Mene ne Auren Mutu'a



Ma'ana:

"Kuma Matayen da kuka yi Mutu'a dasu, izuwa wani kayyadajjen lokacin da aka ayyana, wajibi ne ku basu ladan su (Sadakin su).

Tare da gwamin jumla mai yin bayani karara a tsakiya wato:

"إلى أجل مسمى"

"Zuwa wani kayyadajjen lokaci"

Wanda bukatar su akanta shine bayyana ma'ana da bigire da fassarar ta. Sannnan wannan jumla bayyananna ba zata taba dacewa da auren Da'imi ba face Mutu'a.

2-    hakika lafazin "Mutu'a" koda ya kasance dai-dai ko ingantacce akan amfani ko nufin ma'anar auren Da'imi, to amma yafi fitowa balo-balo a sarari akan nufin auren Mutu'a ne. kamar yadda lafazin "Nikah" koda ya zamanto dai-dai da inganci wajen amfani ko nufin auren Mutu'a, to abinda shima yake balo-balo a sarari shine ana nufin kai tsaye auren Da'imi ne. wanda idan da babu wata alama a sarari, to da bazai yiwu a yarda akan tana nufin auren Mutu'a bane. A sannan sai ya zamo wani lafazi ne dake iya karbar sama da ma'ana guda daya kenan.

3-    Hakika Ayar mutu'a tazo ne cikin Suratun-Nisa' wacce ta fara da ambaton "An-Nikah" wato aure da auren Da'imi, da hukuncinsa a cikin Ayoyi na 3, da 4, da 20, da na 23. Idan har ya kasance abinda ake nufi da "Al-Mutu'atu" shine auren Da'imi har wala iyau to da wannan Aya ta zamo maimaici na neman ambaton abinda ya gabata cikin Surar.

4-    Da kuma "Al-Mutu'atu" ta zamo da ma'anar aure ne na Da'imi, to ina amfanin kuduri da "An-nuskhu" (wato an shafe ta) kenan? Ko kuwa suna nufin "Nuskhu" da an shafe hukuncin auren Da'imi ne?! To don haka Magana akan "An-Nuskhu" cewar an shafe hukuncin auren zai zamo wani karfafane akan Ayar Mutu'a, cewar tana nufin Aure ne "Al-mu'akkit" ai abin yiwa lokaci (Mutu'a) bawai Da'imi ba wato auren mutu-ka-raba.

NASSOSI DA HADISAI

Zamu yanke Sanadin Hadisin don kada rubutun namu ya tsawaita.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next