Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Da wannan ne ake mata lakabi da Zahara. Kuma ba ma Mala'iku kawai ba, har ma mutanen Madina sukan ga wannan hasken. Su suka fi kiran ta ma da Zahara fiye da kowa. Ya Allah ka haskaka mana zuciya da haskenta, ka sa mu a cetonta in kiyama ta tsaya, amih.

 

(j) BATUL (as)

Sanannen abu ne cewa Allah (swt) ya sanya sunansa a cikin komai. ya sanya ka'idoji wadanda ba za su saba ba. Kamar tsirrai ta yadda ba za su iya motsawa nan da can ba, kuma suna da lokaci na tsurowa. Kamar wuta ta yadda take da kuna, to sunan Allah ga wuta shi ne wannan kunar. wanda mai karatu yana iya gano misalai daban-daban dangane da wannan.

Amma su Auliya ullahi sukan zo ne ko kuma su aikata abin da yake ya saba ma wadannan ka'idojin ko sunna, wanda Allah (swt) ya ba su don girmamawa gare su da kuma bayyanar da matsayinsu ga aFumma. Misalin wannan shi ne kamar Annabi Ibrahim (as) yadda yyuta ta zama mai sanyi da ammci gare shi lokacin da kafirai suka jefa shi da nufin halaka shi. Kamar Annabi Musa (as) yadda yake mai da sandarsa ta zama macijiya. sannan kuma ta koma sanda. Kamar Annabi lsa (as) lokacin daukar cikinsa ba tare da uba ba. da kuma tsawon cikin zuwa haihuwa. wanda bai yyuce awa bakwai zima tara ba. wanda duk wannan ya sha bamban da al'adar daukar ciki da haihuwa. To ire-iren wannan suna da yawa a tsakanin Auliyaullahi.

_ To ita tna Nana (as) tana cikin wannan jerin ta yadda Allah (swt) ya dauke mata haila da biki? wanda ya sha bamban da al'adar mace. wacce take daukar ciki da kuma haihuwa. Wannan girmamawa ne ga ita Nana (as) da kuma bayyanar da matsayinta ga aFumma. An samo daga Manzo cewa: An ambaci Fatima da suna Batul ne saboda yankewarta ga jinin haila ko kuma biki. An samo daga Asma'u binti Umais tana cewa: "Na halarci sad da Nana Fatima (as) ta haifi Hasan amma ban ga jini ba, na haila ne ko ko na bikr' Sai Manzoya ce mata "Shin ba ki sani bane cewa diyata tsarkakakkiya ce abin tsarkakewa, wadda ba za a ga jini tare da lta ba na haila ne ko na biki?".

 

(k) AZRA'U (as)

 Daga cikin sunayenta. Ana mata lakabi da Azra'u saboda rashin canzawar halittar jiki wanda Allah (swt) ya yi-mata, kamar matan Aljanna kullum suna nari a 'yan mata ba sa tsufa har abada.

Ga baitukan jerin sunayenta kamar yadda Mustapha Gadon Kaya ya yo cikin wakensa na BATULA.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next