Mene ne Auren Mutu'a



Kwarkwara wacce Hausawa kan kira da "Sadaka" nasan ba zakayi inkarin cewa har yanzu anan Kasar da wasu tsirari ana riko da Ita ba. Halascin Kwarkwara ya faro ne tun daga zamanin Fiyayyen Halittu Annabi Muhammadu (Sallallahu alaiHi wa Alihi), kamar yadda bayanin hakan ya gabata daga Hadisan Annabin da ya fito ta hanyar Abu Sa'idul-Khudriy. Wanda sun nuna cewa ita Kwarkwara ana samun tane daga Ganimar Yaki, wanda akayi shi tsakanin Musulmai da Kafirai. Ko kuma kai ka siya daga

To abin tambaya anan shine:  shin har yanzu ana Yaki tsakanin Musulmai da Kafirai ne da za'ace an sami Ganimarsu?! Ko kuwa su 'Yayayen wadancan ne abin yake gangarowa har kawo i yanzu?! Ko kuwa shima dan da Ubangijin Baiwa ya Haifa shima ba da ba ne Bawa ne?! Don dai ni nasan ko Yakin Shehu Usman dan Fodiyo babu Ganima a cikinsa, don kuwa Yaki ne tsakanin Musulmai da Musulmai (Muminai da Azzalumai). Shi kuwa ba a rikarwa duk wanda yayi Shahada guda biyu (wanda yayi Imani da Ubangiji da Manzon sa) Dukiya, Mata, da sauran su a matsayin Ganima. Duba cikin Tarihin da zai zo nan gaba, Halifa na biyu ne yake yiwa Halifa na daya hani daga Manzon tsira (Sallallahu alaiHi wa Alihi) akan Yakar wadanda basa bashi Zakka. Saboda yana ganin sun Shaida da Shahada biyu.

Don haka Yakin Shehu Usman ma tsakanin Muminai ne da Azzalumai, shi yasa aka kirawo shi da TAJDIDI. Wato Jaddada Musulunci. A Kasar Sa'udiyya yau kusan Shekaru Dari da motsi kenan da hana cinikin Bayi tunda Aali Sa'ud suka karbi Mulki daga hannun Turkawa wadanda da Kasar a hannun su take. Wanda shi kansa wannan cinikin Bayin tun na wancan lokacin gurbatacce ne a Addinin Musulunci. Don kuwa ya ginu ne akan zalunci, dukkansu Musulmi ne, amma sai suke Bautar da Ajnabi (mutumin da ya shiga Kasar Bako musamman ma Bakar fata). Kuma su kansu basu hanu ba sai da Sarkin ya rika bin duk wanda ke da Bawa yana yanka shi. Wannan ne ma yasa idan kace da Dan Sa'udiyya "Dajaj Sa'ud" wato Kajin Sa'ud, (Sa'ud din Sarkin Makka ne na wancan lokacin), to sai dai Shari'a ta raba ku dashi. Domin kuwa haka ya rika bin Kakanninsu yana yankawa kamar Kajin, saboda sunki su daina bautar da Mutane. To ina ga kuma

To abin lura anan nasan dai mai Karatu kasan cewa: Mai Martaba Wane, da Mai Girma Wane, da Shehi Wane, da Malam Wane, da Alhaji Wane, dukkansu suna da Kwarkwarori! Ga Wane da Wane nan duk ka sansu tare kuka taso tun kuna Yara 'Yayan Kwarkwarori ne. Abin tambaya anan ta yaya aka samo su wadannan Kwarkwarorin a irin wannan lokacin wanda tsawon lokaci ya yanke daga samun halastattun Bayi irin wadanda Addinin Musulunci ya yarda da su musamman ma mu a wannan Nahiya? Bazai taba yiwuwa ace Shehi Wane a irin girmansa, da Mai Martaba Wane a irin martabarsa da Alhaji Wane basu san haka bane. To idan kuwa sun sani yaya matsayin 'Yayayen nasu? To la budda akwai wani boyayyen sirri a bayan

