Umar da Ra'ayin Shari'a 1



Hada da cewa manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) da kansa ya I ku ka a wurare da yawa, kuma ya tabbatar da ku ka a kan hakan, kuma ya kyautata shi, kai ya yi kira ma da yin sa.

Ya yi ku ka a kan amminsa hamza zakin Allah kuma zakin manzonsa, Ibn abdulbarri[26] da waninsa ya na cewa: Yayin da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ga amminsa hamza an kashe shi sai ya yi ku ka, kuma yayin da ya ga abin da aka yi masa na kaca - kaca sai ya yi shessheka.

Kuma wakidi[27] ya kawo: Cewa annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya kasance a wannan ranar idan safiyya ta yi ku ka sai ya yi ku ka, kuma idan ta kwalla ku ka sai ya kwalla ku ka, ya ce: Sai Fadima ta rika ku ka, yayin da ta yi ku ka sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi ku ka[28].

Daga anas ya ce: Manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: - yayin da rundunar musulmi ta kasance a Mu’utat - Zaidu ya riki tuta, sai aka kashe shi, sannan sai Ja'afar ya rike ta sai aka kashe shi, sannan sai Abdullah dan rawahta ya karb ta sai aka kashe shi. A lokacin idanuwan manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) su na zubar da hawaye…hadisi[29].

Ibn Abdulbarri ya kawo a cikin tarihin zaidu a littafinsa na “al’isti’ab” cewa: Annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi ku ka kan Ja'afar da zaid, sai ya ce: ‘yan’uwana ne, masu debe mini kewa, masu zantar da ni.

Daga anas daga hadisin da buhari ya kawo shi a littafinsa[30] ya ce: Sannan sai mu ka shiga wurinsa (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ga Ibrahim dansa ya na lumfashi daidai, sai idanuwan manzon Allah su ka rika zuba, sai abdurrahman dan Auf ya ce da shi: Har da kai ya ma’aikin Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka)! sai ya ce: Ya kai dan Aufu wannan shi ne tausayi, sannan sai ya sake yin wani hawayen, sannan sai ya ce: Hakika idanuwa su na zuba, zukata suan bakin ciki, kuma ba ma cewa komai sai abin da zai yardar da ubangijinmu, kuma mu masu bakin ciki ne da rabuwa da kai ya Ibrahim.

Daga usama dan zaid ya ce: Wata ‘yar annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ta aiko masa cewa wani dana ya rasu ka zo mana, sai ya tashi da shi da wadanda su ke tare da shi su Sa’adu dan Ubbada, da ma’azu dan jabal, da ubayyu dan ka’abu, da zaidu dan sabit. Sai a daga yaron zuwa ga annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ransa ta na neman fita, sai idanwuwan manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) su ka zuba, sai sa’adu ya ce: Ya ma’aikin Allah mene ne wannan? Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Wannan ita ce rahama (tausayi) da Allah ya ke sanya shi a cikin zukatan bayinsa, ka sani Allah kawai ya na tausayin bayinsa masu tausayi ne….hadisi[31].

Daga Abdullah dan uamr ya ce: Sa’adu dan ubbada ya yai faman wani ciwo nasa, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya zo masa ya na mai ziyartarsa, tare da shi akwai abdurrahma dan aufu, da sa’adu dan abi wakkas, da abdullahi dan mas’ud, sai ya same shi a cikin cincirindon iyalinsa, sai ya ce: Ya cika? Sai su ka ce a’a ya ma’aikin Allah. Sai annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi ku ka. Yayin da mutane su ka ga kukan annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) sai su ka yi ku ka. Sai ya ce: Ku saurara! Allah ba ya azabtarwa da hawayen idanu, ko da bakin cikin zukata, sai dai ya na azabtarwa da wannan - ya nuna harshensa - ko ya tausaya da wannan… hadisi[32].

A cikin tarihin Ja'afar da ya zo a littafin isti’ab ya ce: Yayin da labarin mutuwa Ja'afar ya zo wa annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) sai ya zo wa matarsa asma’u ‘yar umais sai ya yi mata ta’aziyya. Ya ce: Sai Fadima (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ta shigo ta na ku ka, ta na cewa: Wayyo ammina! Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Lallai kam ga misalin Ja'afar, masu ku ka su yi ku ka[33].

Haka nan ma malaman tarihi da kissoshi kamar su Ibn jarir da Ibn asir da Ibn kasir, da mai littafin akdul farid da suaransu sun kawo abin da Ahmad dan Hambal ya fitar na hadisin dan uamr a shafi 40 daga juzu’I na biyu na masnadinsa, cewa: Yayin da manzon Allah sa ya dawo daga uhud sai matan ansar su ka rika ku ka kan wadanda aka kashe na mazajensu. Ya ce: Sai manzon alalh (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Sai dai hamza ba shi da masu yi masa ku ka. Ya ce: Sannan sai ya yi bacci, sai ya farka su na yin ku ka. Ya ce: A yau idan su ka yi ku ka to suan yi wa hamza ku ka[34].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next