Umar da Ra'ayin Shari'a 2



Hakika macijiya ta yi kisa a Badni Wadi

Ya na mai shayarwa ga 'yan'uwa masu baiwa

Ba ta bar wani makiya ba a ganina

Har zuwa san'a'a da ake neman sa da wani abu.

Sai labari ya je wa Umar dan khaddabi, sai ya yi fushi mai tsanani ya ce: Ba don dai sunna ba ce, da na yi umarni kada a sauki wani bayamane (bayamme) bako har abada, kuma da na rubuta haka a duk fadin duniya. Sannan sai ya rubuta wa gwamnansa na yaman cewa ya kama mutanen nan da su ka sauka gun Abu kharash alhuzali sai ya lizimta musu biyan diyya ya kuma cutar da su bayan nan da ukuba da zai yi musu sakamakon aikinsu[27]!!.

 

Daga ciki, akwai tsayar da haddin zina inda bai tabbata ba

 Wannan ya faru ne cikin abin da Ibn sa'ad ya fitar game da halayen Umar shafin 205 na juzu'I na uku a littafinsa na Dabakat da sanadin mai kyau, cewa wani dan sako ya zo wurin Umar sai ya yada jakarsa, sai wata takarda ta bayyana sai ya dauka ya karanta ta, sai ga shi a cikinta an rubuta:

Saurara Ka isar wa baban Hafsu wani dan sako

Fansa gare ka daga dan'uwa, don amincin matata

'yan matanmu Allah ya shiryar da kai cewa mu



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next