Umar da Ra'ayin Shari'a 2



Ina ma dai ni ina kiwon dabbobi ne don talauci

Na kasance ribatacce gun kabilar rabi'a ko mudhar

Na ce: Ina mai dai halifa bai takura wannan sarki balarabe ba da mutanensa ya bayar da duk wani kokari wurin yardar da wannan mutum fizari don ya yarda, ta yadda zai iya gane wannan sarki ne ko kuma ba ma ta wannan hanyar ba, sai dai yaya Umar zai yi haka.

Umar da wannan aikin da ya yi, ya so ne ya yi wa jabala wulakanci da kaskanci tun a kan farkon kuskure da ya yi karami, sai ya wulakanta shi kai ka ce kamar yadda ake sanya igiya a huda hancin girma na rakuma, kuma wannan ne abin da Umar ya ke yi wa duk wani mutum da ya san ya na da kima kamar yadda wanda duk ya san tarihinsa zai iya sheda da hakan a halinsa.

Kuma ya rigaya gun ka ka ga yadda ya yi na tasnanta wa Khalid da wanda ya ke daga dangogin babarsa.

Kuma duba bambancin abin a ya yi a nan da na ranar da ya yi da sahibinsa Mugira dan Shu’uba yayin ad ya kare masa haddin zina na muhsini kamar yadda ka ji dazun nan, da kuma abin da y ayi na Khalid yayin da ya dage sai ya jefe shi, kuma ba don Abubakar ba da ya jefi shi, kamar yadda za ka ji kuma, wannan kuwa saboda shi khalida ya na jin wani karfi da daukaka da dogaro da kansa don haak ne ya sanya Umar ya ke tsananin tsanantawa gare shi, kamar yadda daukakar jabala da jin girman da ya ke tare da shi ne ya sanya masa wannan daga Umar, sabanin Mugira wanda shi ko da kuwa ya kasance ya na da makirci da dubara, sai day ya fi inuwar Umar yin biyayya ga Umar, kuma ya fi kwantawa da kaskan da kai gaban Umar fiye da takalmin Umar kansa, don haka ne ya bar shi duk da kuwa fajircinsa.

Umar ya na da siyasar tsorata da jama'a da firgita su komai matsayinsu a al'uma kamar jabala da Khalid, kuma wani lokacin ma ya na tsorata mutane ne da auka wa wani daga na kusa da shi kamar yadda ya yi da dansa abu shahmata, da kuma ummu farwa 'yar 'uwar Abubakar, da wanda ba shi dawani amfnai da ake la'akari da shi a sisaya ko a taronta ma, kamar yadda ya yi da ja'ada assalami, da dhabi' attamimi, da nasar dan hajjaj, da dan amminsa abi zu'aib, da abuhuraira miskini da sauransu.

Kuma ya yi riko da tsananta wa kansa a ciknsa da shansa da mazauninsa da hawansa, ya riki yin hakuri daga abubuwan sha'awa, da kamewa daga abubuwan jin dadi, da isa da guzuri da kuma bayar da kyauta mai yawa ga al'umma daga ganima, kuma ba ya tara wa kansa ko iyalinsa wani abu daga ciki, da kuma bayarwarsa daga baitul mali, da riko mai tsanani wurin yi wa ma'aikatansa hisabi, da raba dukiyarsu, da sauran ayyuka masu yawa da misali irin waddnanna wanda su ka sanya al'umam ta biyu da sandarsa. Kuma harsuna su ka yi shiru, bakuna su na rufe, babu wani daga ma'aikatansa da ya tsira daga tsananinsa sai mu'awiya dan abusufyan kawai duk da kuma su na da tsananin bambanci kan halayensu na ci da sha. Bai taba yi masa hisabi ba kan wani abu na ayyuknasa, bai taba ma zarginsa ba kan wani lamari, sai ya ma ya bar shi ya na holewa da kece reni kan jin dadin batansa, yayin da ya ke cewa da shi: Ban umarce ka ba, ban kuma hana ka ba. Kuma duk wanda ya san Umar ya san cewa saboda wani lamari na musamman ne ya kebanci mu'awiya da wannan lamarin na kyaliya.

  

Daga ciki, komawarsa zuwa ga gaskiya bayan kuskurensa, wannan ya na da yawa

Daga cikin akwai abin da ya zo daga Muhammad dna mukhlad al'attar a littafinsa na Fawa'id cewa Umar ya yi umarni da a jefe wata mata mai ciki da ta yi zina, sai ma'azu dan jabal ya fada ya na mai musun hakan cewa: Idan ka na da iko kanta, amma ai ba ka da iko kan abin da ya ke cikinta. Sai Umar ya bata wannan hukuncin, ya ce: Mata sun kasa halittar ka ya kai ma'azu, ba don ma'azu ba da Umar ya halaka.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next