Shi'anci Da Shi'a



Kuma wadannan su ne Ahlul Baiti da Manzo Muhammad (S.A.W) ya kafa su da umarnin Allah a matsayin jagororin al'ummar musulmi saboda ismarsu da tsarkinsu daga sabo da zunubi, da kuma iliminsu mai fadi wanda suka gaje shi daga kakansu, kuma Allah ya yi umarni da sonsu da biyayya garesu yayin da yake cewa, "Ka ce: Ba na tambayarku wani lada a kansa sai dai soyayya ga makusanta"[8]. Kuma ya ce: "Ya ku wadanda kuka yi imani ku ji tsoron Allah ku kasance tare da masu gaskiya"[9]. (Ka koma wa littattafan hadisai da tafsirai da falaloli da darajajin manyan mutane kamar Ahlul Baiti (A.S) da sahabbai daga littattafan Sunna da Shi'a).

16-Shi'a sun yi imani da cewa wadannan imamai tsarkakatarihi bai taba kawo musu wani zamewa ba ta dugadugai, ko wani sabo ko saudaya a zance ko a aiki, kuma sun yi hidima mai girma ga al'ummar musulmi da iliminsu, suka cika ta da sani mai zurfi, da sahihiyar mahanga ta akida, da shari'a da kyawana halaye, da ladubba, da tafsiri, da tarihi. Kamar yadda suka tarbiyyantar da jama'a mai yawa mata da maza gwaraza zababbu na musamman wadanda kowa ya yi furuci da falalarsu da iliminsu, da kyawawan dabi'unsu.

Kuma Shi'a suna ganin cewa duk da an nesantar da su wadannan imamai daga fagen siyasa da jagoranci sai dai su sun bayar da gudummuwarsu da sauke nauyinsu na bayar da ilimi da fikira da nazari ingantacce, yayin da suka kare akidar musulunci da shari'arsa daga hadari.

Da al'ummar musulmi ta ba su dama sun tafiyar da al'amuransu na siyasa da Allah (S.W.T) da Manzo (S.A.W) suka ba su, da al'umma ta samu sa'adarta da daukakarta, da girmanta cikakke, da ta wanzu mai hadin kai mai karfi daya da ba ta da rarraba, babu sabani, babu jayayya, ba fada, ba kashe-kashe, babu daukar kaskanci. (Duba littafin nan na imam sadik (A.S) da mazhabobi huduna Haidar mai mujalladi uku).

17-Shi'a sun yi imani da cewa saboda wadannan dalilai nahankali da ruwya masu yawa da aka ambata a littattafan akida, ya zama waji bi a yi biyayya ga Ahlul Baiti (A.S) da kuma lizimtar tafarkinsu domin ita ce hanyar da manzon Allah (S.A.W) ya zana wa al'umma, kuma ya yi wasiyya da bin ta da lizimtar ta a cikin hadisin sakalain, yayin da yake cewa: "Ni na bar muku nauyaya biyu: littafin Allah da ahliln gidana, matukar kun yi riko da su, ba zaku taba bata ba har abada", Kamar yadda Muslim a littafin da kuma gomomin masu ruwaya sun rawaito wannan hadisi. "(Ka koma wa littafin Risalatuns sakalain na Bash'nawi, wacce jami'ar azhar ta gaskata da ita shekarakusan talatin da suka gabata).

Kuma sanya halifa da yin wasiyya al'amari ne da ya shahara acikin rayuwar annabawa (A.S) da suka rigaya, (Ka duba isbatul wasiyya na mas'udi, da littattafan hadisai, da tarihi, da tafsiri na jama'a biyu).

18-Shi'a sun yi imani da cewa abin da ya hau kan al'umma shi ne ta zauna ta duba wadannan al'amura da idon basira ta hanyar tattaunawa da juna, tare da nisantar duk wani zagi da cin mutunci da tuhuma da kage a kan juna. Kuma abin da ya hau kan malamai da masu tunanin al'umma na kowace jama'a da mazhaba da kungiya ta musulmi shi ne; su taru da kulla tarurruka su yi bincikenwannan al'amari da tsarkin zuciya da ikhlasi, da 'yan'uwantaka bisa dalili da sanin menene 'yan'uwansu Shi'a suke cewa, kuma menene dalilinsu a littafinKur'ani da sunnar Annabi (S.A.W), da kuma hankli da tarihi da siyasa dazamantakewa da suka gabata tun lokacin Annabi (S.A.W).

19-Shi'a sun yi imani da cewa sahabbai da dukkan wadandasuke tare da Annabi sun bayar da tasu gudummuwa mai girma mazansu da matansu, kuma sun yi hidima ga musulunci, sun sadaukar da komai wajen ganin yada shi, kuma musulmi dole ne su girmama su, su nema musu yardar Allah da gafararsa.

Sai dai dukkansu ba daidai suke ba, akwai wadanda ayyukansu na gari ne wasu kuma ba na gari ba wadanda ba su fi karfin kawo su gaban nakadi da musanta su ba, wannan kuwa domin su mutane ne kamar saura da suke iya yin daidai ko kuma su saba, kuma tarihi ya ambaci cewa wasunsu sun kaucewa hanyar manzon Allah (S.A.W) hatta a zamaninsa, kai Kur'ani mai girma ya furta hakan ma a wasu daga surorinsa kamar surar munafikun da ahzab da hujurat, da tahrim dafath, da Muhammad, da tauba.

Sukan wasu munanan ayyuka na wasunsu ba yana nufin kafirtasu ba, domin ma'aunin imani da kafirci sananne ne bayyananne, domin ma'aunin hakan shi ne kore tauhidi da sakon manzon rahama (S.A.W) ko yarda da su, ko kuma kore wani al'amari na larurar addini kamar wajebcin salla, da azumi dahajji, da zakka, da haramcin giya da caca, da sauransu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next