Umar da Ra'ayin Shari'a 2



 

Daga cikin irin wannan misalin

Akwai abin da hakim ya ruwaito a babin wanda aka dauke alkalami daga kansa, daga littafin haddodi shafi na 389 a juzu'I na hudu a littafinsa na mustadrak da sanadinsa zuwa ga Ibn Abbas cewa: An zo da wata mata mahaukaciya mai ciki sai Umar ya so ya jefe ta, sai Ali ya ce masa: Shin ba ka san an dauke alkalmi ga mutane uku ba? Daga kan mahaukaci har sai ya yi hankali, da yaro har sai ya balaga, da mai bacci har sai ya farka, sai Umar ya kyale ta.

Na ce: Wannan ba waccan matar ba ce, domin waccen da mu'azu ya fadakar da shi kan ta ba mahaukaciya ba ne, sai Allah ya sanya ta samu hanyar mafita, sai dai bayan ta haihu, kuma an samu amintuwa kan mai renonsa sannan ne za a iya jefe ta. Amma wannan ita mahaukaciya ce ba shi da wani iko kan kashe ta gaba daya kamar yadda mu ke iya gani.

Haka nan alkalin alkalai abduljabbar ya na da magana a littainsa "almugni" game da umarnin Umar na a jefe mai ciki wanda ya samu bahasi tsakaninsa da sharif murtadha a littafinsa na "asshafi" kuma Ibn abil hadid duk ya kawo maganarsu duka a wurare daban - daban na littafinsa a shafi an 150 zuwa 152 a mujalladi na uku na sharhin nahajul balaga, bugun misira.

  

Misalin irin wannan haka nan

Abin da Ahmad ya fitar daga hadisin Ali shafi na 154 da abin da ya biyo baya na juzu'I na farko daga littafinsa na masnad daga abu zubyan aljanbi[29] ya ce: An zo wa Umar dan khaddabi da wata mata da ta yi zina sai ya yi umarni da a jefe ta, sai Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya kwace ta daga hannunsu ya mayar da su da ita, sai su ka koma wurin Umar su ka ce: Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ne ya dawo da mu. Sai Umar ya ce: Bai yi haka ba sai don akwai wani abu da ya sani, sai ya aika wa Ali, sai ya zo ya na kamar mai bacin rai. Sai Umar ya ce masa: Me ya sa ka dawo da wadannan? Sai ya ce; shin ba ka ji fadin manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ba cewa: An dauke alkalami ga mutane uku: Daga mai bacci har sai ya farka, da karami har sai ya girma, da mai tabin hankali har sai ya yi hankali. Sai ya ce: Haka ne. sai Ali ya ce: Wannan mai dabin hankalin ce ta babun fulan, ta yiwu mutumin ya zo mata ne ta na cikin wannan tabin hankalin. Sai Umar ya ce: Ban sani ba. Sai shi ma ya ce: Ban sani ba. Sai bai jefe ta ba.

 

 

Daga cikin irin wannan

Ibn kayyim ya fada a littafinsa "daurukul hakima, fis siyasatis shari'yya" cewa: An zo da wata mata wurin Umar sai ta yi furuci da yin zina, sai ya yi umarni a jefe ta, sai Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya fadakar da shi cewa ta yiwu ta na da wani uzuri da zai kare mata haddi. Sannan sai ya ce mata: Me ya sanya ki yin zina? Sai ya ta ce: Ni ina da wani abokin tafiya ne, ya na da wura da nono a kayan rakuminsa, ni kuma ba ni da ruwa da nono a kayan rakumina, sai na yi kishi mai tsanani, sai na nemi ya ba ni ruwa, sai ay ki shayar da ni har sai na ba shi kaina, sai ya ki har sau uku, da na ga na samu kishi mai tsanani na ga raina za ta iya fita, sai na ba shi abin da ya ke so gaga gare ni, sannan sai ya shayar da ni. Sai Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya ce: Allahu Akbar "Duk wanda ya shiga bukatar lalura ba mai shisshigi ba, ba kuma mai maimaitawa ba, to wannan Allah mai yawan gafara mai yawan jin kai ne" nahli: 115.

Baihaki ya ruwaito a sunan dinsa[30] daga abdurraham assalami ya ce: An zo wa Umar da wata mata da kishirwa ta yi mata tsanani, sai ta wuce wani mia kiwo sai ya ki shayar da ta ita har sai ta ba da kanta gare shi, sai ta yi. Sai Umar ya yi shawarar kan jefe ta, sai Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya ce: Wannan ta na daga cikin wadanda aka bukatar ina ganin ka kyale ta, sai Umar ya yi hakan.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next