Shi'anci Da Shi'a



A yau da muke ganin al'umma tana cikin mafimunin harin makiya a kan samuwarta da akidarta, kuma hadin kanta yana cikin mafi munin harin makiya, ta hanyar samar da matsala a rayuwarta ta addini da mazhaba da ijtihadi, kuma ga wannan harin yana kusan kai wa ga gaci. Shin ba yana kan ita al'ummar ba ta yi kokarin ganin hada sawunta da karfafa alakarta.

 Duk da kuwa nau'in rarraba ta mazhabobi da takeda ita, amma ta yi tarayya a littafi da Sunna a matsayin madogara, kuma ta yi tarayya a tauhidi, da annabta, da imani da lahira, da salla, da azumi, da hajji, da zakka, da jihadi, da halal, da haram, da kuma son ahlin gidan Annabi(S.A.W) da kuma kin makiyansu, duk da wasu sun fi wasu.

Sassabawar tana kasance ne kamar sassababawar'ya'yan yatsu na hannu daya da dukkaninsu suna tukewa ne zuwa ga gaba daya duk da kuwa tsakaninsu sun sassaba a tsayi da fadi da shakalin kira, wannan al'umma kamar gabubuwa ne na jiki da suka sassaba amma dukkaninsu sun yi tarayya wajen tafiyar da jiki domin hada samuwar dan Adam ta wata fuska tare da kuwa sabaninshakalolinta.

Kuma kamanta wannan al'umma da hannu daya kokuma jiki daya nuni ne zuwa ga wannan hakika din.

Tun da can malamai ma'abota mazhabobi mabambantasun kasance suna rayuwa da jun a tare ba tare da wani jayayya ba ko taho mu gama, saudayawa sukan yi taimakekeniya tsakaninsu, har ma wani ya yi sharhin littafin wani na fikihu ne ko na akida, kuma daliban wasu suka yi karatu wajen wasu, kuma wasu su karfafi ra'ayin wasu, wasu kuma su ba wa wasu izinin ruwaya ga wasu, wasu kuma suna bayar da izinin ruwaitowa daga littafin mazhabinsa dajama'arsa ga wasu.

Kuma suka yi salla bayan juna, suka yi kykkyawarsheda ga juna, suka yarda da juna, kuma suna rayuwa tare waje daya, har ma ta bayyana cewa kamar babu wani sabani tsakaninsu, duk da kuwa wani lokaci a kan samu raddi na ladabi tsakaninsu, raddi na ilimi da dalili.

Da yawa aka samu dalilai na tarihi mai yawa gameda wannan al'amari da taimakekeniya mai zurfi tsakaninsu, kuma malaman musulunci sun cika wayewarsa da kayan tarihi na rubuce-rubuce, kamar yadda da wannan aiki nasu suka bayar da kyakkyawan misali mai girma game da 'yancin mazhabanci, hada da cewa sun iya janyo hankalin duniya zuwa ga himmantuwa dasu, kuma suka kiyaye girmansu.

Mu sani ba wani abu ne mai wahala ba malamanwannan al'umma su hadu cikin sauki da nutsuwa su tattauna da ikhlasi da gaskiyar niyya game da abin da aka sassaba a cikinsa da kuma sanin dalilankowace al'umma da kuma hujjar da take da ita.

Kamar yadda yana da kyau kuma abu ne na hanklaikowace al'umma da jama'a ta bijiro da akidunta, da matsayin ta na tunani da fikihu a cikin 'yanci a fili, domin rashin ingancin abin da ake jifanta na tuhumomi da shubuhohi ya bayyana a fili, kuma kowa ya san bambance-bambancen da yake tsakaninsa da waninsa, kuma su san cewa abin da ya hada kan musulmi ya fi abinda yake rarraba su yawa.

Wannan dan littafi mataki ne zuwa ga kai wa gawannan gaci, kuma domin gaskiya ta bayyana ta fito a fili kowa ya san ta kamaryadda take, Allah ya sa mu dace.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next