Mene ne Auren Mutu'a



Ma'ana:

"Kuma sune wadanda suke kare Al'aurar su (daga yin Jima'i da Mace) sai dai ga Matayen su ko kuma Kuyangin da suka mallaka to su ba ababen zargi bane, wanda kuwa ya nemi wanin haka to sun zamo masu ketare iyaka". (AL-mu'minuna: 6-7).

To amma abin lura anan shine, su wadannan Ayoyin guda biyu sun sauka ne a Makka, ita kuwa Ayar dake Magana kan Mutu'a ta sauka ne a Madina. Kuma abinda ya riga sauka baya shafe wanda yazo daga baya. Sannan ita Mutu'a aure ne, shi kuma wanda ake Mutu'ar dashi mace ce, don haka bazai yiwu a gwama wadannan Ayoyi guda biyu da Ayar dake Magana akan Mutu'a ba har ace maganar shafewa ta inganta.

Akwai kuma maganar da suke kawowa ta shafe Mutu'ar da Ayar Idda inda Allah yake cewa:

"فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِمْ"

Ma'ana:

"To ku sake su da Iddar su" (Addalak: 1)

Suna kawo cewar al'amarin Idda a wannan Aya ya shafe hukuncin auren Mutu'a wacce ita babu Saki babu Idda a cikinta.

Jawabi:

Hakika auren Mutu'a bai kasance ance babu Idda ba, Allahumma sai dai ace babu Saki a cikinsa. Idan muka komo kan aure a Musulunci ya kasu kashi biyu ne: Da'imi da Munkadi'i (Mutu'a), don haka zai kasance kenan ita Ayar Saki tana Magana ne kadai akan auren Da'imi ba Mutu'a ba. Domin alakar da take dawwamammiya (mutu-ka-raba) ce, itace take bukatar sanarwa akan kawo karshen alakar yayin faruwar wani dalili na hadari ayyananne. Amma alaka wacce take "Mu'akkita" wacce daman tuni anyi mata lokacin da zata kare bata bukatar wannan ambatawar, tana karewa ne yayin da lokacin da aka debar mata ya kare da yanayi na nan take. A irin wannan yanayi ne sai Ayar Saki ta zamo an barta har abada, babu wani abin kulawa a cikin ta game da auren Mutu'a, balle har ma takai ga ta zamo ta janyo shafe ta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next