Umar da Ra'ayin Shari'a 2



Daga cikin irin wannan

Abin da Ibn kayyim ya kawo a littafinsa na durukul hakima, shafi 55 fadinsa yayin da ya ce: An kawo wa Umar wata mata da ta yi zina, sai ta yi furuci a gabansa, sannan ta maimaita furuci da shi, ta karfafa abin da ta yi na fajirci, kuma Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya na wurin, sai ya ce: Wannan ita ta na saukaka shi da saukakawar wanda bai san cewa haram ba ne yin hakan, sai ya kawar mata da haddi.

Ibn kayyim ya na cewa: Wannan ya na daga zurfin kafin hankali da kyautata zato.

 

Daga cikin irin wannan lamarin

Abin da allama Ahmad amin bik ya kawo a littafinsa na fajarul islam shafi 285 ya na mai nakaltowa daga littfin a'alamul muwakki'in ya ce: An kawo lamarin wani mutum da matar babansa ita da masoyinta su ka kashe shi. Sai Umar ya yi kaikawon kashe mutum biyu saboda daya. Sai Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya ce: Shin ka na ganin da mutane masu yawa ne su ka yi tarayya a satar da ta ke sanya yanke hannu shin za ka yanke su? Sai ya ce: Haka ne. sai Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya ce: Wannan ma haka ne. Sai Umar ya yi aiki da ra'ayin Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi). ya rubuta wa gwamnansa cewa ya kashe su ko da kuwa dukkan mutanen san'a'a ne su ka yi tarayya a kan kashe shi da na kashe su baki daya.

 

Daga ciki

Abin da ya zo daga ma'abota littattafan sira da tarihi, da lafazin allama Ibn abil hadid bamu'utazile[31] yayin da ya ce: Umar ya kira wata mata don ya tambaye ta wani lamari, kuma ta kasance ta na da ciki, sai ta jefar da jaririn cikinta saboda tsoron Umar, sai ya nemi fatawar manya sahabbai a kan haka. Sai su ka ce: Ai babu komai a kanka, ai kai mai ladabtarwa ne. sai Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya ce masa: Idan sun kula da kai ne a wannan hukuncin da su ka yanke to sun yaudare ka ne, idan kuma sun yi ijtihadi ne da ra'ayinsu to sun yi kuskure, aka da 'yanta baiwa a kanka. Sai Umar da sauran sahabbai su ka koma kan maganarsa.

  

Daga ciki, akwai dimuwarsa kan lamarin wani mutum daga muhajirai na farko daga mutanen badar

Wannan kuwa shi ne kuddama dan maz'un: An zo da shi ya sha giya, sai Umar ya yi uamrni da a yi masa bulala, sai ya ce: Me ya sa za ka yi mini bulala? Tsakanina da kai akwai littafin Allah . sai Umar ya ce: A wane littafin Allah ne ka samu cewa kada in yi maka haddi? Sai ya ce: Allah ya na cewa a littafinsa: "babu lefi ga wadanan da su ka yi imani kuma su ka yi aiki na gari cikin abin da su ka ci…" Ma'ida: 93. Kuma ni ina daga wadadna su ka yi imani su ka yi aiki na gari sannan su ka yi takawa su ka yi imani su ka yi takawa su ka kyautata. Na halarci yakin badar, da hudaibiyya, da khandak, da sauran yakoki tare da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka). sai Umar ya kasa yi masa raddi ya ce: Shin ba za ku yi masa raddi ba. Sai Ibn Abbas ya ce: Wannan ayar an saukar da ita ne don nuna uzurin wadanda su ka gabata, kuma hujja ce kan wadanda su ke na baya, domin Allah (Mai Girma da Buwaya da Daukaka) ya na cewa: Ya ku wadanda ku ka yi imani gida da caca da gumaka da sakandamai dauda ce daga aikin shedan sai ku nuisance su… sannan su ka yi takawa su ka kyautata" ma'ida: 90. Hakika Allah madaukaki ya hana shan giya, to ina takawa ga mai shan ta bayan an hana ta? Sai Umar ya ce: Ka yi gaskiya, me ku ke gani? Sai Ali ya ba shi fatawa da yin bulala tamanin, kuma wannan ya gudana har zuwa yau[32].

 

Daga ciki

Akwai abin da Ibn kayyim ya nakalto daga littafinsa aldurukul hakima a shafin na 47, game da lamarin wata mata da ta makalkale wani saurayi daga ansarn (mutanen madina) da ta kasance ta na son sa, amma yayin da bai taimaka mata lalata ba, sai ta yi masa makirci ta dauki kwai sai ta jefa yalonsa a farjinta, sannan sai ya zuba kwai a tufafinta, da gefen cinyarta, sannan sai ta zo wurin Umar ta na iho wai an keta mata hurumi ta na mai kai kukansa ta ce: Wannan mutumin ne ya yi mini ta karfi ya hau kaina, ya kunya ta ni a iyalina, wannan shi ne kufan abin da ya yi mini. Sai Umar ya tambayi mata mene ne wannan, sai su ka ce masa lallai a tufafinta akwai kufan mani. Sai ya yi nufin yi wa wannan saurayin ukuba, saurayi kuwa ya na neman taimako ya na cewa: Ya sarkin muminai ka bincika cikin lamarina, wallahi ni ban yi wata alfahasha ba, ban kuma taba nufin yin ta ba, kuma ita ce ta nemi ne na ki yarda. Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya kasance ya na wurin kuwa, sai Umar ya ce: Ya baban Hasan me ka ke gani kan lamarinsu? Sai Ali ya duba tufafin, sannan sai ya sa aka kawo ruwan zafi mai tsananin tafasa, sai ya zuba wa tufafin, sai wannan farin kwan ya sandare, sannan sai ya dauke shi ya shaka shi sannan ya dandana shi, sai ga shi da dandanon kwai, sai ya yi wa matar tsawa sai ta yi furuci da abin da ta yi.

 

Daga ciki

Akwai abin da Ibn kayyim ya nakalto daga littafinsa aldurukul hakima a shafin na 30 da abin da ya biyo bayansa cewa: Wasu mutane biyu daga kurasih shun ba wa wata mata dinare dari ajiya, su ka ce mata kada ki bayar da shi ga daya daga cikinmu shi kadai sai tare da dayan, sai su ka zauan shekara guda, sai dayansu ya zo ya ce: Abokina ya mutu, ki ba ni wannan dinarorin. Sai ta ki ta ce: Kun ce kada in bayar da shi ga dayanku sai da dayan tare da shi, kuma ni ba zan bayar da shi gare ka ba. Sai ay yi ta yi mata magina da bi ta hannun danginta da makotanta har sai da ta ba shi. Bayan shekara cikakkiya sai ga dayan kuma ya zo ya ce: Ba ni wadannan dinarorin. Sai ta ce: Abokinka ya zo ya ce ka mutu, ya nemi in ba shi, ni kuwa sai na ba shi. Sai su ka kai hukunci gaban Umar: Sai Umar ya yi nufin zartar da hukunci kanta da biya. Sai ta ce: Ka kai mu wurin Ali dan abu Dalib mana. Sai ya kai su. Sai Ali ya san cewa sun yi mata makirci ne, don haka sai ya ce da mutumin: Ba kun ce kada ta bayar ga dayanku ba sai da dayan ya na nan? Sai ya ce: Haka ne. sai ya ce: Je ka zo da dayan sai ta ba ku, in ba haka ba, to ba ka da wani hakki a kanta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15