Umar da Ra'ayin Shari'a 1



 

Daga ciki, akwai sayar da uwar 'ya'ya daga kuyangi

Ma’abota mazhabobi hudu sun ta fi a kan cewa wanda ya hana sayar da ummul walad (baiwar mutum da ta haihu da shi) shi ne Umar, kuma sayar da su ya halatta a lokacin manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) da halifancin Abubakar da wani bangare na halifancin Umar, kuma su na ganin wannan lamarin ya na daga cikin darajojinsa, kamar yadda su ke ganin sallar asham daga cikin darajojin falalolinsa.

Sai dai masu bincike game da hakikanin wannan lamarin sun samu daga sunna daga manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) da ya ke nuna haramcinsu a zahiri da ya zo daga manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka), sai su ka ce Umar ya riki wannan sunnar ce ya yi aiki da ita, kuma labarin abin da su ka kawo game da iliminsa kan wannan mas’alar ya ishe ka cikin abin da dansa abdullahi ya kawo cewa ya ji manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya na cewa: Ummul walad ba a sayar da ita, ba a bayar da ita, ba a gadon ta, ba a wakafinta, mai ita ya na jin dadi da ita tsawon rayuwarsa, idan ya mutu ta ‘yantu da mutuwarsa.

Ibn Abbas ma ya bayar da labari cewa ya ji ma’aikin Allah ya ce: Duk wata ummu walada da ta haihu gun sayyidinta ta zama ‘ya bayan ya mutu.

Wadannan hadisai ya zo da su da ainihin lafazinsu daga Ibn Umar da Ibn Abbas, shaihud da’ifa abu Ja'afar Muhammad bn Hasan Tusi a littafin ummul walad, a karshen mujalladi na biyu daga littafin Khilaf, a bisa zahiri wannan ra’ayin ba bisa wani ra’ayi ne da Umar ya gani ba, shi dai ya yi aiki ne da hadisin dansa abdullahi da hadisin Ibn Abbas kamar yadda ba ya buya.

Sai sai sheikh Tusi nassosin da su ka zo daga imaman ahlul bait (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) sun sanya shi dole ne ya yi tawilin wannan hadisin da fassara shi ta yadda zai yi daidai da mazhabinsa kamar yadda za ka karanta daga maganarsa kamar haka: Ya ce: Idan mutum ya haihu da baiwarsa ta na mulkinsa to ta na da hurumi saboda haihuwa da ta samu, bai halatta ba ya sayar da ita matukar ta na da ciki, idan ta haihu to mallakarta gun sa ba yta gushewa, bai halatta ya sanayr da ita ba matukar danta ya na nan sia dai a kudin bautarta, idan kuwa danta ya mutu to ya halatta a sayar da ita ta kowane hali ne, idan kuwa ubangijinta ya mutu to sai a sanya ta cikin rabon danta a ‘yanta masa ita. Idan kwa bai bar komai ba sai ita, to sai a ‘yanta rabon danta daga gare ta, a bar sauran ta ga masu gadonta.

Ya ce: Da wannan ne imam Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya yi aiki, da Ibn Zubair, da Ibn Abbas, da abu Sa'id alkhudri, da Ibn mas’ud, da Walid dan ukuba, da suwaid dan gafala, da Umar dan abdulaziz, da Ibn sirink, da abdulmalik dan ya’ala daga mazhabar zahiriyya. Ya ce: Dawud ya ce: Ya halatta a yi tasarrufi da ita kowane iri ne ba tare da ya yi bayani dalla - dalla ba. Ya ce: Abuhanifa da sahabbansa, haka ma shafi’I, da maliku, sun ce: Ba ya halatta a sayar da ita ko a yi tasarrufi da ita a bautarta ta kowane hali ne, kuma ta na ‘yantuwa idan ya yi wafati.

Ya ce: Dalilinmu a kan haka shi ne ittifakin ma’abota mazhabobi da ruwayoyi, kuma babu sabani a kan cewa bai halatta a kwanta da ita ba da mallaka, ya ce: Da kuwa mallakarta ta kawu da wannan bai halatta ba ke nan, kuma ya ce: Asalin lamarinta shi ne cewa ita baiwa ce, duk wani wanda ya yi da’awar gushewar wannan kuwa da tabbatar ‘yantuwarta bayan wafatinsa to sai ya kawo dalili. Ya ce: Abin da Ibn Abbas ya ruwaito daga annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Duk wanta baiwa da ta haihu gun ubangijinta to ita ‘yata bayan mutuwarsa. Wannan ana dora shi ne a kan idan ya mutu sai ta zama cikin rabon danta ne, to a nan ta ‘yantu gun sa. Ya ce: Haka ma abin da abdullahi dan Umar ya ruwaito cewa annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Ummul walada ba a sayar da ita, ba a bayar da ita, ba a gadonta, ba a bayar da wakafinta. Ya na jin dadi da ita matukar rayuwarsa, kuma idan ta mutu, to ta ‘yantu da mutuwarsa, wannan ya na nufin cewa bai halatta a sayar da ita ba matukar ta na da da rayayye, idan kuwa shugabanta ya mutu ta ‘yantu kamar yadda mu ka kawo a cikin ruwayar farko. Wannan shi ne maganar sheikh Tusi Allah ya ji kansa.

 

 

Daga Ciki, akwai Wajabcin Taimama Don Yin Salla da Sauran Su Tare da Rashin Ruwa

Ya ishe ka na daga nassosi a kan haka akwai fadinsa madaukaki mai daraja a surar ma’ida: “Ya ku wadanda ku ka yi imani idan ku ka tashi don yi salla to ku wanke fuskokinnku da hannayenku zuwa gwiwowin hannaye, kuma ku shafa kawukukanku da kafafuwanku zuwa tuduk kafa, kuma idan kun kasance a halin janaba to ku tsarkaka, kuma idan kun kasance marasa lafiya ko ku na kan tafiya ko wani daga cikinku ya yi bayan gida, ko kuma ku ka kusanci mata, kuma ba ku samu ruwa ba, to ku yi taimama wuri mai tsarki, sai ku shafi fusakunku da hannayenku daga gare shi” Surar Ma’ida: 6.

Da fadinsa madaukaki a surar nisa’i: “Ya ku wandanda ku ka yi imani kada ku kusanci salla ku na halin maye, har sai kun san me ku ke cewa, ko kuma ku na janaba sai dai idan ku na masu wucewa ta hanya har sai kun yi wanka, idan kuma kun kasance marasa lafiya ko ku na masu taiyfa ko waninku ya yi bayan gida, ko kuma ku ka kusanci mata, kuma ba ku samu ruwa ba, to sai ku yi taimama wuri mai tsarki, sai ku sahfi fuskokikinku da hannayenku, hakika Allah ya kasance mai yawan yafewa mai yawan gafara” Surar Nisa’i: 43.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next