Shi'anci Da Shi'a



Sai dai, wajibi ne kame harshe ga zagi ko cin mutuncin wanimusulmi wannan kuwa ba bambanci ko sahabi ne ko ba shi ba, haka nan kuma kare alkalami daga hakan, domin zagi ba ya daga cikin sunnar ma'aiki cikamakon annabawa Muhammad (S.A.W). Kuma tare da hakan zamu ga cewa mafi yawan sahabbai salihan bayin Allah ne, masu gyara da suka cancanci girmamawa da jajintawa.

Mu sani neman sanin halayensu domin sanin adili amintacce dawanda ba hakan yake ba, al'amari da ya faru domin sanin waye hadisansa za a karba waye kuma ba za a karba daga gareshi ba. Wannan kuwa ba domin komai ba sai domin kare sunnar Annabi daga cakuda tsakanin karya da gaskiya ko sanin kage da aka yi wa Manzo (S.A.W) wanda tun a zamaninsa wasu daga cikinsu suka fara yi masa karya da kage har ya tsawatar kan hakan. Tare da sanin cewa yi masa karyazai dadu ya yawaita bayan rayuwarsa.

Don haka ne ma malamai masu yawa kamar suyudi da ibn jauzida sauransu na malaman duka jama'u biyu suka yi ta'lifin littattafai domin gano hadisan da suke tabbas daga Annabi (S.A.W) suke da kuma wanda kage aka yi masa.

20-Shi'a sun yi imani da cewa akwai imami mahadi (A.S) wanda ake sauraronsa daga zuriyar Fadima (A.S) saboda ruwayoyi masu yawa daga Annabi (S.A.W). Kuma shi na tara ne daga jeren salsalar 'ya'yan imam Husaini (A.S).

Kuma tunda na takwas shi ne imam Hasan Askari (A.S) wanda yarasu a shekarar hijira 260, kuma ba shi da wani da sai dansa mai suna Muhammad wanda ake yi wa kinaya da Abul kasim (A.S) kuma da yawa daga amintattun mutane sun gan shi, suka kuma bayar da labari game da haihuwarsa da siffofinsa da jagorancinsa da kuma wasiyya da shi ta bangaren babansa, kuma ya buya daga ganin idanuwa kusan shekaru biyar daga haihuwarsa yayin da makiya suka so kashe shi. Don haka ne Allah ya boye shi saboda ya zama ajiya domin kafa hukumar adalici ta musulunci mai game dukkan duniya a karshe zamani, domin tsarkake kasadaga zalunci da fasadi, bayan ta cika da su.

Ba mamaki ga tsawon rayuwarsa, domin Kur'ani mai girma yaambaci Isa Masihu (A.S) cewa rayayye ne har yanzu duk da kuwa ya wuce shekaru 2004, kuma Nuhu (A.S) ya rayu a cikin mutanensa shekaru dubu daya ba hamsinyana kiran su zuwa ga Allah, ga kuma Khidr (A.S) yana raye har yanzu.

Allah mai iko ne a kan komai, kuma nufin mai zartuwa ba maiiya hana shi ko tsayar da shi, shin ubangiji mai daukaka bai fadi ba game da Annabi Yunus (A.S) yana mai cewa: "Ba domin ya kasance cikin masu tasbihi ba * Da ya zauna a cikinsa har ranar tashin kiyama"[10].

Kuma da yawa daga malaman ahlussunna sun yi furuci dasamuwar imam mahadi (A.S) a raye, suka ambaci sunan iyayensa (A.S) kamar:

a- Abdul Mumin Shablanji, Bashafi'e a littafinsa na Nurulabsar.

b- Ibn Hajar Alhaisami Almakki, Bashafi'e a litafinsa naSawa'ikul muhrika, yayin da ya ambace shi da Abul kasim, kuma babansa ya rasu yana da shekaru biyar, sai dai Allah ya ba shi hikima, kuma ana kiransa da Al'ka'imAl'muntazar.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next