabain (N94.()8().OOO-274.400.000) ashekara. Bayan da Allah (swt) ya saukar da ayar da take cewa: "Ka bai wa makusanta hakkinsu." Sai Manzo ya kira Fatima (as) ya ba ta wannan gonar kyauta. Jalaluddin Suyudi ya ruwaito cikin littafinsa Durrul Mansur, juzu'i na hudu, shafi na 177 yana cewa: "An ruwaito daga Abi Sa'idul Khuduri yana cewa: Lokactn da aka saukar da ayar da Allah (swt) yake cewa "Ka bai wa makusanta hakkinsu." Manzo nan take ya mwatar da abin da Allah ya umurce shi, ya kira Fatima ya ba ta gonar Fadak kyauta." An ruwaito daga Aliyn Ibn Abi Talib (as) yana cewa "Manzo ya bai wa Fatima (as) gonar Fadak kyauta * An ruwaito daga Adiya yana cewa: "Lokacin da ayar da Allah (swt) ke cewa: "Ka bai wa makusanta hakkinsu.".., Manzo ya kira Fatima (as) ya ba ta gonan Fadak kyauta. Wannan hadisin da ke bawanar da cewa Manzo ya bai wa Fatima (as) Fadak kyauta "Mutawarin" hadisi ne, wanda malaman sunni da shi'a suka ruwaito shi. Don haka ba za mu tsawaita ba. sai dai mai karata yana iya bmcikawa don amfanin kansa. GWAMNATI TA AMSHE FADAK Bayan kwana gotna da kaftiwaT gwamnati. sai Abubakar ya aika da Wakilinsa a Halbi ya ruwaito a cikin littafin siransa. juzui na uku. shafi na 39. yana cewa: " Ga wata ruwayar kuwa, lokacin da Ummi Aiman ta zo, kafin ta yi shaida sai da ta ce: "Ba zan yi shaida ba ya Abubakar, sai na kafa maka hujja a kaina guda daya. Sai ta ce: Ina gama ka da Allah ka taba jin Manzo ya ce Ummu Aiman mace ce daga cikin matan Aljanna? Sai ya ce ' na taba ji' Sai ta ce: "Na rantse da Allah Mai girma da buwaya lokacin da Allah ya yi wa Manzo wahayi da ayar da yake cewa "Ka bai wa makusanta hakkinsu..." Manzo ya kira "Bayan nan sai Aliyu (as) ya dawo masallaci. sai ya tarar da Abubakar sai ya tambaye shi don mc ya hana
|