Shi'anci Da Shi'a



Na daya: Shi ne domin kare rayukansu dajininsu domin kada a zubar da shi a banza.

Na biyu: Domin kare hadin kan musulmi dakuma rashin bayar da kafar rarraba.

38- Shi'a suna ganin abin da ya kawo wamusulmi ci baya a yau shi ne, rashin wayewar ilmi da kimiyya, kuma maganin hakan shi ne a wayar da kowane musulmi maza da mata, da kuma daukaka matsayinsu na ilimi da wayewa, da samar da cibiyoyin ilimi kamar jami'o'i da wuraren koyarwa da kuma amfana daga abin da ilimin zamani ya samar a wajen kawar da matsalar tattalin arziki da maraya, da sana'a, da sanya dogaro da kai a cikin al'ummar musulmi domin kai su zuwa ga ci gaba a fagen aiki da ilimi domin su samu isuwa da tsayuwa da kafafunsu, kuma su kawar da halin nan na bin sawunwasu kasashen.

Don haka ne ma Shi'a duk inda suke sukankafa cibiyoyin ilmantarwa da koyarwa, suna kuma kafa wuraren koyarwa domin samar da fitattun mutane kwararru a fagen ilimomi daban-daban, kamar yadda sukan shiga fagagen ilimomi kamar jami'o'i a kowane gari, kuma sun fitar damalamai da kwararru a fagage mabambanta.

39- Shi'a suna da alaka da mabiyansu tahanyar abin da ake kira da takalidi (koyi) a cikin hukunce-hukuncen shari'a, kuma suna koma wa zuwa ga malamansu a mas'alolinsu na fikihu, kuma suna aiki da fatawowin malamansu a dukkan fagen rayuwarsu, domin su malamai a wajansu, wakilai ne na imamai masu tsarki, kuma saboda malamansu ba sa dogara da hukumomi da dauloli a rayuwarsu, don haka ne Shi'a suke dogara da aminta da su da amintuwa mai girma.

Makarantun Shi'a na ilimin addini atattalin arzikinsu suna dogara kan humusi da zakka ne wanda mutane suke bayarwa ga malamai bisa son ransu da biyayya, a matsayin hakkin shari'a da ya hau kansukamar yadda salla da azumi da zakka suka hau kansu.

Kuma akwai dalilai masu karfi na wajabcinbayar da humusi wanda wasu ruwayoyinsu sun zo a cikin sihah da sunan.

40- Shi'a suna ganin hakki ne na musulmisu samu hukuma ta musulunci mai aiki da littafin Allah da sunnar manzonsa, wacce zata kiyaye hakkokin musulmi, kuma ta tsayar da alakoki na adalci da aminci tsakaninta da sauran dauloli, ta kuma kiyaye iyakokinta, ta kuma lamunce 'yancin musulmi a wayewar al'adu, da tattalin arziki, da siyasa, domin musulmi su kasance masu izza kamar yadda Allah yake so garesu yayin da yake cewa: "Izza da buwaya na Allah da manzonsa da muminai ne"[24].

Kuma ya ce: "Kada ku yi rauni, kadaku yi bakin ciki, ku ne masu daukaka matukar kun kasance muminai"[25].

Shi'a suna ganin musulunci addini necikakke gamamme da yake kunshe da tsari mai zurfi na dokoki, kuma ya hau kan malaman al'ummar musulmi masu girma su hadu su yi bincike tsakaninsu domin fito da fuskar hakikanin wannan tsari, domin su fitar da al'umma daga dimuwa dadawwamar matsaloli wadanda ba sa karewa, Allah ne mataimaki.

"In kun taimaki Allah, zai taimakeku, ya tabbatar da duga-duganku".

Wadannan su ne mafi bayyanar hanyoyintafarki na Shi'a a fagen akida da shari'a. Wannan jama'a ta Shi'a suna rayuwa a kowane waje tare da sauran 'yan'uwansu musulmi a dukkan duniya, kuma suna masu kwadayi matuka wajen kare musulmi da izzarsu, kuma a shirye suke su sadaukar daduk wani abu da suke da shi a kan wannan tafarkin.

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijintalikai

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17