Umar da Ra'ayin Shari'a 1



Kuma tun da Allah madaukaki ya na son ya gamsar da su da uzurin annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) a kan dagewarsa kan yin yaki, da rashin kula da ayari da mutanensa, sai Allah mai girma da buwaya ya ce: "Ba zai yiwu ga wani annabi - daga annabawa da mursalai daga su ka zo kafin annabinku Muhammad (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) - ya kasance ya na da ribatattun yaki har sai ya zubar da jini a bayan kasa - kuma anabinku ma babu yadda zai kasance ya kama ribatattun yaki har sai ya zubar dajini a bayan kasa kamar sunnar sauran annabawa da su ka kama ribatattun yaki bayan gabzawa, don haka bai damu ba ko da kuwa wancan ayari na su abu sufyan da mutanensu sun gudu sun kubuce masa zuwa Makka, sai dai ku - ku na son rayuwar duniya - yayin da ku ke son ayari da kame mutanensa - ku na fifita ta kan ta lahira, alhalin Allah ya na son lahira ne - da kawar da runduna mai kaya daga makiyansa - kuma Allah mabuwayi ne mai hikima - izza da hikima kuwa a wannan lokacin ta na cikin kawar da izzar makiya da girman kansu, da kawar da wutar yakinsu, sannan sai Allah ya gargadi wadannan sahabban da su ke son a bi ayari a kama mutanensa da cewa; - ba don wajabci ya rigaya daga Allah ba - na cewa tun azal ya san zai hana ku samun ayari da ribace mutanensa, da kun ribace su kun kama mutanen ayari, kuma da kun yi hakan da sakamakon abin da ku ka yi din - da Allah ya kama ku sakamakon abin da ku ka kama - kafin ku zubar da jini a bayan kasa - da azaba mai girma" Anfal: 67 - 68.

Wannan ce ma'anar wannan aya, kuma bai inganta ba a dora ta kan waninta, kuma ni ban sani wani da ya rigaye ni kan wannan ba, yayin da na kawo wannan ayar na yi fassararta da sharhinta a cikin littafin "Fusulul Muhimma"[52].

 



[1] Masnad: J 4, s 370.

[2] Masnad: J 5, s 406.

[3] Mustadrak: J 4, kitabul fara’idh, s 339.

[4] Muntaki; kanzul ummal: J 6, s 15.

[5] Kanzul ummal: J 6, s 15.

[6] Baihaki: Shu’Abul iman; j 6, s 15.

[7] Kalmar hayya, daga litttafin hayawan na Dumairi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next