Umar da Ra'ayin Shari'a 2



Daga ciki, yin amfani da leken asiri kuma an hana yin sa

Ubangiji madaukaki ya na cewa: "Ya ku wadanda ku ka yi imani ku nisanci mafi yawan zato, domin sashen zato zunubi ne, kuma kada ku yi leken asiri, kuma kada wani ya yi da wani a cikinku, shin waninku ya na son ya ci naman dan'uwansa alhlain ya na matacce, to ku ki hakan, kuma ku ji tsoron Allah, hakika Allah mai yawan karbar tuba mai yawan jin kai ne", Hujurat: 12.

A cikin ingantattun ruwayoyi daga manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) cewa: Na hana ku zato, domin zato shi ne mafi karyar magana, kuma kada ku yi binciken sirri, kada ku yi leken asiri, ko algus, ko hassada, ku juya baya, ko fushi da juna, ku kasance bayin Allah 'yan'uwa.

Sai dai ra'ayin Umar yayin halifancinsa shi ne yin leken asiri don amfanin al'umma da gyara daula, sai ya kasance ayan yawon da dare, ya na kuma leken asiri da rana, har sai da wata rana ya na yawon dare ya na leken asirin mutane ya ji wani mutum ya na waka a gidansa sai ya haura katangar mutumin, sai ya samu wata mata da kuma kwanon giya a wurinsa, sai ya ce ya kai makiyin Allah shin ka na tsammanin Allah ya suturta maka alhalin ka na kan wannan sabon?. Sai ya ce: Kada ka yi gaggawa ya sarkin muminai, idan ni na yi sabo daya to kai ka yi uku ne. Allah ya ce: "kada ku yi leken asiri" Hujurat: 12, kuma kai ka yi leken asiri. Kuma ya ce: "Ku shiga gidaje ta kofofinsu" Bakara: 189, kai kuma ka haura ta Katanga. Kuma ya ce: "Idan za ku shiga gida ku yi sallama" Nur: 61, kai kuma ba ka yi sallama ba. Sai ya ce: Shin ka na da wani alheri da za ka yi idan na yi maka afuwa? Sai ya ce: Haka ne. sai ya yi masa afuwa ya fita[18].

Daga sadiyyu ya ce: Umar dan khaddabi ya fita sai ga wani haske a tare da shi kuma akwai abdullahi dan mas'ud, sai ya bi wannan hasken har sai da ya shiga wannan gida, sai ga fitila a wani gida, sai ya shiga shi kadai, ya bar dan mas'ud a waje, sai ga wani tsoho a zaune a gabansa akwai abin sha na giya, ga wata mata ta na yi masa waka, kuma bai an kara ba sai ga Umar ya yi masa hujumi, sai ya ce: Ban taba ganin wani mummunan abu ba irin ganin tsoho da ajalinsa ya ke sauraronsa amma ya na irin wannan, sai tsohon ya daga kansa ya ce: Abin da ka yi ya fi abin da ka gani daga gare ni muni saboda kai ka yi leken asiri kuma Allah ya hana leken asiri, kuma ka shiga ba tare da izini ba. Sai Umar ya ce: Ka yi gaskiya.

Sannan sai ya fita ya na mai cizon tufafinsa ya na ku ka. Ya ce: Kaicon uwar Umar, har dai inda ya ke cewa:

Sai wannan tsohon ya kauracewa majalisin Umar yayin nan, sai wata rana bayan nan Umar ya na zaune sai ga wani ya zo ya na dan boye kansa, har sai da ya zauna can karshen mutane, sai Umar ya gan shi sai ya ce: Ku kawo mini wancan, sai aka ce masa: Amsa wa sarkin muminia, sai ya tashi ya na ganin kamar ko Umar zai muzanta shi saboda abin da ya gani gare shi ran nan. Sai Umar ya ce: Matso kusa da ni, bai gushe ba ya na kusanto da shi har sai da ya zaunar da shi kusa da shi, sai ya ce; ku santo kusa da ni, sai ya kusanto kusa da shi, sai Umar ya ciji kunnensa, sannan sai ya ce da shi: Na rantse da wanda ya aiko da Muhammad da gaskiya ban ba wa wani mutum labarin abin da na gani daga gare ka ba, koda kuwa Ibn mas'ud da ya ke tare da ni[19].

 Daga sha'abi: Umar ya rasa wani mutum daga sahabansa, sai ya ce da dan auf: Zo mu ta fi gidan wane mu gani, sai su ka su ka ta fi gidansa, sai su ka samu kofarsa a bude ya na zaune, matarsa ta na zuba masa wani kwano na giya ya na sha. Sai Umar ya ce da dan auf: Ka ga abin da ya hana shi zuwa wurinmu. Sai dan auf ya ce da Umar: Yaya ka san ko mene ne cikin kwanon? Sai Umar ya ce: Shin ka na jin tsoron kada wannan ya zama leken asiri ne? sai ya ce: Leken asiri ne mana. Sai ya ce: Yaya zan tuba daga wannan? Sai ya ce: Ka nuna ba ka san mene ne ka gani ba kan lamarinsa...![20]!

Daga musawwar dan makhrama, daga abdurrahamn dan auf: Cewa ya yi gadin garin madina tare da Umar dan khaddabi wata rana da dare, su na cikin tafiya sai ga wata fitila a wani gida, sai su ka ta fi suan bin ta, yayin da su ka kusanci wurin sai ga wata kofa a kulle da wasu mutane a ciki, ga kuma magana ana yi sama - sama da lagawu a cikinta, sai Umar ya kama hannun Abdurrahman dan auf ya ce amsa: Wannan tgidan rabi'a dan umayya ne, kuma ga shi yanzu su na shan giya yaya ka ke gani? Sai ya ce: Ina ganin mun yi abin da Allah ya hana na leken asirin mutane, sai su ka juya su ka bar su!.[21]

Daga dawus: Umar ya fito wata rana sai ya wuce wani gida da wasu mutane su na shan gida sai ya daga murya ya na cewa: Fasikanci? Fasikanci?, sai wasu su ka ce: Ai Allah ya hana ka wannan, sai Umar ya koma ya bar su!.

Daga abu kilaba ya ce: An ba wa Umar labara cewa abu mahjan assakafi ya na shan giya a gidansa shi da abokansa, sai uamr ya ta fi har sai ya shiga wurinsa, sai abu mahjan ya ce: Ya kai sarkin muminai wannan bai halatta gare ka ba, alhalin Allah ya hana ka leken asiri, sai Umar ya tambayi zaid dan sabit da Abdurrahman dan arkam, sai su ka ce ya yi gaskiya: Sai Umar ya fita ya bar shi!![22]!!



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next