Umar da Ra'ayin Shari'a 2



Wasu Abubuwa Da Umar Ya Saba Wa Nassin Shari’a

Daga ciki: Abin da ya kasance ranar Hunai na hanin kashe ribatattun yaki

Yanin da Allah ya taimakin bawansa manzonsa (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) a ranar yakin Hawazin ranar Husani, Allah ya yi masa bude mabayyani, sai ya yi shela: Cewa kada a kashe wani daga cikin wadanda aka kama daga mtujaen, sai Umar dan khadabi ya wuce wani mutum daga ribatattun yaki ana ce masa dan Akwa'u ya na daure, kuma shi ne wanda kabilar Huzai su ka aika ranar budim yakin Makka a matsayin dan leken asirinsu don ya yi leken asiri kan manzon Allah ya samo labarinsa, da labarin sahabbansa, sai ya ba su labarin da komai da ya shafin labarin manzon Allah na aiki da na magana, yayin da Umar ya gan shi sai ya ce: - kamar yadda sheikh mufi ya kawo a yakin husani a littafinsa na "Irshad" - Wannan makiyin Allah ne, ya kasacne da ya yi leken asiri a kan mu, ga shi an kama shi an ribace ku kashe shi, sai wani daga cikin mutanen madina ya sare wuraynsa, yayain da wannan labarin ya zo wa manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) game da kashe shi sai ya su ke su kan abin da su ka yi, ya ce: Shin ban umarce ku da kada ku kashe wani ribatacce ba.

Sannan kuma su ka kashe wasu mutanen daga wadanda aka kama daga cikinsu akawai Jamil dna mu'ammar dan zuhari, ya ce: Ya sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya aika wa mutanen madina jin hasushin sa kan abin da su ka yi ya na ce msuu: Me ya sanay ku kashe shi alhalin dan sakona ya zo muku ya na sanar da ku kada ku kashe ribatacce? Sai su ka bayar da uzuri, su ka ce mu mun kashe shi ne saboda maganar Umar, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya kawar da kai ya kaurace, har sai da Umair dan wahab ya ba shi hakuri kan hakan.

Na ce: Daga cikin wadanda aka kashe a wranar yakin Hawazin akwai wata mata daga cikin hawazinawa da Khali dan Walid ya kasahe ta, sai wannan ya bata ran manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) yayin da y wuce ta mutane sun taru kanta, sai ya ce da wani daga sahabbasa: Samu Khalid ka ce masa: Manon Allah ya hana ka kashe wani yaro ko mace ko wani mai aiki. Kamar yadda ya zo a ruwayar Ibn Ishak yankakke.

Kuma Ahmad dan Hambal[1] ya ce: Abu Amir abdulmalik dan Amru ya ba mu labari cewa, Mugira dan abdurrahaman ya ba mu labari daga abuzzinad ya ce: Almurka dan saifi ya gaya masa daga kakansa a wani yaki da ya yi wanda a gaba akwai Khali dan Walid, sai Ribah da wasu sahabban manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) su ka wuce wata mata an kashe ta daga cikin abin da na gaban yaki su ka yi, sai su ka tsaya su na kallon ta, su na mamakin halittarta har sai da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya riske su a kan abin hawansa, sai su ka matsa su ka ba shi wuri, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya tsaya ya ce: Wannan ba ta kasance mai yaki ba, bai kamata ba a kashe wannan. Sannan ya ce: Ka riski Khalid ka gaya masa cewa: Kada ya kashe wata zuriya ko wani mai aiki, haka nan ma abu dawud da nisa'I da Ibn majah sun ruwaito shi daga hadisin malmur'ka dan saifi.

 

Daga ciki: Akwai gudu ranar yaki

Ya isa cewa lamarin haramcin gudu daga wurin yaki a fili ya ke, kuma an yi kira ga muminai baki daya da kada su gudu daga wurin yaki: "Ya ku wadanda ku ka yi imani idan ku ka hadu da wadanda su ka kafirce da yaki to kada ku juya musu baya. Wanda kuwa ya juya musu baya a wannan rana sai dai wanda ya karkata don wani yaki ko mai karkata zuwa ga wata jama'a to hakika ya samu fushin Allah, kuma makomarsa jahannama, tir da makoma", Amfal: 15 - 16.

A nan akwa nassi karara a wannan ayar muhkama daga kur'ani mai girma da ta ke sukan duk wani daga sahabbai da ya zabi ra'ayin a aiki da nassin shari'a, sannan wannan lambarin ba wai ya faru sau day aba ne, ya faru a wurre masu yaw ane.

Daga ciki akwai ranar Uhud yayin da Ibn kamia ya kai hari kan mus'ab dan umair ya kashe shi, ya na mai tsammanain manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ne, sai ya ce: Na kashe Muhammad, sai ya koma wurin kuraishawa ya na yi musu albirhin cewa ya kashe muahmam, sai mushrikai su ka rika yi wa junan su albishir, suan cewa: An kashe muhamma, an kashe muhamma, Ibn kamia ya kashe munammad, sai zukatan musulmi su ka rusu, sai su ka fara gudu suan masu dimuwa ba ma mai kallon wani, kamar yadda Allah madaukaki ya kawo a littafisna yayin da ya ke cew: "Yayin da ku ke hawa ba kwa juya wa ga wani, kuma manzo ya na kiran ku a na karshenku, sai bakin ciki da bakin ciki su ka hadu gare ku…", Aali Imaran: 153.

Manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya kasance ya na kiran su ama su na ta hawa dutwatu su na gudu ya na mai krian su "Ku zo nan bayin Allah, ku zo gare ni bayn alla, ni ne manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka), wanda duk ya koma ya na da aljanna, ya na kiran su da wannan kira har na karshensu, ai tun daga na farko masu gudu har na karshen masu gudu, ya na kiran su, amma ba ma mai juya wa ya ga wani ko ya ga waye mai kiran.

Ibn Jari da Inb Asir sun kawo a tarihin su cewa: Sai jama'ar musulmi su ka rusu daga cikin su akwai Usman dan affaran da waninsa har zuwa A'awas, su ka zauna can har kwanaki uku, sannan sai su ka dawo madina, yayin da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya gan su bayan su ndawo, sai ya ce musu: Kun zo da abin kunya.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next