Shi'anci Da Shi'a



 Kuma ayoyi masu yawa sun sauka game da wannanal'mari mai girma.

Kamar yadda Annabi ya nemi mutane su yi mubaya'aga imam Ali (A.S) su sanya hannuwansu a kan hannunsa, sai suka yi masa bai'a kuma na gaba-gabansu su ne manyan sahabbai mutanen Makka da madina da shahararrunsu. (Duba littafin Ghadir na allama Amini, da ya cicciro dagalittattafai daban-daban na tafsiri da tarihi)

12- Shi'a suna imani da cewa imami (jagora)bayan Manzo (S.A.W) tunda shi ma dukkan abin da ya wajaba ga Annabi (S.A.W) shi ma ya wajaba a kansa (A.S) kamar al'amarin jagorancin al'umma da shiryar da ita, da tarbiyynantarwa da bayanin hukunce-hukunce, da warware matsalolin tunani masu wahalar warwara, da kuma maganin mas'alolin zamantakewa masu muhimmanci. Don haka dole ne ya kasance mutum ne da mutane suke samun nutsuwa da shi, domin ya jagoranci al'umma zuwa ga tudun tsira, kuma yana tarayya da Annabi a siffofinsa kamar isma, da ilimi, domin yana tarayya da shi a dukkan abin da ya shafi cancanta da daukar nauyi, in ban da annabta ka karbar wahayi, domin annabci an cika shi da cikamakon annabawa Muhammad (S.A.W), wanda yake cikonannabawa da manzanni (A.S).

Kuma addininsa shi ne cikamakon dukkan addininAllah (S.W.T), shari'arsa ita ce karshen shari'o'i, littafinsa karshen littattafai, kuma babu wani Annabi bayansa, kuma babu wani addini bayan nasa, babu wata shari'a bayan shari'arsa. (Shi'a suna da wallafe-wallafe a wannanfage masu yawan gaske).

13- Shi'a sun yi imani da cewa bukatuwar al'ummazuwa ga mai jagoranci mai shiryarwa kuma shugaba ma'asumi ta sanya kada al'amarin ya tsayu da kafa imam Ali (A.S) halifansa kawai, dole ne al'amarin ya ci gaba har zuwa mudda mai tsawo har a samu kafuwar musulunci kafuwa mai karfi kuma a kiyaye asasin shari'a, kuma da kare dokokinta daga abubuwan hadari da suke kawo mata hari, kuma suke barazana gareta kamar yadda ta yi barazana ga dukkan wata akida da imani da Allah da dukkan tsarin ubangiji madaukaki. Kuma domin wadannan jagorori na Allah su tsayu da matsayin bayar da kyawawan misalai a lokuta mabambanta game da ayyukansu a halaye mabambanta da suka dace dadukkan halayen da al'ummar musulmi zata shige su a nan gaba.

14- Shi'a suna imani da cewa Muhammad danAbdullah (S.A.W) don wannan dalili ne da kuma hikima madaukakiya ya kafa imamai goma sha daya bayan imam Ali (A.S) a matsayin jagorori a bayansa. Wadanda su ne  imamai goma sha biyu har da imam Ali (A.S) da aka yi nuni da su da kabilarsu ta kuraish a sahihul Buhari da Muslim da lafuzza mabambanta: Yayin da suka ruwaito daga manzon Allah (S.A.W) cewa: Wannan addini ba zai gushe ba yana mai tsayuwa da kafafunsa yana mai daukaka da buwaya har sai an samu shugabanni/halifofi goma sha biyu daga cikinku dukkaninsu daga kuraishawa (Ko bani hashim, kamar yanda ya zo a wasu ruwayoyin wasu littattafai, domin kuwa sunayensu sun zo a wasu littattafan a babin falaloli da darajoji da wakoki daAdabobi).

Hadisan cikin Buhari da musulim duk da su ba su kunshisunayensu ba, amma sun yi daidai da adadin imaman Shi'a goma sha biyu, wato Ali (A.S) da sha daya daga zuriyarsa kamar yadda Shi'a suka yi imani da hakan. Kuma ba yadda za a iya fassara wannan hadisi sai da abin da ya yi daidai da zancen da Shi'a suka tafi a kai. (Koma wa littafin khulafa'unnabi, na ha'iri bahrani).

15- Shi'a ja'afariyya sun yi imani da cewaimamai kuma halifofin manzon Allah da Allah ya yi umarni da binsu guda goma shabiyu ne, wadanda su ne:

Imam Ali (A.S) surukinmanzon Allah wanda yake auren 'yarsa, kuma dan amminsa (A.S), Shekara 23 K.Hzuwa 40 H

Abu Muhammad Hasan ZakiyyiShekara 2 H … 50 H



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next