Mene ne Auren Mutu'a



Mene ne Auren Mutu'a

Bismillahir Rahmanir Rahim

Alhamdu lillahi Rabbil Alamin, wa afdhalus salati wa atammut taslim ala Khatamil Anbiya'i wal Mursalina Muhammadul Musdafa wa Alihid Dahirinal Mujtabin, allazina azhabal Lahu anhumur rijsa wa dahharahum tadhira.

Lokuta da daman gaske nakan rasa gane menene kan fusata mutum har yayi munanan lafazai yayin da yaji an furta kalmar "Mutu'a". To amma da na dan yi dogon tunani sai naga ashe ba sasakai ba, babu makawa a bayan wannan kalmar akwai wani boyayyen abu, ba wai kalmar bace kadai. Domin kuwa da na yi tunani kan wadannan kalmomi na JAKI DA ZAKI, akan menene ke fusata mutum yayin da aka kira shi da Jaki, kuma menene ke dadada masa yayin da aka kira shi da Zaki? Sai mu ga ashe a dai-dai lokacin mutum kan hararo wata halitta ne mai dauke da wannan Suna. Don haka a lokacin ba yana kallon Sunan bane a matsayin wasu harafai guda hudu (J-A-K-I, Z-A-K-I) a'a yana kallon wannan sunane a matsayin Siffar Dabba mummuna ko kuwa kyakkyawa.

To idan hakane me ke faruwa ga kalmar "Mutu'a" da har idan mutm yaji an ambace ta kan fusata har yayi mummunan furuci? Shin irin abinda yake faruwa ne akan kalmar Jaki ko Zaki? Don haka ashe lokacin da kalmar Mutu'a take tsirgawa cikin Kunnen mai sauraro ba komai Zuciyar sa ke kawo masa ba illa ga wasu mutane guda biyu Namiji da Mace a kwance cikin aikata wata alaka da shi a tunanin sa, aure ne kadai kan shiga tsakaninsu har Addinin Musulunci ya amince da wannan alaka tasu. saboda haka kasantuwar wannan yasa yake kallon "Mutu'a" da wani irin kallo na daban.

Shin aure ne kadai kan sa Musulunci ya amince da wata alaka ta Jima'i tsakanin Namiji da Mace?! Amsa a'a! Ba lalle sai da aure a tsakanin ka da Mace zaka iya hulda da Ita har kuyi Jima'i ba. Idan muka duba cikin littafin Allah mai tsarki zamu samu Allah Madaukakin Sarki yana cewa:

"وَاْلمُحْصَنَاتُ مِنَ اْلنِّسَاءِ إِلاَّ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانِكُمْ........"

Ma'ana:

"Kuma da Mata masu aure banda abinda hannuwan ku suka mallaka (Baiwa)"

Malam Ibn Kathir ya fada a cikin littafinsa na Tafsiri cewa ita wannnan "Illaa maa malakat aimaanikum" ana nufin banda abinda hannuwanku suka mallaka na Fursunonin Yaki, domin kuwa su halas ne gareku, kuyi Jima'i da su yayin da sukayi Istibra'i, (yace) hakika wannan Aya ta sauka ne akan haka. Sannan yace: Malam Ahmad Hanbali (cikin littafinsa) 2/72, yace: "Munzo da Fursunonin Yaki daga Fursunonin Yakin ranar "Audas" a cikin su akwai Mata. Sai muka ki muyi tambaya akansu, akwai Mata a cikin su. Sai Annabi (Sallallahu alaiHi wa Alihi) ya tambaye mu, a take sai wannan Ayar ta sauka, aka halasta mana Farjinsu (Tafsirin Ibn Kathir: juzu'i na 1, shafi na 474).

Sannan Malam Muslim ya fitar ta hanyar Sa'idu dan Abii Urwata daga Katadata daga Abil-Khalil Alkamatul-Hashimiy daga Abi Sa'idul-Khudriy, Hakika Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi) ya tura Runduna zuwa "Audas" ranar Hunainu suka riski Makiya inda suka cimmasu, sukayi galaba akansu, suka kamo Fursunonin Yaki. Sai mutane daga Sahabban Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa Alihi) suka zamanto abin gwasale daga masu ziyartarsu a dalilin matansu, daga ciki akwai Mushrikai. Sai Allah Ta'ala ya saukar da "Wal-muhsanatu ……" ai su halasne gareku idan sun gama Idda. (Al-Aja'ib fii bayanil-Asbab: juz'i na 2, shafi na 855).

Da wadannan takaitattun Hadisai zamu fahimci cewar akwai wata alaka da Addinin Musulunci ya yarda da ita, wacce ta halastawa Namiji Saduwa da Mace, wato hanyar mallakar Baiwa. Babu wani batun daura aure sai dai kawai ka jefa ta Daki abinka. Don hakane ma ta samo suna a Hausance da (Sadaka),wato ka saka a Daki. Sannan wani abin a kula game da Sadaka ko Kwarkwara (Baiwa) shine, babu wani maganar Saki fa illa yayin da ka siyar ko ka bayar da ita (Baiwar) shine Sakinta. To kaga ashe Ala gafarta Mallam bawai ta hanyar Daura aure ne kadai Mace ke halasta ga Namiji ya Sadu da Ita ba.

In dai har kana kyamar Mutu'a don rashin bayyana Daurin aure a fili ne, to ya zaka ce kuma akan Kwarkwara da itama ba a bayyana Daurin auren ta bilhasali ma ita Kwarkwara babu wani Daura aure kwata-kwata a wajen mallaka?! Ko kuwa kana kyamar tane don babu Saki a cikinta? To idan haka ne yaya zaka ce kenan akan Kwarkwara da itama babu Saki a wajen rabuwa da Ita? Sakin ta shine ka sayar ko bayar da ita shike nan alaka ta kare. Idan kuwa tunanin ka ya tafi ne wajen rashin Wajabta Ciyarwa, Shayarwa, Dawwamammen Matsuguni, to yaya zaka ce akan auren Da'imi da shima wadannan hakkokin kan saraya yayin da Matar ta zamo Ballagaza marar kama kai, kuma auren ya cigaba a hakan? Shin zaka iya kace zaman da Shari'a bata yarda da shi bane shima?!



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next