A tunanina ni nasan darajar Shehi Wane da iliminsa bazai taba yiwuwa ace ya yarda yana aikata abinda Shari'ar Musulunci bata yarda da shi ba. Don haka ni nake ganin anya kuwa ba suna ninke mutane bai-bai bane, su tsira daga canjin Suna kada a jefesu da wani bangaranci na Addini. Ko kuma Jama'a ta watse ta barsu, dan abin shan miyar da suka saba samu daga Dalibai ko Yara ya sullube musu? Saboda su kansu sun yi tunanin cewar: "KODA YAUSHE DAN ADAM YANA MATUKAR GABA DA ABINDA YA JAHILTA" yasa suce kurum Kwarkwarorine tunda yawancin Al'uma sun tafi akan halascin Kwarkwarori a yanzu. Don haka sai su rika kulla Auren mutu'a dasu, amma a zahiri sai suce Kwarkwarori ne. To abin dai na bukatar dogon Nazari da Tunani. Allah yasa mu dace.

Tunda mun samu cewar ba lallai sai ta hanyar Daurin aure Mace kan halasta ga Namiji har ya Sadu da Ita ba. Akwai wasu hanyoyin daban. To mai zai hana Al'umma ta rika yiwa Mutu'a kallo irin na alakar Kwarkwara? Don haka su ma daina kara kalmar aure din, suce Mutu'a kai tsaye. A matsayin dai itama wata hanya ce da Addinin Musulunci ya halasta ta, Mace da Namiji su gudanar da wata alaka ta Sirri kamar yadda Addini Musulunci

SHIMFIDA

Yana da kyau kafin mu kutsa kai tsaye cikin zurfin ramin bayani kan "Mutu'a", mu dan gangaro da bayani dan kadan akan Shari'a da Hukunci. Dukkanin wata Shari'a ko Hukunci suna farowa ne daga Ubangiji Madaukakin Sarki, daga nan sai Fiyayyen Halittu Annabi Muhammad (Sallallahu alaiHi wa Alihi), amma shima kansa Manzon (Sallallahu alaiHi wa Alihi) sai yayin da akace ne babu wani Hukunci akan abin daga Ubangiji Madaukakin Sarkin, to sannan ne sai ya zartad da nasa Hukuncin akai. Amma yayin da ya zamanto Ubangiji ya yanke nasa Hukuncin akai to bazai yiwu a tashi wannan Hukunci na Allah ba. Haka nan abu ne marar yiwuwa ace Hadisi ya tashi hukuncin Ayar Ubangiji. Domin maganar Manzo in dai har tasa din ce bata sabawa da Maganganun Allah mudlakan.

Sannan kuma bayan Manzo (Sallallahu alaiHi wa Alihi) sai "Fukaha'u" Manyan Malamai wadanda suka kai matsayin "Mujtahidai" , suma sai idan ya kasance babu Hukuncin daga Ubangiji da Manzonsa ne suke da damar shiga cikin Kur'ani da Hadisan Manzo su fitar da Fatawa akan abinda ya taso babu yankakken Hukunci akan sa daga Kur'ani da Hadisi. Don haka bai yiwuwa batatan bayan Ubangiji da Manzonsa sun yanke wani Hukunci na Halasci ko Haramci akan wani abun a sami wani mutum daban ya tashi wannan Hukuncin, da fadar sa Ubangiji Madaukakin Sarki:

"وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلاَ مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى الله وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَنْ يَكُونَ لَهُمُ اْلخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَنْ يَعْصِ اللهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلاَلاً مُبِينًا"                        (الأحزاب – آية 36)

Ma'ana:

"Kuma baya taba yiwuwa ga Mumini ko Mumina idan Ubangiji da Manzon sa suka Hukumta wani lamari suce ga wani zabin (Hukumcin) ba nasu ba, duk wanda ya sabawa (Hukumci ko maganar) Ubangiji da Manzon sa to hakika wannan Mutum ya bata Bata mabayyani". (Ahzab:36)



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next