Mene ne Auren Mutu'a



MAGANA TA UKU

MATSAYIN SAHABBABI DA TABI'AI AKAN AUREN MUTU'A

Wani dalilin daban akan rashin shafe ta shine Shaharar ta (Mutu'a) ga Sahabbai da Tabi'ai da "Fukaha'u" Malamai, har zuwa lokacin da Mazahabobi hudu suka kasance suna bayyana ta a fili a Karnoni na biyu na uku da na hudu.

Shaida akan haka kuwa shine abinda  Malam Bukhari da Malam Muslim a ingantattun litattafansu na Hadisi suka ruwaito na ruwayoyi daga Salma binul-Ak-wa' u bn Mu'id, da Jabir bn Abdullahil-Ansari, da Abdullahi bn Mas'ud, da Ibn Abbas, da Subrata bn Mu'id, da Abu Zarril-Gifari, da Imrana bn Hasin, da Ak-wa'u bn Abdullahil-Aslami. (duba: Sahih Muslim Sharhin Nawawiy: 9/179 – 189, da Sahihul-Bukhari Kitabut-Tafsir Babi na 33 Hadisi na 4156, da Kitabun-Nikah babi na 32 Hadisi na 4724, da Kitabul-I'itisam babi na 28 Hadisi na 6819).

Malam Muslim ya fitar a babin "Nikahul-Mut' ati" ruwayoyi da yawa daga Jabir bn Abdullah, da Abuz-Zubair, cewar su sun yi Mutu'a a zamanin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi), da zamanin Abubakar, har lokacin da Umar dan Haddabi ya hana.

A cikin Sahihul-Bukhari kuwa cewa yayi: an saukar da Ayar Mutu'a a cikin littafin Allah, mun aikata ta tare da Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) kuma Kur'ani bai sauka yana haramta ta ba kuma Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) bai hana ba har ya Rasu. Sannan wani mutum kawai yazo ya fadi son ransa. (Sahihul-Bukhari: 5/185).

Amma wadanda suka soke wannan haramcin, basu yarda da shi ba manyan Sahabbai ne kamar Imam Aliyy (Alaihis-Salam) da Abdullahi bn Abbas, da Jabir bn Abdullahil-Ansari, da Abdullahi dan Umar, da Abdullahi dan Mas'ud. Sannan akwai cikin Malaman Sunna a karni na daya dana biyu na Hijira da ya bada Fatawar ayi, kai yama aikata, shine Malam Abdul-Malik bn Juraij wanda yai wafati Hijira tana da shekara (149).

Malam Ibn Hazmin cikin Al-Muhalla yace: "Jama'a da yawa cikin 'Salafu' (Magabata) sun tabbatar da halascin auren Mutu'a bayan Manzo (Sallallahu alaiHi wa AliHi) daga cikinsu akwai Sahabbai, irin su Asma'u bint Abubakar, da Jabir bn Abdullahi, da Ibn Mas'ud, da Ibn Abbas, da Mu'awiyata bn Abu Sufyan, da Amru bn Huraith, da Abu Sa'idul-Khudriy, da Salmah, da Ma'abad 'Yayan Umayyata bn Khalaf. Sannan Jabir bn Abdullah ya ruwaito daga gurin baki dayan Sahabbai anayi tsawon zamanin da Manzo (Sallallahu alaiHi wa AliHi) yayi a Duniya, dana Abubakar da karshen Halifancin Umar ……

Gareka tarin Sahabbai da Tabi'ai da suka tafi akan halascin auren Mutu'a ba haramcin sa ba, sune:

1. Imrana binul-Hasin.

2.Abdullahi bn Umar.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next