Mene ne Auren Mutu'a



"A yayin da yaga Dare (Annabi Ibrahim) ya raba Tauraro ya fito sai yace wannan shine Ubangijina ….., Da ya kuma ganin Wata ya fito sai ya sake cewa ah wannan shine Ubangijina ….., Da ya kara ganin Rana ta fito sai yace wannan itace Ubangijina don tafi girma ……,"

Wanda daga karshe yake ce musu Shi Ubangijinsa shine wanda baya gushewa, Ubangijin Dare, Rana, Wata …… Don haka ashe hankali wani abu ne mai darajar da akan fara gabatar da shi kafin Nassi. Domin da hankali ne ake gane kyawu da munin komai a tantance shi. Hattana shi kansa Addinin Musuluncin sai akace na masu hankaline, don hattana Sallah, Azumi da sauran Ibadu ma an dauke su ga wanda bashi da hankali. Don haka ya Dan'uwa mai Karatu ka gane hakika shi hankali wani abune muhimmi wanda Ubangiji ya tanadarwa mutum don amfani dashi wajen taimaka masa gano da tantance Gaskiya da Karya, Fari da Baki, Haske da Duhu da sauransu. Hakanne yasa Ubangiji ya sanya Hankalin ya zamo "Ma'asumi" a koda yaushe shi Hankali baya yin kuskure, sai dai mutum ya bi son ransa. Amma shi hankali kullum akan dai-dai yake sai dai zuciya ta karkata.

Misali, duk lokacin da mutum yaga abu to hankalinsa zai gaya masa ai wannan abun Fari ne. To baya taba yiwuwa Wani yace a'a ba Fari bane Baki ne ko Kore ne, duk kuwa wanda yazo a wannan Farin zai ganshi.. Allahumma sai Mahaukaci wanda shi bashi da hankalin. Don haka ne ma a wani Hadisin na Fiyayyen Halittu (Sallallahu alaiHi wa AliHi) yake cewa: "Kada ka aikata abinda hankalin ka bai kwanta da shi ba, ka aikata abinda hankalin ka ya kwanta dashi".

Don haka mu Mabiya Mazhabin Ahlul-Baiti (Alaihimus-salam) muka tafi akan Adalcin Ubangiji Ta'ala, har ya zamanto Adalci yana daya daga cikin Usuluddinin mu. Mun san cewar Ubangiji koda yaushe baya zaluntar  Bayinsa. Sannan kuma baya dora musu abinda baza su iya ba. Kamar yadda Yake cewa:

"لا يكلف الله نفسا إلا وسعها"   (البقرة – 286)

Ma'ana:

"Ubangiji baya dorawa Rai face abinda zata iya"

Sannan kuma Shi Ubangiji a koda yaushe yana aikata alheri ne ga Bayi ba Sharri ba. Idan kuwa kaga sharri to ba daga Allah bane daga gare ka ne, da fadinsa Madaukakin Sarki:

"وما أصابكم من مصيبة فبما كسبت أيديكم ويعفوا عن كثير"   (الشورى – 30)

Ma'ana:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next