Shi'anci Da Shi'a



Haka nan suna shafa kafafunsu dakawukansu ba sa wanke wa saboda wannan dalilin da muka ambata, kuma dan Abbas yana cewa: Alwala wankewa biyu ne, da shafawa biyu, wato abin wanke wa biyu da abin shafawa biyu ne, (koma wa sunan da masanid, da tafsirin fakhrur razi, guntafsirinsa ayar alwala).

26-Shi'a suna tafiya a kan cewa aurenmutu'a halal ne, saboda nassin Kur'ani mai girma da ya ce: "Abin da kuka ji na dadi daga garesu da shi, to ku ba su ladansu"[13]. Kuma saboda musulmi sun yi a lokacin manzon Allah (S.A.W) har zuwa rabin lokacin halifancin umar. Kuma shi aure ne na shari'a, da ya yi tarayya da aure na da'imi a:

a- mace ta kasance ba ta wani aure, kumata yi siga shi kuma mijin ya karba.

b- kuma wajibi ne a ba wa mace ladanta,kamar yadda Kur'ani yak ira shi da wannan sunan, abin da ake cewa da shi sadakia aure da'imi.

c- kuma dole ne mace ta yi idda bayanrabuwarsu da mijin.

d- kuma dole ne bayan wajebcin idda, daya zama na mijin ne idan an samu haihuwa, kuma dole mijin ya zama shi kadai ne,ba sama da hakan ba.

e- ana gado tsakanin uwayen da kumatsakanin yaron da iyayen nasa akasi da akasi.

Wannan aure ya bambanta da aure da'imi awajen cewa shi yana da mudda da aka ayyana karewarsa, da kuma rashin wajebcin ciyar da mace, da rashin wajebcin raba kwana tare, da rashin gado tsakanin ma'autan biyu, da rashin bukatar saki idan mudda ta kare. Domin karewar mudda shi kadai ya isa ya zama yankewa da rabuwa, ko kuma idan mijin ya yafe mataragowar muddar.

Hikimar shar'anta wanna aure ita ce:domin biyan bukatun namiji da mace na sha'awa ga wanda ba zai iya daukar nauyin jigilar yin aure na da'imi ba, ko kuma wanda/wacce ya/ta rasa matarsa/mijinta, saboda wafati, ko wani dalilin, tare da nufin rayuwa cikin mutunci da daukakaba rayuwar zina ba.

Mutu'a wani abu ne da yake na farko wajenwarware matsalar zamantakewa mai hadari da takan iya kai al'umma zuwa ga fasadi mai muni na zina, ko madigo, da fitar da mani ta hanyar haram.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next