Umar da Ra'ayin Shari'a 1



 

 

Daga ciki, zartarwarsa mai tsira da aminci ga gaskiyar Hadib, da haninsa da kada su fadi wani abu game da shi sai alheri

Buhari ya buhari ya fitar daga littafinsa daga abi uwanata dan Husain, ya ce: Abu abdurrahman da hibban dan atiyya sun yi jayayya, sai abu abdrrahman ya ce da Hibban: Hakika ni na san abin da ya sanya sahibinka ya yi jur’a kan zubar da jini - ya na nufin Ali - sai ya ce da shi mene ne? sai ya ce: Wani abu da na ji yaan fada. Sai ya ce: Mene ne? ya ce: Manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya aika mu da ni da Zubair da abu marsad, dukkanmu mahaya dawakai ne, ya ce: Ku ta fi har sai kun zo wani Raudhatu[39] Hajj. (Abu salama ya ce: Haka nan Abu Uwanata ya ce Hajj), akwai wata mata a wurin a tare da ita akwai takarda daga Hadib dan Abi Balta’a zuwa ga mushrikai, ku zo mini da ita, sai su ka ta fi a kan dawakai har sai da su ka same ta inda manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya gaya musu ta na tafiya a kan wani rakuminta, Hadibu ya rubuta wa mutanen Makka cewa ga manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) nan zuwa gare ku, sai mu ka ce da ita: Ina takardar? Ta ce: Ba ni da wata takarda. Sai mu ka sunkuyar da rakuminta mu ka bincika babu komai a cikinsa, sai abokan tafiyata su ka ce: Ba mu ga wani rubutu tare daita ba. Sai ya ce: Sai na ce mun san annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) bai yi karya ba, sai ya rantse mini: Na rantse da wanda ya rantse da shi sai kin fito da littafin ko kuma mu fito da ke[40], sai ta karkato daga cikin ‘yar bukkarta (ta kan rakumi) wacce aka yi ta da kaba, sai ta fito da wani dan rubutu, sai su ka zo wa manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) da shi. Sai Umar ya ce: Ya ma’aikin Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) wannan ya ha’inci Allah da manzonsa da muminai, bari in sare wuyansa. Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce masa: Ya kai Hadib, me ya sanya ka yin wannan? Sai ya ce: Ya ma’aikin Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ba wai na kasance ba mumini ba da Allah da manzonsa, sai dai ni ian son ya zama ina da wani abu da zaikare mini iyalina da dukiyata gun mutanen, babu wani daga sahabbanka sai ya na da wasu dangi da Allah zai kare masa iyalanda da sukiyarsa gun mutanen. Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Ya yi gaskiya, kada ku fadi komai a kansa sai alheri, ya ce; sai Umar ya sake maimaitawa ya ce: Ya ma’aikin Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) wannan ya ha’inci Allah da manzonsa da muminai, bari in sare wuyansa…hadisi[41].

Na ce: Ya zama wajibi kan Umar kada ya maimaita hakan bayan manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ba su labari da gaskiyar mutumin da hana su fadin wani abu game da shi sai alheri.

 

 

Daga ciki, wasikarsa zuwa ga wakilansa game da wanda su ke aiko masa

Imam Malik da Bazzar sun kawo - a bayanin kalmar lakaha bisa wazanin baraka daga littafin “Hayatul Haiwan” na Dumair - cewa, daga manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) yayin da ya aika takardu zuwa ga wakilansa cewa: Idan ku ka aiko mini da wani mutum, to ku aiko mini da mai kyawun su na, mai kyawun fuska, sai Umar ya tashi yayin da ya san wannan ya na mai cewa: Ban sani ba, in fada ko in yi shiru? Sai annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce masa: Fadi ya kai Umar. Sai ya ce: Yaya za ka hana mu shu’umci, kai kuma ka yi shu’umci? Sai ya ce: Ban yi shu’umci ba, sai dai na zaba ne. Nan ya tuke.

 

 

Daga ciki, zumdensa ga annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) a game da zakka, kamar yadda Allah madaukaki ya kawo a surar tauba, sai ka duba da kula

Imam Ahmad ya fitar a masnadinsa daga hadisin Umar daga Salman dan Rabi’a, ya ce: Na ji Umar ya ce: Manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi rabo, sai na ce: Ya ma’aikin Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka), wasu sun fi wadannan cancantar wannan, ahlus sufa. Ya ce: Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Ku ku na tambayata da mummuna, kuma ku na sanya ni marowaci kuma ni ba marowaci ba ne.

 

 

Daga ciki, fadinsa ga Umar yayin da ya musulunta, ka boye musuluncinka

Sheihin masu irfani Muhyiddin dan Al'arabi[42] ya ruwatio cewa manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce da Umar dan Khaddabi yayin da ya musulunta cewa: Ka boye imaninka, sai Umar ya ki sai da ya bayyana.

Na ce: A wannan zamanin hikima shi ne a boye imani, kuma kira zauwa ga Allah da mnzonsa ba ta da wanta hanay sai ta hanyar boyewa, sai dai Umar da gwarzantarsa sai da ya ki sai dai ya bayyana ya saba wa umarnin shari'a.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next