Umar da Ra'ayin Shari'a 2



Mun shagaltu daga barin ku lokacin yaki

Babu wasu budurwowi da su ka samu masu runguma

A garin Kifa Sila'in a can wuraren Kogi

'yan mata ne daga banu sa'adu bn bakru

Da (kabilun) aslama, ko juhainata ko gifari

Ja'ada daga (kabilar) Sulaimi ne ya ke rungumar su

Ya na maimaitawa ya na neman kawar da budurci

Sai Umar ya ce: Ku kira mini ja'ada dan sulaim, sai aka kra shi, sai ya yi uamrni a yi masa bulala dari a daure, sannan ya hana shi shiga wurin matar da mijinta ba ya nan.

Na ce: Ba wani dalili kan tsayar da haddi don kawai wadannan baitocin domin ba a san mai fadin su ba, ko wanda ya aiko su, hada da cewa ba komai cikinsu sai batun okiran halifa ga ja'ada da da'awar cewa ya ketare iyakar 'yan matan kabilun banu sa'ad dan bakru, da aslama, da juhainta, da gifar, ya na wasa da su, sai ya daure su kamar yadda ake daure 'ya'yan rakuma, ya na neman saryar da mutuncinsu, wato sanya su abin kunya, wannan kuma shi ne abin da ya ke cikin wadannan baitoci da aka danganta shi ga ja'ada. Kuma da wannan ya tabbata a shar'ance to babu wani abu da zai sanya tsayar da haddi kan sa, sai dai abin da zai kai ga wajabta yi masa da ladabi da ladabi. Kuma ta yiwu wannan abin da halifa ya yi irin wannan ne. sai dai abin da ya yi a nan, da kuma abin da ya yi daga Mugira dan Shu’uba ya bambanta matuka kamar yadda za ka ji nan gaba kadan,I in Allah ya so.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next