Tarihin Fatima Zahra [a.s]



NEMAN AUREN NANA FATIMA (AS)

A shekara tafarko bayan hijira mutaneko'ina sunamaganar kammaluwar Nana (AS) wajcn cikar hankali. yawan basira. zurfin tunam da tann ilimi. ga ibada. Wajcn kyau kuwa Larabayya ba su.taba ganin wata mace mai kyawunta ba. gaba daya duk "Jaziratul Arab'. Koina sai maganarta ake yi da kuma tunanin wancnc Allah zai mishi gam da katar yaaurc ta tsakanin manyan masu kudi da mulki na Larabawa'?

Shu aibu Ibn Sa ad ya ruwaito ccua "Lokacin da hasken ranar kyawunta ya haske dukkan sasanni, sannan farin watan kamalarta ya game ko'i ina. sai dukkan tunani da kauna na zababbun mutane daga Muhajimn da Ansar ya koma ya zuwa gare ta. Amma Manzo bai amsa musu ba, yakan ce masu ne "Sai wahayi ya sauka." ABUBAKAR, UMAR DA ABDURRAHMAN SUN NEMA An samo daga Anas Ibn Malik yana cewa "Wata rana Abubakar ya je gaba ga Manzo yana mai cewa: "Ka san kyawawan halayena da dadewata cikin Musulunci." da kaza da kaza. Sai Manzo ya ce "Me ke tafe da kai ne?" Sai ya ce "Na zo ne ka aura min da Fatima." Sai Manzo ya yi shiru bai ce masa komai ba. Daga nan sai Abubakar ya koma ya ba Umar labari. yana mai takaicin zuwansa. Daga nan sai Umar ya ce masa "Ka saurara a nan. ni ma bari in je in jarraba." Ko da ya je ga Manzo sai ya fadi kwatankwacin abin da Abubakar ya fada. Sai Manzo ya yi shiru bai amsa masa ba. Sai Umar ya koma zuwa ga Abubakar yana mai cewa 'Lallai Manzo yanajiran wahayi ne."

An ruwaito cewa Abdurrahman Ibn Auf ya je wajen Manzo neman auren Fatima (AS) sai Manzo bai amsa masa ba. Sai ya yi zaton cewa ko al'amarin batun kudi ne. Sai ya ce nia Manzo ya fadi sadakinta ko nawa ne. shi yana so zai biya. Daga nan sai ran Manzo ya baci. bai ji dadin wannan magana ba. Sai Manzo ya sa hannu ya dauko tsakuwowi a tafin hannunsa. Sai suka kama tasbihi a hannunsa. Daga nan sai suka zama liTulu'u da murjani. Sai Manzo ya ce "Ka biya waniian a nan. inda gaske ne. In har ba ka iyawa ta yaya za ka ce a yi wa diyar Manzon Allah kudi ko nawa ne za ka biya?" Sai Abdurrahman ya yi nadamar fiinicin da ya yi. ya ba Manzo hakuri.7-9 IMAM ALIYU YA TAFI NEMA

An ruwaito daga Salman Farisi yana cewa: Wata rana Abubakar da Umar suna zaune a masallacin Manzo, a tare da su akwai Sa'id Ibn Mu'az Al-ansari suna tattaunawa a kan alamarin Fatima. sai Abubakar ya ce: Hakika ba wani babban mutum a garin nan wanda bai nemi auren Fatima gun Manzo ba face ya ce masa "Al'amarin aurenta yana ga Ubangijinta. in ya so ya aurar da ita ga wanda ya ga dama'" Sai Aliyu ne kawai bai je ya nema ba. Ni ina ganin ko karancin abin hannu ne ya hana shi. Lallai zuciyata tana raya min a kan Allah da Manzonsa shi suke nufin su bai wa aurcn Fatima In maganar kudi ne lallai mu za mu taimaka masa gwargwadon lko' Sai Saad Ibn Mu'az ya ce '"Lallai wannan magana taka hakatake."

