Umar da Ra'ayin Shari'a 2



Na ce: Wanda duk ya bi ruwayoyin tarhi kan leken asirinsa zai ga wannan ya na daga cikin siyasarsa da ayyukansa da ya yi wurin cimma wannan siyasar a fili.

Kamar dai cewa dokokin shari'a ba sa tabbata ta hanyar kuskuren jagora wurin gano su, don haka ne ma ba yi wa wani daga cikin wadannan mutanen haddi ba, bai ma cutar da su ba, kuma wannan ya na nuna cewa ba mamamki wannan leken asirin bai da wani amfani sai kara wa masu laifin karfin gwiwar yin laifi bayan sun ga wannan sakacin da rashin ko in kula daga jagoransu?!!

 

 Daga ciki, shar'anta haddin sadakin mata

Ya wajaba sadaki ya kasance daga aibn da musulmi ya ke mallaka, a hannu ne ko na bashi, ko wani amfani, kuma yawansa ya na hannun ma'aurata a cikin abin da su ka yi yarjejeniya da shi a kansa kadan ne ko mai yawa, matukar dai bai fita daga abin da aka sani na dukiya ba, kamar karancin ya yi yawa kamar a ce kwayar shinkafa, sai dai ta fuskacin yawa an so kada ya kai sama da sadakin sunna wato dirhami dari biyar.

Umar ya kasance ya dauki niyyar hana tsadar sadakin mata don ya saukaka lamarin yin aure wanda shi ne hanyar saumn yada zuriya, kuma da shi ne za a samu kare kai daga haram, kuma wanda ya yi aure ya kiyaye sulusin addininsa, sai ya tashi wata rana ya na mai yin huduba don wannan, daga cikin abin da ya ce a hudubarsa: Kada wani labara ya zo mini cewa wata mata sadakinta ya wuce sadakin manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) sai ta mayar da wannan na hana mata shi. Sai wata mata ta tashi zuwa gare shi ta ce: Wallahi Allah bai sanya maka wannan ikon ba, domin shi ya na cewa: "Kuma idan ku na son canja wata mata a matsayin wata mata kuma ku ka ba wa dayarsu dukiya to kada ku karbi wani abu daga ciki, shin za ku karbe shi bisa laifi da zunubi mai girma. Yaya kuwa za ku karbe shi alhali sashenku sun kusanci sashe, kuma sun karbi alkawari mai grima daga gare ku", Nisa: 20 - 21. Sai ya fasa yin wannan hukuncin nasa ya na mai cewa: Shin ba kwa mamakin imamin da ya yi kuskure da matar da ta yi daidai?! Ta yi fafatawa da imaminku sai ta kayar da shi[23].

A wata ruwayar[24] ya ce: Ko wa ya fi Umar ilimi, ku na ji na ina fadin irin wannan maganar amma ba kwa musa min har sai wata mata da ba ta fi matanku ilimi ba ta amsa nini?!

A wata ruwayar[25] sai wata mata ta tashi ta ce: Ya kai dan khaddabi Allah ya na ba mu kai kuma ka na hana mu, sai ta karanta wannan ayar, sai Umar ya ce: Kowa dai ya fi Umar ilimi, sai ya janye hukuncinsa.

Na ce: Sun kafa dalili da wannan lamarin da makamancinsa a kan adalcin Umar da furucinsa, kuma da yawa daga wandannan ruwayoyin suan da yawa tsakanin Umar da wasu mutane masu ilimi ko ammawa na maza da mata da su ka kawo masa wannan a matsayin adalci da furuci da ya yi, kuma ya kasance idan magana ko wani aiki su ka kayatar da shi sai mamaki ya kwashe shi, sau da yawa jin dadin kambamawa ya bayyana gare shi.

Kamar yadda ya faru gare shi tare da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) yayin da aka tambaye shi game da wasu abubuwa da ya ke ki, daga abin da buhari ya kawo daga abu musa al'asha'ari yayin da ya ce: An tambayi annabi game dawasu abubuwa da ya ki, cikin abin da buhari ya ruwaytio daga abu musa al'ashar'ari ya ce: An tambayi annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) wasu abubuwa da ya ki saboda abubuwa ne da masu hanakli ba sa la'akari da su, kuma ba a aiko annabawa don bayanin su ba, yayin da ya yawaita sai ya yi fushi saboda shisshginsu a cikin tambaya, da maganarsu kan abin da ba a bukatar sa gare su, sannan sai ya ce da mutane, ku tambaye ni, kamar da cewa mazon rahama (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya gan su sun ji kunya yayin da su ka fusata shi, sai ya yi sakar musu fuska da cewa: Ku tambaye ni, ya na mai tausaya musu da rahama da jin kai. Sai wani mutum ana cewa da shi abdullahi dan huzafata ya mike tsaye ya ce: Waye babana ya ma'aikin Allah?. Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce masa: Babanka shi ne huzafata. Sai wani ya ta ce ana ce masa sa'adu dan Salim ya ce: Waye baban ya ma'aikin Allah? Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Babanka shi ne salim maulan abu shaiba. Asalin wannan tambayar kuwa ita ce mutane su na sukan nasabarsu, yayin da Umar ya ga abin da ya samu manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) na fushi sai ya ce: Ya manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) mu mu na tuba zuwa ga Allah madaukaki daga abin da zai kai ga fushinka.

Kuma sai ya yi farin cikin cewa manzon Allah ya danganta abdullahi da babansa huzafata, da kuma danganta Sa'ad da babansa salim domin gaskatawa da uwayensu mata game da nasabar su.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next