Shi'anci Da Shi'a



A garin Mash'had kuwa da yake Iran akwaikabarin imam Ali arridha (A.S). A garin Kum da Shiraz kuwa akwai na 'ya'yansu. Haka nan na Damashk da take Siriya akwai na sayyida Zainab Kubra (A.S).

A birnin Alkahira akwai na sayyida Nafisadaya daga manyan zuriyar Ahlul Bait (A.S).

Wannan kuwa duka domin girmama wa ne gamanzo (S.A.W) da ahlinsa, domin mutum ana kiyaye shi ta hanya kyautatawa zuriyarsa ne, kuma girmama su girmamawa ne gareshi. Kuma Kur'ani mai girma ya yabi Ali imarna, da Ali yasin, da Ali Ibrahim, da Ali ya'akub, ya kuma yaba su sosai, alhalin wasunsu ba ma annabawa ba ne. Yana cewa: "Zuriya ce sashenta daga sashe"[14].

Kuma Kur'ani mai girma bai hana wa wadandasuka riki kabari masallaci ba, yayin da suka ce: "Lallai sai mun riki (yin) wani masallaci a gunsu"[15]. Wato sai mun yi wani haramin ziyara a kaburburan as'habul Kahafi domin mu bauta Allah a wajen, kuma wannan aikin nasu ba a siffanta shi da shirka ba, domin musulmi mumini yana ruku'u da sujada ga Allah ne shi kadai, kuma yana zuwa kabari ne na wadannan waliyan bayi na Allah domin tsarkin wurin sakamakon albarkacinsu. Kamar yadda ya faru ga annabi Ibrahim (A.S), da fadinsa madaukaki: "Ku riki matsayar Ibrahim wajan yin salla"[16].

Wanda ya yi salla bayan makamu Ibrahim baya bauta wa makam ba ne, haka nan wanda ya yi ibada tsakanin safa da marwa shi ma ba bawan duwatsu ba ne guda biyu, amma Allah ya zabi wajen ne mai albarka da matsayi mai tsarki domin wajen yana dangantuwa zuwa ga Allah ne, domin kwanaki da wurare suna da tsarki da matsayi kamar ranar arfa, da kasar mina, da kasar arfa, saboda an danganta su zuwa ga Allah madaukaki.

30- saboda haka ne kamar sauran musulmi,Shi'a suke himmantuwa da sha'anin manzon Allah (S.A.W) da ahlin gidansa masu tsarki ta hanyar ziyarar kaburburansu, domin girmama wa garesu, da kuma sabunta musu alkawarin biyayya, da kokari a kan tafarkinsu wanda saboda shi ne suka yi shahada, domin ziyarar wadannan kaburbura nasu, yana tunatar da falalarsu da jihadinsu, da tsayar da sallarsu, da zakkarsu, da kuma juriyar da suka yi wajen shanye duk wata azaba da cutuwa a kan wannan tafarki, hada da cewa a cikin wannna akwai taya manzon rahama bakin ciki game da abin da ya samu ahlinsa(A.S) da aka zalunta.

Shin bai fada ba game da shahadar Hamza(A.S) "Sai dai Hamza ba shi da mai yi masa kuka"?!

Shin bai kasance ya yi kuka ba a mutuwarIbrahim (A.S) dansa abin sonsa?!

Shin bai kasance yana zuwa Bakiyya bayana ziyartar kaburbura?!

Shin bai kasance yana cewa: "Ku ziyarcikaburbura ba, domin itan tana tuna muku lahira ba?![17].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next