Mene ne Auren Mutu'a



ABU NA GOMA SHA SHIDA

Sannan yayin da aure ya kare, idan ta kasance wacce take yin Haila, to wajibi ne tayi Idda zuwa jini biyu, idan kuwa bata Al'ada, to sai tayi kwana arba'in da biyar kafin tayi wani auren. Idan kuwa ma sam bai Sadu da Ita ba to babu Idda akanta. Sannan da zai mutu a lokacin suna auren to daga sannan sai ta fara lissafi zuwa wata hudu da kwana goma (Takaba), ya Sadu da Ita ne ko bai Sadu da Ita ba. Sai dai idan ta zamo "Ha'ila" (wacce bata Al'a wannan zatayi wata biyu da kwana biyar ne. Abisa abinda Shaikhul-Mufid ya tafi akansa (Al-Mukni'ah: 536).

Idan kuma ta zamo mai ciki, to zatayi lissafi ne da mafi nisan Ajali, wato zuwa Haihuwar ta. Sannan ko da Baiwa ce in daida) to "Ha'ila" ce to zatayi wata biyu ne da kwana biyar.

 

 

 

 

 

 

 

ABU NA GOMA SHA BAKWAI

Idna har lokacin da suka diba ya kare bai Sadu da Ita ba, to bai halasta ya Sadu da Ita ba har sai sun sake kulla wani auren sabo, koda kuwa abinda ya jawo daga gare shi ne ko daga gareta. Da za a ce kuma ta hana shi kwanakin sa bai Sadu da Ita ba, to bazai yiwu yace sai ta rama masa da wadansu kwanakin ba. Sai dai kurum a dawo masa da Sadakin sa idan ya riga ya bata.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next