Umar da Ra'ayin Shari'a 1



 

Daga ciki, akwai rabon magada (daga abin da iyaye su ka bari da mukusanta) ta fuskacin kabilar larabawa da waninsu

Ubangiji madaukaki ya na cewa: “maza suan da nasu kaso daga abin da iyaye su ka bari da makusanta, mata suan da nasu kaso daga aibn da iyaye su ka bari da makusanta, daga abin da ya karanta daga gare shi ko ya yawaita, kaso (rabo) ne da aka sanya” Nisa’i: 7. Da fadinsa: “Allah ya na yi muku wasiyya game da ‘ya’yanku, namiji ya na da rabon mata biyu” Nisa’i: 11. Da kuma ayoyin kaso da gado duk su na zuwa ne bisa bayani babu wani kaidi a surar Nisa’I, sia a koma a duba, haka nan ma akwai wannan a ruwayoyi masu yawa da kuma ittifakin al’umma da fatawowi.

Imam Sadik (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya na cewa: Musulunci shi ne shaidawa babu abin bauta sai Allah, da gaskatawa da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka), da wannan ne jini ya samu kariya, da gudanar aure da yin gado.

Imam Bakir (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya na fada a ruwayar Humran cewa: Musulunci shi ne abin da ya bayyana na magana da aiki, kuma a kansa ne wasu jama’a daga musulumi su ke dukkansu, kuma da shi aka kare jini, da gudanar gado da yin aure, da su ka hadu a kan yin salla, da zakka da azumin watan ramadhan, da hajjin dakin Allah, da wannan sai su ka fita daga kafirci aka dangana su da imani.

Sai dai maliku ya bayar da labari a muwatta daga amintacce gunsa cewa ya ji Sa'id dan musayyib ya na cewa: Umar ya ki ba wa wani daga ajamawa (wadanda ba larabawa ba) gado, sai dai idan da ne na larabawa, sai maliku ya ce: Amma idan ta zo da cikinsa daga kasar makiya sai ta haife shi a kasar larabawa to shi danta ne da ya ke gadon ta idan ta mutu, kuma ta na gadon sa idan ya mutu gadon ta a cikin littafin Allah[10].

 

 

Daga ciki, akwai gadon dan'uwan uwa ga dan 'yar'uwarsa

Sa'id dan Mansur ya fitar da sunan dinsa cewa: Wani mutum ya gano wata ‘yar’uwarsa da aka ribace ta a lokacin jahiliyya, a tare da ita akwai wani danta da bai san waye ubansa ba, sai ya saye ta ya ‘yanta ta, sai wannan yaron ya samu dukiya mai yawa, sannan sai ya mutu, sai su ka zo da shi gun dan mas’ud su ka gaya masa wannan. Sai ay ce: Ku je wurin Umar ku tambaye shi, sannan ku dawo wurina ka ba ni labarin abin da ya ke ce maka, sai ya zo wurin Umar ya gaya masa wannan, sai ya ce: Ba na ganin ka na daga danginsa, ba ka daga masu gado, bai ba shi gado ba, sai ay dawo wurin Ibn mas’ud ya ba shi labari, sai Ibn mas’ud ya ta fi wurinsa tare da shi har sai da ya shiga wurin Umar sai ya ce masa: Yaya ka wa wannan mutumin fatawa? Sai Umar ya ce: Ba na ganin sa daga dangi ko masu gado, ban ga dalilin ba shi gado ba, yaya ka ke ganin ya kai baban Abdullah? Sai ya ce: Ina ganin sa mai kusanci (domin shi ne dan’uwan babarsa) mai kula da lamarinsa shugaban (don shi ya ‘yanta shi), ina ganin ya na da gado, sia Umar ya bata hukuncinsa na farko.

Mai littafin kanzul ummal ya kawo wannan lamarin a babin gado shafin na 8, juzu’I na shida, sai dai fatawar Ibn mas’ud ta na inganta ne idan da uwar yaron ta mutu kafin danta.

 

 

Daga ciki, akwai iddar mai ciki da mijinta ya mutu ya bar ta

Baihaki ya kawo a cikin littafin “shu’Abul iman” cewa wata mata ta nemi fatawar Umar ta ce masa: Na haife cikina bayan wafatin mijina kfin karewar idda, sai ya yi mata fatawa da wajabcin dakatawa zuwa mafi nisan iddodi biyu, sai ubayyu dan ka’abu ya yi masa musun hakan a gaban matar, kuma an ruwaito masa cewa ya ce; iddarta shi ne har sai ta haihu, ya yi mata izinin yin aure kafin ta cika wata hudu da kwana goma, Umar bai ce mata komai ba sai cewa ni ma ina jin abin da ki ka ji[11], kuma ya bar fatawarsa ta farko, sai dai bayan nan sai ya samu dacewa da yarda da ra’ayin ubayyu dan ka’abu, sia ya ce: Da ta haife cikinta mijinta ya na kan gadon mutuwa ba a binne shi ba, da ta halatta ga mazaje[12], kuma wannan ne masu mazhaba hudu su ka ta fi a kansa har zuwa yau din nan.

Sai dai mu shi’a imamiyya mun samu ayoyi biyu da su ke karo da juna game da iddar wacce mijinta ya mutu ta na mai ciki, wadannan kuwa su ne: Fadinsa madaukaki: “masu ciki muddarsu shi ne su haife cikinsu’ Talak: 4. Da fadinsa madaukaki: “wadannan da mazajensu su ke mutuwa su na barin mata, to sai su zauna iddar wata hudu da kwana goma” Bakara: 234. To mai ciki idan ta dauki ayar farko ta halatta ga mazaje ke nan ko da kuwa ba ta yi muddar da aka fada a aya ta biyu ba ke nan, ama idan ta yi amfani da aya ta biyu to ta saba wa aiki da aya ta farko, kuma ba za ta iya hada su duka biyu ba sai dai idan ta jira wacce ta fi nisan zango daga cikin iddodin da su ke wadannan ayoyin sai ta yi aiki da ita, kuma babu wakawa da yin hakan. Wannan ne kuma aka ruwaito daga imam Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) da Ibn Abbas[13], kuma shi ne imamiyya shi’a su ke a kansa na daga ruwayoyin da su ka zo daga imamansu (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next