Mene ne Auren Mutu'a



ABU NA GOMA SHA TAKWAS

Sannan a auren Mutu'a ba wajibi ne Shaida ko Sanarwa ba, sannan ba Mustahabbi bane, duk da dai sun zamo Mustahabbine wajen kwanciyar hankalin su. Allahumma sai dai idan suna tsoron Tuhuma da Zina. To anan Mustahabbi ne a Sanar a Shaida.

ABU NA GOMA SHA TARA

Idan macen Karama ce baya halasta a daura auren sai da izinin Waliyyan ta, kamar Uba ko Kaka na Uban, kamar dai auren Da'imi.

Idan kuwa Baiwa ce to bai halasta sai da izinin Ubangidanta (Mai Mallakar ta). Idan kuma mai Mallakar ta ta mace ce to shima dai sai da izinin nata. A wata ruwayar kuma akace ya halasta ba tare da izinin nata ba (At-Tahzib: 7/257 lamba 1113, da Istibsar: 3/219 lamba 795). Amma Al-Mufid shi bai yarda da hakan ba. Sannan yin Jima'i da Ita ba tare da izinin ta ba (Uwargijiyar) amma kuma tare da izininta wajen kulla auren to shi yafi kyau (Al-Musnaf ya nakalto daga gare shi cikin Al-Mukhtalif: 7/232, da Al-Hilliy cikin Sara'ir:2/622) .

Idna kuwa 'Yantacciya ce Baliga mai Hankali, to wannan za a iya auren ta ba tare da izinin Waliyyi ba.

ABU NA ASHIRIN

Ya halasta a kulla auren Mutu'a da mace ba sau daya ba, sau da daman gaske daya bayan daya, idan lokacin da akayi ya fita na fari, kai koda ma lokacin Iddar ta bai kare ba. Sannan ya halasta a kulla wani auren da 'Yar'uwar ta bayan lokaci ya kare ko da bata fita daga Idda ba. Amma Ita bazai yiwu tayi wani auren da wani ba sai Iddar ta ta kare. Idan kuma bayan sun yi auren taga tana da bukatar kari a cikinsa kafin lokacin ya kare, to zata iya barin kwanakin na ta sannan a sake sabo zuwa lokacin da duk suka so.

MAS'ALOLI DABAN-DABAN

NA DAYA

Aure yana inganta yayin da daurashi ya zamanto ingantacce a Shari'a. Idan kace: "Tazawwajtuki" , (na aure ki) har zuwa, ko har lokacin da na Sadu dake, to wannan aure ya baci. Idan kuwa kace: na aure ki idan na Sadu dake to na Sake ki, to auren ya inganta, amma wannan Sharadi ya baci. Sannan tana da "Mahrul-Mumas- thal" wato Sadaki na kwatankwaci (akan auna Ta ne da Wata da aka bada nata Sadakin ta bangaren Nasaba, Kyau, Wadatar su, da sauran su). Da zai aure ta yana mai kudurin cewa zai Sake ta idan ya Sadu da Ita, ko kuma Ita tayi kudurin haka, ko kuma dukansu su biyun, ko kuma suyi Sharadin haka kafin auren, kuma sukayi to auren ya inganta. Kuma ya wajaba abinda aka ambata (na yin Sakin).

Dukkanin gurin da aka hukunta ingancin aure a cikin sa, to hukunce-hukuncen aure ya rataya gare shi. Sannan dukkanin gurin da aka hukunta bacin aure cikin sa, to hakika abinda yake tsarki shine Saduwa bata tabbata a cikin sa. To shin ya halasta ga mijin farko? Hakan mai yiwuwa ne, domin kuwa shi aure ne da tsarki yake tabbatar da shi kuma babu Haddi akansa, sannan wajibi ne bada Sadaki, haka nan yakan dauki rashin Sadaki, don kuwa shi aure ne da baya inganta da "Li'ani", don haka yana gudana ne dai kamar Kuyanga. Shaikhud-Dusiy ya karfafa hakan (Al-Mabsud: 4/348).

NA BIYU

Daidaito sharadi ne cikin aure, shine daidaituwa cikin Imani daga bangaren mijin kadai, baya halasta ga Mumina ta auri wanda ba Mumini ba koda ya kasance Musulmi. Amma ya halasta ga Mumini ya auri duk wacce yaso daga Musulmai. Sai dai Mustahabbi ne ya auri Mumina har wala iyau.

Shin yana daga Sharadi samarwa da mata "Nafakah"? a wani kaulin akace: I, sai dai abinda yafi shine ba Sharadi bane. To idan da kuma ya gaza ga "Nafakah" din fa? To anan akwai ruwaya biyu wajen ingancin zabin matar, mafi karfi shine rashinta (At-tahzib: 7/454 lamba 1817, da shafi na 462 lamba 1853, bayan kawo wannan Magana sai Al-Musnaf cikin Al-Mukhtalif: 7/327 "Mu muna daga cikin tsayayyu akan haka").

Ajami daidai yake da Balarabe, Balarabe daidai yake da Kuraishawa. Hakanan ya halasta ga Bahashimiya auren wanin ta, hakanan shima Bahashime. Hakanan ba'a lura da Sana'a, ya halasta ga mai makaskancin aiki kamar mai yin Kaho, ko mai Gadi, ko mai kula da Bandaki ya auri wacce take 'Yar Babban Gida, da 'Yar Manyan Mutane masu daraja, da masu manyan Sana'a, kamar manyan 'Yan kasuwa.

NA UKU

Yin Jima'i da wacce take Jini Haramun ne ta Farji, idan Jinin ya dauke to auren ya warware. Shin wajibi ne yin Wanka? To abinda yafi shine ba Sharadi bane. Sai dai Mustahabbi ne mai karfi. Idan kuma ka Sadu da Ita tana Haila to sai ka Tuba ga Allah, sannan Ta'aziri yana kanka. Kuma akan wajabcin Kaffara akwai Magana biyu, ka koma cikin Risala..

NA HUDU

Makaruhi ne ga wanda yayi mafarki ya Sadu da mace kafin yayi wanka, da zai yi Jima'i da mace bazai yiwu ya kuma koma mata karo na biyu ya Sadu da Ita ba, ko kuma ya Sadu da Wata ma ba Ita ba sai idan yayi wanka.

NA BIYAR

Yin "Istimna'i" (Azalo) da hannu Haram ne, kuma ya wajaba a yiwa mutum "Ta'aziri".

Dukkanin kurakuren da yake ciki daga gareni ne kuma ina fatan Ubangiji ya yafe mini ya karbi wannan aiki nawa. Allah Ubangiji yasa mu dace.

Nuruddeen Ibn Muhammad (Darus-thakalain (

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26