Umar da Ra'ayin Shari'a 1



 

 

Daga ciki, abin da ya faru a farkon musulunci da ya shafi yin azumi

Wannan kuwa saboda mai azumi ya kasance idan ya yi yamaci to ci da sah da mata sun halatta gae shi a watarn ramadhan da sauran abubuwa har sai ya yi sallar isah, ko ya yi bacci, idan ya yi sallar isha' ko ya yi bacci to duk abin da ya haramta kan mai azumi ya haramta kan sa har sai ya shiga dare na gaba, sai dai uamr ya zo wa matarsa da dare, sai ya yi wanka, ya yi nadama kan abin da ya yi, sai ya zo wurin annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya na mai cew: Ya ma'aikin Allah, ina neman uzuri wurinka daga kaina mai kuskure, ya ba shi labarin abin da ya yi, yayin nan ne sai wasu mutane su ka tashi su ka ce su ma su na yin yadda Umar ya yi bayan isha', sai Allah ya saukar da kayar nan: "An halatta muku kusaci zuwa ga matanku a daren azumi, su tufafi ne gare ku, ku ma tufafi ne gare su, Allah ya san cewa lallai ku kun kasance ku na ha'intar kawukanku, sai ya tuba gare ku, ya yi muku afuwa, to yanzu ku kasance su, ku nemi abin da Allah ya wajabta muku, kuma ku ci, ku sha, har sai farin silili ya bayyana gare ku daga bakin silili na alfijir, sannan sai ku cika azumi zuwa dare" Bakara: 187[43]. Wannan aya ta nuna a fili cewa sun kasnce suan ha'intar kawukansu wato ba sau daya su ka yi ba, sai dai ta yi bayanin tuba gare su da yi musu afuwa, sai Allah ya yalwata wa al'umma da wannan abin da ya kallafa musu shi. Mu na godiya ga Allah bisa afuwarsa da gafararsa, kuma godiya gare shi bisa yalwar rahmarsa.

 

 

Daga ciki, abin da ya zo game da giya da haramcinta

Wannan kuwa saboda Allah ya saukar da ayoyi uku game da harancin giya, ta farko fadin Allah madaukaki cewa: "Su na tambayarka game da giya da caca, ka gaya musu a cikinsu akwai zunubi mai yawa, da wani dan amfani ga mutane…" Bakara 219. sai a cikin musulmi wani ya bar sha, wani kuma ya ci gaba da sha, har sai dawani mutum ay sha sai ya fara salla, sai ya yi munanan kalamai na buguwa, sai Allah ya saukar da ayar nan mai fadinsa madaukaki: "Ya ku wadanda ku ka yi imani kada ku kusanci salla alhalin ku na cikin maye har sai kun san me ku ke cewa…" Nisa'i: 43, sai kuma wasu su ka ci gaba da sha daga cikin musulmi, wasu kuwa su ka daina sha, masu tarihi suan kawowa cewa har sai da Umar dan khaddabi ya sha wata rana sai ya dauki kashin habar rakumi ya fasa kan Abdurrahman dan aufi da shi, sannan sai ya zauna ya na kukan bakin cikin kafiran da aka kashe a yakin Badar, ya na mai fadin wakar nan ta Al'Aswad dan Ya'afur yayin da ya ke cewa:

* Da wadanda su ke cikin kalib rijiyar Badar

Na daga samari da larabawa masu daraja

* Shin dan Kabsha zai yi mana alkawarin raya mu

Idan mu ka

* A yanzu zai kasa kawar da mutuwa daga gare ni

Sai kuma ya tashe ni idan na kasusuwana su ka rube



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next