Umar da Ra'ayin Shari'a 2



Kuma Ibn jari dabari da Ibn asir alajari sun kawo a tarhinsu cewa: Ansa dan Nadhar wanda ya ke shi ne ammin ansa dan mali ya zo wurin Umar da Dalha da wsu muhajira sun jefar da abin da ya ke hannunsu, ya ce: Me ya ke tsyar da ku . sai su ka ce: An kashe annabi. Sai ya ce: To me ke nan kuma za ku yi da rayuwa bayansa? Ku tas hi ku mutum a kan abin da ya mutu a kansa. Sannan sai ya durfafi mutanen kafirai ya yi ta yin yaki har sai dai aka kashe shi, sai aka samu sara da su ka saba'in a jikin sa, har babu wanda ya gane shi sai wata 'yar'uwansa, ita ma ta gane shi shi ne da yatsunsa.

A wata ruwayar ya zo cewa: Ansa dan Nadhar ya ji wasu daga sahabbai daga cikinsu akwai Umar da dalhar su na cewa: Ina mai dai za mu samu wanda zai je wurin abdullahi dan ubayyu don ya karbar mana aminci gun abu sufyan kafin su kashe mu, sai ansa ya ce musu: Ya ku mutane idan an kashe Muhammad to ai ubangijin Muhammad shi bai mutu ba, ku yi yaki a kan abin da a kansa ne muhammd ya yi yaki, sannan sai ya ce: Ya ubagnij ni ina barranta gun ka daga abin da wadandannan su ka ce - ya na nufin musulmi su Umar - ina kuma barranta gun ka daga abin da wadanann su ka yi - ya na nufin kafirai - . Sannan sai ya yi yaki har sai dai ya yi shahada[2].

Daga ciki akwai yakin hunain fadin Allah madaukaki "Yayin da yawanku ya kayatar da ku, kuma bai wadatar da ku komai ba[3], duniya ta yi muku kunci duk fadin ta, sannan sai ku ka juya ku na masu bayar da baya. Sannan sai Allah ya saukar da nutsuwa kan manzonsa da kuma kan muminai", Tauba: 25 - 26. wannan ya na nuni da wadanda su ka tabbata tare da shi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ne yayin da sahabbansa su ka gudu su ka bar shi, kuma daga cikin wadnda su ka gudu da akwai Umar dan Khaddabi kamar yadda buhari[4] ya kawo shi a hadisin da ya karbo daga Abu katada al'ansar yayin da ya ce: Sai musulmi su ka waste a ranar yakin hunai, kuma na gudu tare da su, sai ga Umar dan khaddabi tare da mutane, sai ya na ce masa, : Me ya samu mutaen ? sai ya ce: Lamarin Allah ne.

Daga ciki akwai ranar da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ta fi yakin Khaibar, sai ya aik Abubakar sai ya ta fi sai su ka gudu har sai da ya dawo[5].

An karbo daga Imam Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) cewa: Yayin damznon Allah ya ta fi Khaibar sai ya zo ya aika Umar tare da wasu mtuaen zuwa gaeinsu, ba su dade ba sai ga su sun gudo Umar da shi da sahabbansa, sai su ka zo su na cewa da shi matsoraci, shi mayana cewa da su matsorata…hadisi[6].

Daga jabir dan abdullahi a wani hadisi mai tsayi da hakim ya kawo shi kuma ya ingantan shi a littafinsa na mustadrak[7], ya na mai fadi a cikinsa: Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Gobe zan ba wa wani mutum da Allah da manszonsa su ke son sa tuta, shi ma ya ke son su, ba ya bayar da baya, Allah zai yi budi a hannunsa, sai kowa ya rika daga kansa ya na neman, kuma a ran nan Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya na ciwon ido, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya gaya masa wani sirr. Sai ya ce: Ya ma'aikin Allah ba na ganin wani wuri, sai ya yi msa tofi a ido, sai ya ba shi jama'a ya ba shi tuta. Sai Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya ce: A kan me zan yake su? Sai manzon Allah sa ya ce amsa a kan su yi sheda da babu abin bauta sai Allah, kuma ni ma'aikin Allah ne, idan su ka yi haka, to sun kare jinisu da dukiyoyinsu daga gare ni, sai da da hakkinsu, kuma hisabin su yaan ga Allah madaukaki, ya ce: Sai ya hadu da su, Allah ya yi budi ta hannunsa.

Daga ayas dan salama, ya ce: Babana ya ba ni labari ya ce: Mun halarci yakin Khaibar tare da manzon Allah ya yin da ya yi tofi a hidanuwan Ali sai su ka warke, sai ya ba shi tuta, sai Marhab bayahude ya bayyana ga Ali ya na cewa:

Khaibar ta sani cewa ni ne marhab

Mai rike makami gwarzo kwararre

Idan ya ki ya zo sai ya kama da wuta



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next