Umar da Ra'ayin Shari'a 1



A tarihin hamza a cikin lttafin isti’ab ya karbo daga wakid, ya ce: Babu wata mata daga matan mutanen madina da za ta yi ku ka kan wani mamaci har zuwa yau din nan, bayan fadin manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) cewa: “Sai dai hamza ba shi da masu yi masa ku ka”, sai ta fara yi wa hamza ku ka.

Na ce: Ya ishe ka dalili cewa wannan al’ada ta ci gaba ta yin ku ka ga hamza tun daga lokacin manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) da na sahabbai da tabi’a da masu bin tabi’ai har yau, kuma ya isa dalilin son yin ku ka ga wanda ya ke kamar hamza ko da kuwa lokacin da ya rasu ya jima.

Kada ka manta fadin annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) garesu cewa sai dai hamza ba shi da masu yi masa ku ka ya na mai zarginsu kan kin yi masa ku ka, da kuma motsa su da kwadaitar da su ga yi masa ku ka, kuma ya ishe ka haka da fadinsa (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka): “Ga mutum kamar Ja'afar ne masu ku ka su ke yin ku ka” da ya ke nuna dalili kan mustahabbancin hakan.

 Amma duk da hakan sai ya kasance ra’ayin halifa Umar dan khaddabi shi ne ya hana kukan ga mamaci ko mai girmansa, har ma ya kasacne ya na duka da sanda, ya na jifa da duwatsu, ya na zuba kasa[35], ya na aikata haka tun lokacin manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) kuma ya ci gaba a kan hakan tsawon rayuwarsa.

Imam Ahmad dan Hambal ya kawo daga hadisin Ibn Abbas[36] daga cikin hadisan da ya ambaci mutuwar rukayya ‘yar annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) a ciknsa da kukan da mata su ka yi mata, sai ya ce: Sai Umar ya rika dukan su da bulala, sai annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Rabi da su su yi ku ka, kuma ya zauna a gefen kabarin ga Fadima (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ta na ku ka a gefensa, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya rika shafe idanuwan Fadima da tufafinsa don tausaya mata. Nan ne ya tuke.

Hakan na kuma Imam Ahmad dan Hambal ya kawo a masnadinsa daga abuhuraira[37] wani hadisi da ya zo a cikinsa cewa manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya wuce wata janaza a tare da ita akwai masu ku ka, sai Umar ya yi musu kyara, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce masa, Rabi da su hakika rai ta samu bala’I, idanu ya na zuba[38].

A’isha da Umar sun kasance sun yi hannun riga a wannan mas’alar, sai Umar da dansa Abdullah su ke ruwaito cewa annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) yace: Ana yi wa mamaci azaba saboda kukan da danginsa su ke yi masa, a wata ruwayar: Da wani kukan da danginsa su ke yi masa, a wata ruwayar da ku ka da yankinsu su ke yi masa, a wata ruwayar ta hudu ana azabtar da shi a kabarinsa saboda kukan da ake yi masa, a wata ruwayar ta biyar; wanda duk aka yi wa ku ka za a azabtar da shi. Wadannan ruwayoyin dukkansu kuskure ne daga masu ruwaito su da hukuncin hankali da shari’a.

Alfadhilun Nawawi ya na cewa: Inda aka wadannan ruwayoyin a babin mamaci ana yi masa azaba saboda kukan danginsa a kansa a sharhi muslim ya ce: Wannan ruwayoyin dukkansu daga ruwayoyin Umar dan khaddbi ne da dansa abdullahi. (ya ce): A’isha ta musanta musu wannan kuma ta jingina su zuwa ga mantuwa ko kuskure, ta kafa hujja da fadinsa madaukaki: Cewa; “Wata rai ba ta daukar zunubin wata ran” Surar An’am: 164.

Na ce: Haka nan Ibn Abbas da imaman ahlul - baiti (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) gaba daya sun yi inkarin wannan ruwayar gaba dauya, su ka kafa hujja a kan kuskuren mai ruwayar, kuma ai’ash ba ta gushe ba da ita da Umar ana jayayya kan wannan mas’alar har sai da ta yi kukan wafatin babanta, sai abin da ya faru tsakaninsa da ita ya faru kamar yadda dabari ya kawo a cikin tarihinsa yayin da ya kawo batun wafatin Abubakar a cikin abubuwan da su ka faru a shekara ta 13 bayan hujira, a juzu’I na hudu na tarihinsa, da sanadinsa zuwa ga Sa'id dan musayyab. Ya ce: Yayin da Abubakar ya rasu, sai A’isha ta tsayar da ku ka gareshi, sai Umar dan khaddabi ya zo har sai da ya tsaya a gaban kofarta, sai ya hana su yin ku ka ga Abubakar, sai su ka ki hanuwa, sai Umar ya ce da hisham dan Walid: Shiga ka fito mini da ‘yar dan Abukuhafa, sai A’isha ta ce da hisham yayin da ji wannan magana daga Umar: Ni na haramta maka shiga gidana. Sai Umar ya ce da hisham: Ni na ba ka izinin shiga, sai hisham ya shiga ya fitar da ummu farwata ‘yar’uwar Abubakar zuwa ga Umar, sai ya rufe da bulala ya yi mata dukan tsiya da bulala, sai mata masu ku ka su ka watse da su ka ji haka. Nan ya kare.

A nan ne za mu jawo hankulan mutane masu tunani zuwa ga sanin dalilin da ya sanya sayyida zahara (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ta yi nesa da gari yayin da ta yi ku ka ga babanta (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka), da fitar ta da ‘ya’yata cikin wasu mata zuwa ga bakiyya su na masu ku ka ga manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka), su na masu zama karkashin inuwar itacen arak da su ke can. Yayin da aka sare itacen don su tashi, sai Imam Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya yi mana wani dan daki karami a nan bakiyya da ake ce wa da shi “dakin bakin ciki” wanda ta ke zuwa can ta na kukanta a ciki. Wannan dakin ya kasance ana ziyartarsa tun zamanin da kamar yadda ake ziyarar sauran wurare masu tsarki har sai da a wadannan shekarun aka rusa shi a wadannan ‘yan shekarun da umarnin sarki abdul’aziz dan sa’ud bawahabiye yayin da ya mamaye hijaz, ya rusa wurare masu tsarki a bakiyya da aikin da ya yi bisa akidar mazhabarsa ta wahabiyanci, wannan kuwa ya faru a shekara ta 1344 hijira, mu mun samu albarkacin yin ziyarar wannan wurin a shekara ta 1339 yayin da Allah ya yi mana baiwar yin hajjin dakinsa mai alfarma da ziyarar annabinsa (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) a wannan shekarar, da kaburburan alayen gidansa masu tsarki da daraja a bakiyya aminci ya tabbata gare su.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next