Daga nan suka bazama neman sa. Sun neme shi, artuna ba su gan shi ba. Daga nan sai suka nufi wata gona ta dabino, inda yakan shayar da dabino ana biyan sa. Ko da Imam Aliyn ya gan su sai ya ce "Me ke tafe da ku ne9" Sai Abubakar Ibn Abikuhafa ya ce "Ya Aliyu babu wata kyakkyawar dabi'a wacce ba kayi fice ka zarce kowa akanta ba. Kana da matsayin da babu wani mai shi gurin Manzo na kusanci, sahibanci, da farkon shiga Musulunci. Hakika manya daga Kuraishi sun nemi auren Fatima gun Manzo amma bai amsa musu ba, yakan ce al'amarin auren yana ga Ubangijinta in ya so.ya aurar da ita ga wanda ya so. Me zai sa ba za ka je ka nemi aurenta gun Manzo ba? Ni ina tsammanin Allah da Manzonsa kai suke sauraro." Ko da Aliyu ya ji haka, sai idanunsa suka cika da hawaye. Sai ya ce "Ya Abubakar ka tayar min da abin da yake kwance, ka farkar da ni daga abin da na gafala daga gare shi. Wallahi lallai babu wanda kaunarta bai cika mishi zuciya ba. babu wanda ya kamace ta kamar ni. Amma ba wani abu ya hana ni ln nema ba sai dai karancin abin hannu." Sai Abubakar ya'ce masa "Kada ka fadi haka ya Aliyu. Ai durm a da abin da ke cikinta kamar kura ne abar watsarwa a gurin Manzo. ka yi hanzari ka je."

Daga nan sai Imam Aliyu ya koma gida ya kintsa ya nufi gun Manzon Allah (SAW) don neman auren Nana Fatima (AS). Manzo ya kasance yana dakin Ummi Salma sai Imam Aliyu (AS) ya kwankwasa kofa (kafin ya fadi sunansa) Sai Manzo ya ce Ƙi tashi Ummi Salma ki bude kofa ga mutumin da Allah da Manzonsa suke kaunarsa." Sa: Ummi Salma ta ce: "Uwata da Ubana fansarka ne. wane mutum ne wannan kake yabon sa tun kafin ka gan shi?" Sai ya ce Ummi Salma "'Ba zuga bane. shi no dan’uwanka. dan Ammina. sannan mafi soyuwa gare ni ga dukkan halitta. Ummi Salma ta ce sai na tashi cikin hanzan na bude kofa. sai ga Aliy u Ibn Abu Talib (AS). Sai Aliyu Ibn Abi Talib ya shiga gurin Manzo ya amsa "Wa alaikassalam. Ya Aliyu zauna." Sai Alnai (AS) ya zauna gaba ga Manzo ya sunkuyar da kansa kasa. yana kallon kasa don kunyar Manzo Ko da Manzo ya ga haka sai ya ce "Na san akwai abin da ke tafe da kai. Ka fadi duk abin da ke zuciyarka kar ka ji komai. Ni mai biyan duk bukatunka ne'

Daga  nan sai Imam Aliyu [a.s] ya ce Uwanta da Ubana fansarka ne.Lallai kana sane ka dauke ni daga hannun Amminka Abi talib

da Fatima Bint Asad tun ina karami. Ka ciyar da ni abincinka, ka shayar da ni abin shanka, ka tarbhyantar da ni tarbiyyarka. Ka kasance mafi tausayi, da tausasawa gare ni fiye da Abi Talib da Fatima Bint Asad. Lallai Allah ya shiryar da ni ta hannunka. Lallai wallahi kai ne tattalina kai ne tattalina duniya da lahira. Ya Manzon Allah kamar yadda Allah ya yi min goma ta arziki ta hannunka zan so ya kasance ma da gida. Ina da mata wacce zan dinga natsuwa ya zuwa gare ta. Hakika na zo ne ina mai nema. mai buri a kan ka aurar min da diyarka Fatima. Ko hakan zai yiwu?"

Da jin wannan sai fuskar Manzo ta cika da farin ciki. haske yana ta wulkawa saboda murna da farin ciki. Ana hakan sai ga Fatima ta shigo. Sai Manzo ya ce mata '"Aliyu ne wanda kika sani ya zo yana naman ki da aure. ya kika gani?"" Sai ta yi shiru ba ta nuna aiamun ki ba. Sai Manzo ya yi kabbara. yana mai cewa "Shininta yardarta ne

Ummi Saltna ta ce ' Sai na ga fuskar Manzo ta cika da fann ciki da haskc saboda muma. Sai ya dubi fuskar Aliyu ya yi murmushi. Sai Manzo ya ce "Ya Aliyu kana da wani abu wanda za ka bayar in aurar maka da ita.1 Sai Aliyu ya ce: "Uwata da Ubana fansarka ne. Wallahi ba wani abu da zan boye makagame da alamarina. Ban mallaki komai ba sai takobina. sulkena da kuma abin sana ata wanda nake shayar da dabino ana__biyana. Sai Manzo ya ce: "Takobinka ba mai raba ka da shi. Da shi ne kake jihadi a tafarkin Allah. kakc kashe makiya addinin Allah. Abin sana'arka kuma ka bar shi don lyalinka. Saboda haka na aurar maka da Fatima a kan sadakmta shi ne sulkenka na yaki.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next