Shi'anci Da Shi'a



Ba sa karbar hadisan isra'ilanci (na attaura dainjila) da majusanci da suka dauka Allah yana da jiki, kuma suke kamanta shi dabayinsa.

Ko kuma suke danganta zalunci zuwa ga Allah madaukaki.Ko kuma suke danganta aikata mummuna zuwa ga annabawa tsarkaka ma'asumai.

6-Sun yi imani cewa Allah adali mai hikima, yahalicci halittarsa da adalci da hikima, bai yi halittar wani abu don wasa ba, sandararre ne, ko tsiro, dabba ne ko mutum, sama yake ko kasa, domin wasa ya koru ga Allah wanda yake mai dukkan kamala korarre daga dukkan tawaya da aibi.

7-Sun yi imani cewa Allah ya aiko manzanni daadalcinsa da hikimarsa zuwa ga mutane gaba daya, tun daga farkon rayuwarsu a duniya, annabawa da manzanni da suka siffantu da isma da ilimi mai yalwa, da Allah ya yi musu baiwarsa ta hanyar wahayi, don shiryar da dan Adam da kuma taimaka masa domin kaiwa zuwa ga kamalar da aka zana musu. Da kuma shiryar da su zuwa ga biyayya da zata kai su zuwa ga aljanna, take kuma samar musu da dacewa zuwa ga rahamar Allah da yardarsa. Mafi shaharar wadannan sun hada da annabawa da manzanni kamar: Adam, da Nuhu, da Ibrahim, da Isa, da Musa, da sauran wadannda aka ambaci sunansu da halayensu a cikin Kur'ani da Sunna madaukakiya.

8-Sun yi imani da cewa wanda ya bi Allah yagudanar da umarninsa, ya tafiyar da dokokinsa a fagagen rayuwa to ya tsira ya rabauta, ya kuma cancanci yabo da lada, koda kuwa bawa ne baki. Kuma dukkan wanda ya saba wa Allah (S.W.T) ya yi kunnen uwar shegu da umarninsa to ya tabe ya halaka ya kuma cancanci zargi da azaba koda kuwa bakuraishe ne sharifi kamaryadda ya zo a hadisin Annabi madaukaki.

Kuma sun yi imani da cewa inda za a yi sakamakoda lada ko azaba a ranar lahira ne wanda a cikinta akwai hisabi, da ma'auni, da aljanna, da wuta, wannan kuwa bayan wucewar kabari da barzahu. Amma tanasuhi wanda masu musun ranar kiyama suka tafi a kansa, to Shi'a suna musunsa domin yalizimta kayarta Kur'ani mai girma da Sunna madaukakiya.

9-Sun yi imani da cewa karshen annabawa damanznnai kuma cikamakonsu mafificinsu, shi ne Muhammad manzon Allah (S.A.W) dan Abdullah, dan Abdul Mudallibi (A.S) wannan da Allah ya kare shi daga sabo da kurakurai. Ya kuma kare shi daga manyan sabo da kananansu, kafin annabta da bayanta, a al'amuran isar da sako ko a waninsu. Ya kuma saukar masa da Kur'ani mai girma domin ya kasance littafin tsarin dokoki ga rayuwar dan Adam har abada, sai Manzo (S.A.W) ya isar da sako, ya bayar da amana da gaskiya daikhlasi, ya kuma sadaukar da komai.

Shi'a suna da gomomin littattafai da sukawallafa game da tarihin rayuwar Annabi (S.A.W) da halayensa da mu'ujizozinsa. Koma wa littafin Irshad na Sheikh Mufid, da kuma A'alamul wara, da a'alamul huda na Dabrasi, da kuma biharul anwar na Majlisi, da kuma littafin arrasululMusdapha na sayyid Muhsin khatami.

10- Shi'a sun yi imani da cewa Kur'ani mai girmada Allah ya saukar ga annabinsa Muhammad (S.A.W) ta hanyar jibrilu (A.S) kuma wasu daga sahabbai masu girma suka rubuta shi, wanda imam Ali (A.S) yana gabansu a lokacin Annabi (S.A.W) kuma a karkashin kulawar Annabi da lurarsa garesu, da shiryarwarsa da kuma hardace shi a zuciya (da ka), da kuma kiyaye rubuta haruffansa da kalmominsa da ayoyinsa da surorinsa da kare su da kiyaye su, wanda suka nakalto shi kakanni da iyaye har zuwa yau, wanda shi ne musulmi suke karantawa gaba dayansu a cikin dare da rana, ba tare da wani dadi ba ko ragi, ko canji ko jirkita. Kuma Shi'a sun yi rubuce-rubuce masu yawa game da wannan al'amari, sai ka koma wa littattafansu matsawaita da magajerta. (Koma wa littafin al'Kur'ani na Zanjani, da tamhidul Kur'ani na Hadi ma'arifa dawasunsu).

11- Shi'a sun yi imani cewa Muhammad (S.A.W)Manzon Allah ne kuma bawansa ne, wanda yayin da ajalinsa ya kusanto ya sanya Ali (A.S) halifansa a bayansa, kuma jagoran musulmi gaba daya bayansa domin ya jagorance su a siyasance, kuma ya shiryar da su a tunani, ya waraware matsalolinsu, ya ci gaba da tarbiyantar da su, da tsarkake su, wannan kuwa duk da umarnin Allah ne (S.W.T) a wani wuri da ake kira Ghadir Khum, a karshen shekarun rayuwarsa kuma a hajjinsa na karshe, a cikin jama'ar musulmi masu yawa wadanda suka yi hajji tare da shi, wadanda a wasu ruwayoyi ya zo cewa adadinsuya kai kusan mutum dubu dari.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next