Umar da Ra'ayin Shari'a 1



Maliku dan anas ya kawo a muwatta[19] cewa, daga inb shihab daga ass’aib dan yazid: Cewa ya ga Umar dan kahddabi yaan dukan almkandir[20] saboda yin salla bayan la’asar.

Abdurrazak ya ruwaito daga zaid dan khalid[21] cewa Umar ya na halifa ya gan shi ya na yin raka’a bayan sallar la’asar sai ya doke shi. Sai ya kawo wannan hadisin. A cikinsa sai Umar ya ce: Ya zaid! Ba don ni ina jin tsoron mutane su dauke su a matsayin tsani da za su yi ta yin salla har zuwa dare ba, da ban yi duka saboda yin su ba.

An ruwaito Tamimud Dari shi ma ya kawo shigen wannan, ya na kawowa a cikinsa cewa: Umar ya na cewa: Sai dai ni ina jin tsoron wasu mutane su zo bayanku su na yin salla tsakanin la’asar har zuwa faduwar rana har su wuce lokacin[22] da annabi ya hana yin salla a cikinsa. Nan ne ya kare da lafazinsa.

 

 

Daga ciki, canja makamu Ibrahim (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) daga wurinsa:

Makamu Ibrahim shi ne dutsen da mai yin Hajji ya ke yin salla wurinsa bayan ya kare aikin dawafi saboda yin aiki da fadin Allah madaukaki: “Ku riki makamu Ibrahim wurin salla” Bakara: 125. Ibrahim da Isma’il (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) a yayin da su ke gina dakin Allah, gininsa ya yi sama, sun kasance su na tsayuwa kansa domin mika duwatsu da tabo, kuma ya kasacne a hade da ka’aba, sai dai larabawa bayan Ibrahim da isma’il sai su ka canja masa wuri su ka ajiye shi inda ya ke a yau din nan, yayin da Allah ya aiko Muhammad (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) da shiriya ya bude masa Makka sai ya dawo da shi ya hada shi da dakin ka’aba kamar yadda ya ke a lokacin kakanninsa Ibrahim da isma’il (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) amam yayin da Umar ya zama halifa sai ya sake da wo da shi inda ya ke a yau (wato inda mushrikan jahiliyya su ka ajiye shi), alhalin lokacin manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) da Abubakar ya kasance a hade da ka’aba ne[23].

A cikin shekara ta goma sha bakwai da hijira sai Umar ya yalwata masallaci mai alfarma da ya hada da gidajen mutane da suek gefensa, sun kasance sun ki sayarwa, sai ya rusa gidajen a kansu[24], ya sanya kudinta a cikin baitul mal har sai da su ka karba.

 

 

Daga ciki akwai ku ka ga mamata

Bakin cikin mutum yayin mutuwar wadanda ya ke so, da kukan da ya ke yi musu ya na daga abubuwan da su ke na ban tausayi ga dan Adam, kuma suan daga cikin abubuwan da su ke nuna tausayi muddin mutum bai hada su da munann zantuttuka da ayyuka ba.

Kuma manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya fada a wani hadisi ingantacce da Ahmad dan Hambal ya karbo daga Ibn Abbas[25] cewa: Duk abin da ya kasance daga zuciya da ido daga Allah ne da kuma tausayi, kuma duk abin da ya kasance da hannu da harshe to daga shaidan ne.

Kuma ayyukan musulmi tabbatattu da sauran su sun ginu a kan haka ba tare da wani mai musu ba, kuma dokar asalin halacci ma ta na hukunta haka ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next