Shi'anci Da Shi'a



Haka nan domin annabi da imami daga ahlingidansa shahidai ne kuma shahidai rayayyu ne, kamar yadda Allah ya fada awurare masu yawa a littafinsa mai girma.

32- Shi'a suna mauludin annabi (S.A.W) daimamai daga ahlin gidansa (A.S) gaba daya, suna kuma yin bukukuwa da kuma zaman makokin wafatinsu da rasuwarsu, suna masu ambaton falalarsu da darajojinsu da matsayansu wadanda suka zo a littattafai kamar yadda Kur'ani ya kawo labarandarajojin annabawa da matsayinsu kuma ya shelanta hakan.

Sai dai Shi'a suna nesantar abubuwanharamun a wadannan bukukuwa kamar cakuda maza da mata, da cin haram ko shansa, da shisshigi a yabo, da sauran abubuwan da suka haramta wadanda suka sabawa shari'ar musulunci, da kuma ketare haddi, ko sabawa wata aya ko wata ruwaya kowata doka ta littafi da Sunna.

33- Shi'a suna amfani da liattattafai dasuke dauke da hadisan manzo da ahlin gidansa masu tsarki (A.S) kamar littafin Kafi, na Kulain, da Manla Yahaduruhul Fakih na Saduk, da Istibsar da Tahzib na Dusi.

Wannan littattafai duk da suna dauke dahadisai masu inganci amma masu wallafa su ko Shi'a ba su sanya musu suna sahihai ba, don haka ne malaman shi ba su yi imani da ingancin duk abin da yake cikinsu ba, suna karba ne daga abin da ingancinsa ya tabbata gunsu, suna barin abin da ba sa ganinsa ingantacce ko kyakkyawa, ko kuma abin da zai yiwu a yi rikoda shi a bisa dokar ilimin rijal da dokokin ilimin hadisai.

34- haka nan suna amfana daga wasulittattafan ruwayoyi masu yawa a fagen akida da fikihu, da addu'a, da kyawawan halaye, kamar littafin Nahajul balaga na sayyid Radi wanda ya hada hudubobinimam Ali (A.S) da wasikunsa da hikimominsa.

Da kuma kamar littafin alhukuk da sahifasajjadiyya ta imam sajjad (A.S), da alawiyya ta imam Ali (A.S), da littafin uyun akhbarir Ridha (A.S), da tauhid, da khisal, da ilalus shara'i'i, dama'anil akhbar.

Saudayawa Shi'a sukan dogara da hadisanmanzon Allah (S.A.W) da suka zo a cikin littattafan 'yan'uwansu Ahlus Sunna wal jama'a, a fagage mabambanta ba tare da wani bangaranci ba, kuma littattafansu na da, da na yanzu sheda ne a kan hakan. Ta yadda suka rawaito hadisai masu yawa da suka zo daga matan annabi (S.A.W) da kuma manyan masu ruwaya kamar Abu huraira, da Anas da wasunsu. Da sharadin rashin cin karonsu da Kur'ani da kumahadisi ingantacce, da kuma hankali, da haduwar malamai.

36- Shi'a suna ganin bala'in da ya fadawa musulmi tun da, da kuma yanzu ba komai ba ne sai sakamakon abu biyu:

Na daya: Kaucewa da kuma mantawa da AhlulBaiti (A.S) a matsayinsu na jagorori masu dacewa, da kaucewa daga koyarwarsu,musamman tafsirinsu ga Kur'ani mai girma.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next