Mene ne Auren Mutu'a



Da yake ni ina rayuwa ne a wannan Nahiya ta Najeriya, kuma Ubangiji na kowa da ko'inane. Me zaka ce akan mutanen da basu da halin aure, kullum fama suke da abinda zasu kai bakinsu, sannan a gefe guda kuma ga Sha'awa tana sasakar su kamar sun banke Mace? Sannan gashi ita wannan sha'awar halittace, sannan kuma an haramta musu yin Zina. To ya Dan'uwa Musulmi tambaya anan ina Adalcin Ubangiji yake? Ya sanya masa Talauci, ga Sha'awa, ga ya haramta masa Zina, duk a lokaci daya.

Halittun Allah suna da yawa basu da iyaka, kaga Kyakkyawa kaga Mummuna kaga Tsaka-tsaki. Idan muka zakulo Matayen da suke Munana, wadanda rashin kyawun su ya hana su Auruwa, alhalin gasu suna da Jiki Kyakkyawa na Sha'awa, amma kash! Muninsu yafi tasiri. To me zakace akan wannan Baiwar Allah da ta taso tana Sha'awa, aure ya faskara, kuma idan batun da Saduwa ne (Jima'i) akwai wadanda za a samu su taba su tashi. Gashi an haramta mata Zina. Kana nufin ta zauna a haka cikin wannan kuncin?

Ina Zawarawa? Wadanda suka dandani aure, yazo ya sullube, tsawon lokaci wani auren ya faskara, anyi Addu'ar, anyi yawo da hoton, shiru kamar an shuka Dusa. Ga sha'awa suna fama da ita, musamman su da sun dandani aure sun saba da kwanciya da Namiji. Shin kana nufin su zauna a haka cikin irin wannan kuncin wanda duk da kuncin Talauci bai kai shi ba? Akwai ire-iren wadannan da yawa ba zasu kidanyu ta dadi ba, kai ma ka taya ni kawowa.

A hakikanin gaskiya abinda yake a fili shine, idan muka baiwa Kwakwalwar mu 'Yanci, muka bi abin ta hankali zamu taras anan Adalcin Ubangiji bai tabbata ba, kuma za a iya siffanta Ubangiji anan da Zalunci. Koda yake watakila yanzu wani yace kunji shi ya dora misali karkashin hankali, har yace to ai Shari'a sabanin hankali ce. Shin baka duba fadin Ubangiji bane inda yake cewa cikin Littafinsa mai Tsarki:

"أفلا تعقلون ...,     أفلاتعلمون ...,      أفلا تتدبرون ....,    لأول الألباب ...,"

Ma'ana:

"Shin ba zaku hankalta ba …,    ga Ma'abota hankali …,"

Ai Ubangiji ma kansa yana yin maganane ga masu hankali ne ba marasa hankali ba. Dubi mana lokacin da Annabawa kan yi kira ga Al'umar su, kafin komai sai sun fara kafa musu hujja ta hankali tukuna kafin sukai ga kaiwa maganar Jalla Tabaraka. Me Kur'ani yake bamu labari akan Annabi Ibrahim (Alaihis-salam) ? Cewa yayi:

"فلما جن عليه الليل رءا كوكبا قال هذا ربي ......, فلما رءا القمر بازغا قال هذا ربي ......, فلما رءا الشمس بازغة قال هذا ربي هذا أكبر ......,"    (الأنعام 76-78)

Ma'ana:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next