Umar da Ra'ayin Shari'a 1



 

Fasali

Musulmi sun yi sabani kan farawar iddar da ta ke wata hudu da kwana goma ce, sai dai wanda mafi yawa su ka ta fi a kansa shi ne ta na farawa daga mutuwar mijinta ne, shin ta san da mutuwarsa ko ba ta sani ba saboda ya boyu daga gare ta saboda wani dalilin.

Amma mu abin da mu ke a kansa na ra’ayi da aiki a wannan iddar shi ne tun farkon da ta san wafatin mijinta, don haka da ba ta sani ba to ba za ta yi aure ba don ta sani komai kuwa dadewar mutuwar tasa har sai ta yi idda bayan ta samu labarin mutuwar tasa har zuwa wata hudu da kwana goma sannan za ta iya yin wani aure ta halatta ga mazaje aiki da wannan ayar da riko da yin takaba wajiba a kan mace saboda mutuwar mijinta.

 

 

Daga ciki, akwai aurar da wacce mijinta ya bace

Alfadhil dawalibi ya ce[14]: Haka nan Umar ya yi ijtihadi game da mtar da mijinta ya bace yayin da ya yi hukunci da cewa dole ne matar da mijinta ya bae ta yi shekara hudu bayan rasa shi sannan sai ta yi aure bayan kuma ta yi idda, ko da kuwa mutuwar mijinta ba ta tabbata ba, wannan kuwa don gudun kada mace ta zauna haka nan tsawon rayuwa.

Ya ce: Da wannan ne maliku ya yi aiki sabanin hanafi da shafi’I da su ka ce mace za ta ci gaba da zama matar mijinta da igiyar aure har sai an tabbatar da wafatinsa ko irin masu shekarunsa sun rasu, domin asalin wannan lamarin shi ne ya na nan raye har sai an samu dalili a kan yankewar rayuwarsa.

Ya ce: Sai dai uamr ya ga wannnan abin da ya yi ya fi saboda ya kawar da cutar wannan mata ta zahiri, kuma kamar yadda mu ke gani ba ta wannan dammar ya sama da zahirin nassin shari’a da sauran imamai su ka yi riko da ita.

Ya ce: Wannan kuwa ba komai ba ne sai canja hukuncin Allah da bin yanayi a cikinsa da babu makawa a kaddara shi daidia gwargwadon kariya da takura, manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya na cewa: Babu cuta, babu cutarwa. Hakan nan Allah madaukaki ya na cewa: “ba a sanya muku wani tsanani ba a cikin addini” Hajji: 78. Ya ce: Wannan bisa hakika ba wurgi ne da hukuncin shari’a ba, sai dai aiki da shari’a bisa maslaha da yanayi.

Na ce: Amma mu shi’a imamiyya mu na da riko da imaman shiriya masu tsarki, da nassosi da su ke hukunci bisa asasin ilimi kan hakan, da su ka bayyana cewa wacce mijinta ya bace idan ta jahilci labarin sa, kuma matarsa ta kasance akwia wanda ya ke daukar nauyinta, wajibi ne ta saurara har sia ya zo ko kuma an tabbatar da wafatinsa, ko wani abu makamancin hakan, idan kuwa babu wani mai ciyar da ita, to sai ta kai kara gun jagoran musulmi mia hukuma, idan ta yi, sai ya bincika game da lamarinsa shekaru hudu tun daga lokacin da ta kai kara, za a yi binciken ne ta fuskacin jihar da ya bata, in babu wata jihar sai a binciki jihohi hudu duka, sannan sai jagora ya sake ta ko kuma ya umarci mai kula da lamarinta. Abin da ya fi ya gabatar da mai kula da lamarinta, idan ya ki sankinta sai shi jagoran ya sake ta don haka ruwayoyin su ke nufi. Kuma wannan sakin ya na yiwuwa ne bayan muddar da aka fada, da komowar masu nema ko makamancin hakan, sai kuma ta yi iddar wafati wata hudu da kwana goma bayan hakan, sai bayan idda sannan ta ke halatta ga mazaje, idan mijin da ya bace ya zo bayan idda to shi ne ya fi cancanta da ita, amma idan ba haka ba to ba shi da wani iko a kanta, ya same ta da ta riga ta yi aure ko kuwa kafin auren. Wannan shi ne mazhabin imamiyya kan wannan mas’alar biyayya ga imamansu (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi).

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next