Umar da Ra'ayin Shari'a 2



A sahihul buhari ya zo haka nan daga anas dan mali cewa abdullahi dan huzafata ya tambayai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) cew: Waye babana? Sai ya ce: Babanka shi ne huzafata.

A sahih muslmi ya zo cewa: Ana kiran sa da jingina shi ga wanin babansa, yayin da babarsa ta ji tambayarsa wannan sai ta ce: Ban taba jin dan da ya saba wa babarsa ba fiye da kai, shin ka yarda da cewa babarka za ta iya zuwa da abin da matan jahiliyya su ke yi ne sai ka kunyata ta a gaban idanunwan mutane. Sai Umar ya durkusa gabanta a kan gwiwarsa a gaban manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya na mai kayatar da jin dadin gaskatawar da annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi wa uwar abdullahi dan huzafata a nasabarsa ya na mai cewa: Mun yarda da Allah ubangiji, musulunci addini, Muhammad annabi[26].

Ya fade ta ya na mai annashuwar jin dadin suturtawar manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ga mata masu yawa da su ka yi masha'a a cikin jahiliyayya, kuma musulunci ya riga ya shafe abin da ya ke gabaninsa.

 

Daga ciki, canja hukuncin shari'a da wani umarni da shi ya zaba babu wani dalili

Dagar irin wanna akwai wani yaro na hadib dan balta'a da su ka yi tarayya cikin satar taguwar wani mutum daga muzaina, sai aka zo da su waurin Umar sai su ka yi furuci, sai Umar ya umarci kasir dan assalt ya yanke hannayen su, yayin da aka ta fi da su, sai Umar ya dawo da su wurinsa, sannan sai ya kira dan maulansu wato Abdurrahman dan hadib ya ce masa: Amma wallahi da kun kasance ku na sanya su aiki ku na yunwata su da na yanke hannayenku. Wallahi duk da ban yi ba, amma sai na yi mu ka izaya da za ta ji maka ciwo. Zuwa karshen abin da ya kasance na abin da ya faru, sai ka koma wa shafin 32 da abin da ya ke bayansa na juzu'I na uuk daga litafin A'alamul muwakki'in. kuma allahama Ahmad bin ya kawo shi a littafinsa na (fajarul islam) shafin na 287. Kuma Ibn hajar askalani ya yi nuni da hakan a bayaninsa game da Abdurrahman dan hadib yayin da ya kawo wannan a kisimi na biyu na littafin Isaba ya na ce: Ya na da wani lamari tare da Umar.

Na ce: Ta yiwu abin da Umar ya yi na ture haddi daga wadannan 'yan samarin ya zama ya na da wani dalili, wannan kuwa saboda sata ba ta kasancewa sai da wani dalili kamar yunwa da ta sanya su tilas su yi sata don su samu abin toshe yunwarsu domin su zama cikin wadanda Allah ya yi nufi da fadinsa : "wanda duk ya bukatu ba mai zalunci ko shisshigi ba to babu laifi gare shi", Bakara: 173.

Sai dai su sun yi furuci da yin sata da ta tabbata kansu ba tare da sun yi da'awar wata larura ba da ta sanya su yin sata, kuma da sun ma yi da'awarta, to da ya hau kan shugaban musulmi da ya nemi su tabbatar da it a, sai dai mu ba mu ga wani abu ba daga gare shi, in banda tausaya musu ya na mai tsanantawa kan dan hadib, ba mu sani ba ta yaya ya san cewa sun kasance su na yunwata su da wannan yunwar?

  

Daga ciki, karbar diyya daga wadanda ba ta wajaba kansu ba, kuma ba su ne masu alhakinta ba

Da wani bayani da ya fi inganci wato karbar diyya inda ba a shar'anta ta ba.

Wannan kuwa ya faru ne yayin da Abu Kharash alhuzali sahabi ne mawaki, wasu mutane dayaman sun zo wurinsa su na masu Hajji, sai ya dauki salkarsa ta ruwa, sai ya ta fi wurin ruwa da dare har sai da ya samo musu ruwa da za su sha, sannan sai ya zo ya na dawowa sai wata macijiya ta sare shi kafin ya kai gare su, sai ya dawo har sai da ya kawo musu ruwan, sai ya ce: Ku dafa akuyarku ku ci. Bai gaya musu abin da ya same shi ba, sai ya su ka kwana suan ci har sai da safiya ta yi, sai ga Abu kharash matacce, ba su bar inda su ke ba har sai da su ka binne shi, ya fada ya na mutuwa a wakarsa cewa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next