Umar da Ra'ayin Shari'a 2



Haka nan ne wannan abin takaici ya kare da lafazinsa daga Ibn khalikan, sai ka koma tarihin yazid dan ziyad alhimyari, a juzu'I na biyu na littafin wafayatul a'ayan.

Hakim ma ya kawo wannan lamarin a tarihin Mugira a shafi na 448 zuwa baya, a juzu'I na uku na sahihinsa mustadrak, kuma zahabi ya kawo shi a cikin talkhisul mustadrak kuma, kuma ya yi nuni zuwa ga tarihin dukansu na Mugira, da na abubukrata, da nafi'u, da shibli dan ma'abad, da dukkan masu kawo tarihin abin da ya faru na shekarar 17 hijira na daga masu tarihi.

  

Daga ciki, tsanantawarsa ga jabalata dan aiham dan abi shimr algasani

Wannan kuwa ya faru ne lokacin da ya zo masa a tare da shi akwai mahaya 500 na kabilar akka da jafna, su na masu damuwa da sha'aninsu na larabci, kuma su na da kayan saka na zinare da azurfa, a gabansu akwai jabalata, wanda a kansa ya na sanye ne da hularsa ta iko, wanda a cikinsa akwai wani dan kunne na kakarsa mariya, sai su ka musuluinta gaba daya, sai musulmi su ka yi farin ciki mai tsananin da su da kuma abin da su ka gani na mabiya masu yawa da su ke da shi, kuma a wannan shekarar sai jabala da shi da sahabbasa su ka halarci aikin Hajji tare da halifa, su na cikin yin dawafi a dakin Allah sai wani mutum daga kabilar fazara ya taka rigar jabala, sai ya mare shi, sai wannan mutumin farazi ya nemi sai ya rana, sai Umar ya nmei lallai jabala ya ba shi dama ya rama ko ya yi wani abu da zai yardar da shi, sai Umar ya kuntata wa jabala kan hakan har sai da ya samu yanke kauna, yayin da dare ya yi sai ya fita da his da sahabbasa har sai da su ka zo kisdandiniya sai su ka koma kiristoci gaba daya su na masu nisanta da kyarmar rashin yafiya da afuwa da su ka gani daga musulmi da jagoransu, kuma sun samu matsayi mai daraja da karrama da girmama a wurin Hirakal a can fiye da yadda su ke tsammani[28], amam duk da haka jabala ya kasacne ya na ku ka saboda abin da ya kubuce masa na rashin sanin musulunci ya na mai waka ya na cewa:

Masu dara sun zama kiristoci saboda mari

Kuma da na hakura kansa da babu wata cutuwa

Sai ga jin kai da isa sun hana ni karbar hakan

Sai na sayar da idanu mai gani na karbi makaho

Ina ma dai uwata ba ta haife ni ba, kuma ina ma dai

Na koma zuwa ga maganar nan da Umar ya gaya mini



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next